Sashe 1
Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
NANA KHADIJA (littafi na daya)
NA
BINTA UMAR ABBALE
(Maman Abdul Wahabu)
NA FARA DA SUNAN ALLAH SARKI BUWAYI ,WANDA YA QAGI SAMA DA KASA SARKIN DA BABU KAMARSHI,
ALLAH KAYI DADIN TSIRA GA ANNABI MUHAMMADU(SLW) WANDA KABAWA YA YADDA KA ,ALLAH KA KARA TSIRA DA AMINCI A GARESHI DA AHALINSA DA SAHABBANSA TSARKAKA
ALLAH YADDA KABANI IKON RUBUTA LITTAFIN NAN ,LAFIYA INA ROKANKA KASA IN GAMA LAFIYA, ALLAH KA YAFEMIN KUSAKURAI NA NA CIKI.
AMEEN.
WANNAN LITTAFIN QAGAGGE NE DA GA NI MARUBUCIYAR BANYI DOMIN WANI KO WATA BA WANDA YAGA YAYI DAI DAI DA RAYUWARSHI A RASHIN SANI NE
GARGADI
BAN YADDA WANI KO WATA YAYI AMFANI DA WANI BANGARE NA CIKIN LITTAFIN NAN
BA BATARE DA SANINA BA ,DUK WANDA YA TABAMIN WANI SHASHE A CIKI ,ZAMU TSAYA A GABAN HUKUMA
*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*
Wata yarinyace "yar kimanin shrkaru biyar zaune akan dakalin gidansu tare da wasu yara da baza su wuce shekarunta ba sai faman bal bala musu masifa take tace "wallahi ke indo bazan yadda ba sai nasa keyi ke kuma sa'a da kike cewa nafadi bayan kina ganin indo CE ta bige min hannu na dazaki CE na bata yi wallahi Baku isaba" indo CE ta miqe ke tace " wallahi baki isaba dama kinsaba yima na runto kullum in munayi to yau kam sai kin bayar eheeee! dan batsoranki muke jiba" "e ai sai in baki tunda na kine " cewar Dije itama ta tashi harda cire dan kwalli tana ta faman zagin indon sa'a CE ta riqe hannun dije ganin tana kokarin kaiwa indo duka tace " Aa ke dije banda zagi da duka" da,ike ita duk tafisu sanyin hali indo ko jin Dije na zaginta ba tayi wata wata ba ta fuxgo kafar ta ta yarda ita a kasa ai kwan Dije assitin ta tashi tayi kan indo kan kace kwabo fada ya rin ca6e tsakanin Dije da indo sai faman ko kawa suke Dije sai faman zagin indo take itako indo sai faman dukan "yan kayanta take itama dama Dije bata da wani karfi sai aikin tsokanar fada gashi bata da wani jiki indo ta fita jikin girma Sa'a ko sai kokarin rabasu take yi suna hadawa da,ita,,
,,wata irin tsawa sukaji an ce "kai wannan wane irin iskanci ne kukeyi anan da dabbanci "? cikin sauri Dije ta saki indo sai haki take ta juyo jikinta sai tsuma ya keyi ganin yaya Ali ne a tsaye a gabansu ,,sai faman zare ido take harara ya banka mata yace "wato ke dan ubanki bazaki daina wannan iskancin ba ko kitara yara ki ta kokawa a waje dan rashin kamun kai" ya mutsa baki tafara tana kunkuni dashi "to ina ruwanka za kazo ka wani ta kura mana ni banasan a shiga min sabga" duka ya kai mata abakin cikin zafin nama yace "dan ubanki wakikewa haka nisa anki ne " cikin sauri ta dafe bakin hawaye ya na zuba tace "Allah ya isa mugu" cikin kunkunin tayi maganar mari ya kaimata gami da cewa "wato bakin ki bazai mutu ba ko wallahi sai na gyaramiki zama shashashar yarinya kawai stupid " yafada tare da jan hannuta tana turjewa yadaki kafarta ta fadi kasa ya hau janta kamar wani kayan wanki
Su indo kuwa tun lokacin da yaya Ali ya mari Dije suka gudo sabuda sun San halinsa harsu zai hada ya Zane babu abinda ya dameshi,,janta yake yana dukanta da kafarsa itako bakin ta baibar yimai rashin kunya ba Nene, CE azaune a tsakargida tana ta faman gyaran wake ta ji ihun Dije tashi tai dausari ta tana gyara daurin zaninta tana fadin "wallahi na tsani mugunta irin ta "yayan unguwar nan me kuma marainiyar Allah tai musu suke dukanta" kafin tarufe bakinta ta hango Dije a kasa Ali ya na janta kamar yana Jan tsumma Salati ta tabka tace "kai Ali wannan wane irin abune mai tayi maka dan mugunta "? tafada tare da karasawa tana kokarin kwatar Dije daga hannunsa "wai bada kai nake ba kasake ta mana wallahi ka kiyayeni akan wannan marainiyar Allah sa,arkace ita dazaka dunga dukanta iyi"? ,sakinta yayi yana jan tsaki tare da hararar Nene "yace wallahi Nene ke kike daurewa yarinyar nan ginda take yin abinda tagada ma" "to ina ruwanka da,ita iyi?" cewar Nene n cikin 6acin rai ya kalleta tare da daure fuskarsa yace "samunta nayi fa a waje ta tara yara suna ta faman dan be sai kace wasu dabbobi dan nai mata magana tahau zagina wallahi kija mata kune ta kiyayeni kan in bar garinnan sai na canja zamata kammanni da duka"
Harara Nene ta galla masa tace "ka ki yaye ni Ali nifa ba na San ne man magana taya daga zuwan ka zaka ta kurawa yarinya tana wasa da kawayenta gaskiya in dai zaka zo ka ta kura mana ne gwara ka juya ka koma bana son zuwan naka haba ina dalili"! Tafada tana gyara daurin zaninta,
Fuskarshi babu Walwala yake kallonsu yana Mamakin Abinda Nene tace tabbas Nene in dai a kan yarinyar nan ne babu da Wanda baza ta 6ata ba ,cikin yanayin maganarshi yace "ae ba gurin ki nazo ba gurin "yan Uwa da Abokan Arziqi nazo wancan Mara kunyar yarinyar bata isa ta Sani na bar garin nan ba batare da na shirya ba"
Harara D'ija ta galla masa tare da murgude baki tana bayan Nene A la6e
Yana kallonta yana Mamakin Rashin kunyar yarinyar,
Nene tace "to babu ruwanka da'ita har ka bar garin to kaji!!
Bai ce komai ba ya Nufi bakin rijiya domin daukar bota da nufin daura Alwala ganin har an soma kiraye kirayen sallahr magari ba
Ya na sane ya zira kafarshi daya wacce ke sanye da takalmi sawu ciki ya mutsikewa D'ija "yan ya tsu yayi saurin dauke kafarsa ya sakai ya fice daga gidan hannushi riqe da bota
Wata kara D'ija ta kurma tana kallon kafarta guda domin Sam bata lura dashi ya take mata ba
Da sauri Nene ta jiyo tace ke lafiyarki kuwa ?Cikin ihu D'ija tace "Nene kunama ce ta har beni yanzu"
Da sauri Nene n ta kafama kafar D'ijan tana duba wa gami da jan yeta da gurin tana sallalami , ta hau duba kafar
Tace" kefa kin fiye sangarta haka harbin kuna ma yake ko dai wani kwaron ne ? Tashi ki bani guri in kara duba gurin"
Da sauri D'ija ta matsa gefe tana jan kafa sai kace wacce tayi targaade
Hakadai Nene takaraci dubanta a gun bata ga komai ba juyowa tai gurin dijan race" Ai sai ki tashi daga gurin ko kije kiyi alwala lokacin sallah yayi na gaya miki kidai nai wa manya rashin kunya kinki ji idan yaje yaji miki ciwo babu ruwa na Ato,,cikin zumbura baki dije ta tashi da ga gun ta nufin inda butocin Al,wala suke ta dau daya dan duk abunta bata wasa da sallah da lokaci yayi take barin abinda take taje tai sallah
Shi kam Ali yana gama alwala wani yaro yabawa butar ya mayar gidan ya huce masallaci bai dawo ba saida ya jira lokacin isha ya gabatar da ita yai adu,oinsa sannan ya dawo gidan
Nene ya tarar ta idar da sallah isha dije kuma tana can gefe itama ta idar da sallahr tana ta faman cin wake da shinkafa wanda tasa nene tayi mata itakam tana bala'in san wake da shinkafa da manja da yaji tai ta zabga yaji tana ci tana dadar baki, ko kallon inda take bai yi bah ya samu gefen Nene ya zauna yana karewa tsakar gidan kallo dan shi kam mutum ne mai tsamtsami abu kadan sai yasayi tashin zuciya yana da bala,in stafta komai nashi a tsare dan baya shiri da kazami gashi da wani irin hali. muskiline sosai sai ya gadama yake magana ko acikin abokansa ma haka dan har suna suka samasa ammafa duk wannan halinnasa bai raina mutum ko mai kankantarshi da iyayansa ya na bala,in sansu da kannansa to suma kannansa suna ji dashi sosai sabida ya nai musu abinda suke so Ammafa suna jin tsoransa musaman idan sukasan sunyi wani laifin dan baya musu wasa musamman akan harkar karatunsu,, wannnan kenan
Nene ce tajiyo bayan tagama lazimi race" to sarki kafi sarki mulki kazo kazaune min iye zakafara iyayin naka ko,,tafada tana gallamasa harara
Murmushi yasaki ya kalleta yace " ke ba ayin abin arziki da ke daga zuwa na ko ruwan kirki baki bani nasha ba kina ta wani naiman fada dani ,,dariya Nene tayi to ai kaine daga zuwanka ka farayimin halin naka,,
Ta shi tai tai hanyar madafi wata katuwar kula ta fito dashi ta a jiye a gabansa hade da da faranti tace "gashinan ay mutumin kane nai maka sabida nasan ka ce yau zaka zo tafada tana kokarin zuba masa tuwon shin kafa ne da miyar taushe wanda taji nama da manshanu sai kamshi ne ke tashi agun tun lokacin da tabude kular ,tazuba mai ta ajiye a gabansa to gadanga bissimilah tafada tana murmushi dan in taso tsokanarsa da wannan sunan take kiransa ,
Gyara zama yai ya ce "saura ruwa ai cika ladanki uwargidana" gyara fuska tai tace "wannan kuma sai ka tashi ka dauko da kanka wai kai komai sai ammaka" tafada tana harararsa,, hade fuska yai yace " sai kiyi ai nikuma bazanci ba indai baruwan kika kawumin ba ya fada yana kallonta da murmushi a fuskarsa dan yasan halinta indai baici abinci ba tashin hankalinta take,
Duk wannan abin da suke dije nagefe tana jinsu dan indai da sabo tasaba indai yazo sai sun ta tabkawa da Nene
Nene ce ta kalleta tace" dije na tashi ki dauko masa ruwa a kinji tunda nari ga na zauna bazan tashi,,