← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 35

Sashe 10

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ali ko tafiyarshi yayi ya kyalesu a gurin ganin abinda sukeyi shifa ya tsani shirme, kai tsaye part din shi ya nufa ,Wanka kawai yakeson yayi sabida yadda yake jin nauyi a jikinshi ,kwata-kwata baya son zafi ko kadan

Nene ko hararar Na'ima take tace"ai sai ki sake ni ko sai ki yadda ni"

Na'ima na dariya tace"wace ni yadda uwar masu gida,gaskiya naji dadin zuwanki Nene nayi kewarki sosai,sabida kinzo kenan ,baza ki kuma ba"

"To ai sai ki rike min kafafu ki hanani tafiya,Nene tafada tana galla mata harara

Dariya Na'ima tasa ,ta kalli D'ija tace "ke wai ba zaki gaishe ni ba"?

D'ija ta kalle ta tana zumbura baki tace"tabdijam ke zan gai sai tab!

Na'ima tace"ni ba yayarki bace to"

Zumbura baki D'ija tayi batare da ta gaida Na'iman ba suka wuce ciki gidan ita da Fa'iza sai karadin surutu sukeyi.

Girgiza kai Na'ima tayi tana murmushi sabida tasan halin D'ija da tsiwa

Gaba dayansu suka shiga babban falon hajiya Zainab tana khicin ita da mai.aikinsu Asabe yau da kanta ta shiga kichin din domin girkin na mussaman ne sabida zuwan Nene bayan hakama tasan Ali bacin abincin masu aiki yake ba duk da cewa Asabe akwai tsabta shikam inda ba ita ce tayi abinci ba to bayaci. Sabida yasan tes din girkin kowa shiyasa babu yadda zatayi take shiga khicin din tai mai dashi da maigidan,, sukuma asabe tayi musu nasu ,,gashi asaben ta,iya girki sosai bata da kazanta ko kadan amman duk da haka Ali bai yadda ba shikam haka Allah ya hallice shi da tsamtsami

Cikin sauri Ummi domin haka suke cema ta ,tafito da ga khicin tana goge hannuta

Cikin fara,a tace "sannu da zuwa Nene kunsha hanya" tafada tana zama a kujarar da,take kallon Nene

"Ai kam dai munsameku lafiya"? "Lafiya lau wallahi ya mutan gida da sauran "yan uwa?

"Nene tace kowa lafiya lau duk suna gaisheku",

"To masha,Allah muna amsawa"

Asabe ce tashigo hannunta rike da wani babban tire ,itama cikin fara,a tace "sannu da zuwa hajiya ,,

"Yawwa sannu Asabe mun sameku lafiya

Cikin sauri Asabe tace "lafiya lau hajiya tana kokarin budewa mata lemo

Cikin fara,a Ummi ta kalli dija wacce suke ta faman surutu ita da fa,iza tun zamansu a gun "tace Dijan Nene babu magana ko?

Cike da kunya Dja ta sunkuyar da kanta tace "ummi inayini"? domin itama da haka take kiranta

Dariya ummi tayi tace "bazan amsaba sai. Da na roka sannan"kara sukuyar da kanta tayi tana murmushi tace "to kiyi hakuri",ummi tace" nakiyi "

"Tace Nene kina jina da mutuniyar taki ko wai sai da na roki gaisuwa sannan"

Dariya Nene tayi tace "ai in suka hadu da wannan berar basa ji basa gani"

Ummi tace "ai kam dai"
"Tace Nene kisauko kasa ma kici abinci zai fi dadi ko" tafada tana kokarin gyara gun

Nene tace "me kuka girka ne"? domin dai nikam bazan iya wannan ciye,ciyen naku ba,,

Murmushi ummi tayi sabida tasan hali tace "ai
Nene wainar shinkafa ce sai tuwon semo sai ki zabi wanda zaki ci,,

"To koda naji,samin towan kadan"

"Asabe ummin ta kwalawa kira cikin sauri sai ga asabe ummi tace fito da ledar ki shimfida

To asabe tace ta juya cikin sauri ta dauko ledar tashin fida a gun da suke zaman cin abinci India ba,akan daining zasu ciba

Na'ima ce tace "kakus,zanci tare dake dan inkara karfin ido"

"Banza, Nene tayi mata yayin da take kokarin tashi da ka kan kujerar ba ta ce mata komai ba

Ummi ce ta hada wa Nene abincin daidai yadda tace ,,

Sai farfesu da ta zuba mata shima ta ajiye mata a gefe.

Kallon miyar Nene tayi gani wani uban nama da ta zubamata
Ga,farfesu a gefe yana jiran ta sai kace wata kura

Kallon ummin tayi tace "ina zan kai wannan uban abincin baya ga ha kama wanann naman miyar yayi yawa kwashe shi ki barmin uku ya isa "

Cikin sauri Na'ima ta duro daga kan kujera tace "ummi zubamata wata miyar daban bara nazo naci da wannan ni"

Harara Nene ta gallamata tace "to kura sarkin kwadayi ke dai kici nama har yanzu kinanan da wannan halin naki"

Na'ima tace "to Nene in bake ba wazai ki nama"

Ita dai ummi bata ce komai ba illah can zawa Nene wata miyar da tai

Kallon N'aimar tayi tace "gatanan ki ka ra wata akai sai ku hadu da kannannaki ai kuci tare"

Su dija kam hankalinsu baya gurin hirarsu suke irinta yarinta suna ta faman kyalkyala dariya,,

Ummi ce takalli inda suke zaune tace "ke fa,iza haka ake ai sai ki kyale kawartaki ta ci Abinci ta huta kafinan sai kicika ta da labarin naki" laa Ummi yanzu zatazo ai kinsan mun Dade bamu haduba shiyasa" tafada tana dariya dija kam itama dariyar tai fa,iza tace "taso muje muci Abinci kinji ta rike hannun dija

Gefen Nene suka zauna Ummi ta ce "Na'ima,ki dibar mu ku yadda zai isheku,,

Tare suka hadu sukaci su uku suna ci suna wasa da dariya Nene,ma takan sa musu baki cikin hirartasu

Ali ne ya shigo cikin sallama

Cikin sauri Na'ima tajuya " ya Ali sannu da zuwa andawo lafiya?

Bakin ta sai rawa ya ke itama fa,iza jiki na kyarma take gaishe shi

Kallonsu yai yana nazarin su sai kace wasu marasa gaskiya

Hararar Na'ima yai yace "wannan rawar jikn da kike nameye?

"Babu komai ta fada hade da sunkuyar dakanta yace " ina Ummi ne?

Cikin sauri fa,iza tace " ta hau sama yanzu ina jin sallah za tayi"

Bai ce komai ba ya Ciro wayarsa daga aljihu n jins din daya ke jikinsa sakamokon jin kira da yaji ya shigo wayar

Nene kam tace "mutum sai kace wani mala,ika daka zuwan ka Guri yara sun yi wani tsuru!,tsuru" tafada yayinda take mikewa daga inda take bayan tagama cin abincin

So take taje tai sallah itama ganin lokacin sallar yana neman wucewa,

Faruk ne ya kira shi
Cikin jin haushi yace "wai dallah malam mene wai daga da wiwa kaki barin mutane su huta sai faman kiran waya kake,iyi?

Daga daya bangaran
Shima faruk din cikin fusata yace" an dame ka din kai dan rainin hankali ne wallahi ya zai,ai in dinga kiran wayar ka kaki dagawa sabida tsabar baka da mutumci "

"An ki daga wayar me zakamin to zaka da me ni da kiran waya" yafada yana dan murmushi sabida yasan ya gama kunna faruk din

Cikin hayaniya faruk din yace "ubanka zanma dan isa kawai"

"Dallah malam kasan wannan takardun suna wajanka kasamu muna ta faman ne masu ehe?

Dan dariya Ali yasaki kasa kasa yace " wane takkadu kuma?

"Bayan ka zo ka kar6a saga hannuna" yana sane so yake ya kular da faruk din ta kaddun suna hannunsa

Tsaki faruk din ya ja yace "ni zaka mayar wani shashasha ko

Ai ganin zuwa kafito dasu dan raini wayo kawai "

Kashe wayar yai ya mai da ita aljihunsa

Ummi ce ta sakko.bayan ta idar d sallahr

Tace "kaida waye ne kuke magana naji kamar magana sama sama. Ya mutsa fuska yayi yace ,,faruk ne

"Au ko danaji. Yana ina tafada tana kallon falon,,

"Bai zo ba waya mukai mybe kin ganshi yanzu ai akwai wasu takkadu da muka cike zai zo ya karba su"

"Ummi mun same ku lafiya ?

"Kalau muke" yace " wai ina jameel ne ?

Ummi tace " bai Dade da fita ba kasanshi kayan bol yasa yafice ai yau sai an ganshi kuma"

Shiru yai bai CE komai ba domin dai bayadda zaiyi da jameel kasan cewar sa tun yana yaro kwallo tashiga ransa yana masifar son kwallon kafa shiyasa ko wace irin bol za,a buga kallonta baya wuce shi ga musu acikin abokai sunayan "yan kwallo kuwa Babu wanda bai sani ba

"Ummi.Mai kika girka min ne ?

Yafa da yana marai raicewa harararsa tayi tace Babu abinda na dafa "

Dariya yai yace "nasan wasa ne Ummi na CE fa,,

Nasan tayi min girkinta mai dadi da gamsarwa"

Shiru Ummi tayi bata ce komai ba

"Kinji Ummi na wallahi wata irin yunwa nake ji please "yafada da yanayin shagwaba

Su dija dake gefe kam kallon ikon Allah take ganin irin tabarar da Ali yakewa ummi sai kace wani yaro,,

Ta6e baki tayi aranta tace dube shi abin ma ko kyau bai mai ba

Ummi tace " ni kam Ali wanann larurar taka ta isheni wanann wane irin abu ne to in kayi aure yazakai iyi? dole dai kaci abincin matar taka domin dai kasan mu nan mun sallama ka ato"!

Mikewa tayi ta nufi kchin

Dija ce takewa fa,iza magana kasa kasa tace "wai dama haka wannan ya Alin yake sai yaita wani abu wai shi maitsafta yai tacewa mutane kaza mai "

Da sauri fa,iza ta kalli inda yake zaune. ta kalli dija tace "ke wallahi Babu ruwa in yajiki tam"

Shikam bai San me sukeyi ba domin eir pic ne a kunnashi yana jin kira,a tare d shek malam sulaiman ya na masifar son kira'arsa, idanoshi a lumshe,,

Ita ma dija kallo gun tai tana ya mutsa fuska bata cekomai ba ,,

Tace "wai ina Nene ne?

Fa,iza tace" " ta tafi sallah tashi muje muyi muma "

Ummi CE tashigo da Abinci cikin wani plete
Ta ajiye a gabashi "gashinan ai "

Tafada tana zama cikin kujera,,

Bude idanowanshi yai yace " iluv ummi na godiya nake"

Kallon Cikin plete din abincin yai wata lafiyar yiyar waina ce ta shinkafa taji miya sai kamshi take gefe lemo wanda yake bala,in so da ummin take masa shi kadai zo6o ne ake mai wani irin hadi wanda ummin ce ta,iya shi

Sauko wa kasa ya yi ya tankwashe kafafunshin yai bissimillah ya fara ci

Sallamar faruk yai tare da shigowa sabida ya saba babu wani shamaki da gidan sabida yazama dan gida abotarsu da Ali tun da kuruciya karatu ma tare sukayi komai na su irin daya sai banbancin hali da kowa ya ke dashi ,,

Shi faruk yana da sakin fuska da fara,a sabanin Ali da yake miskili na ,ajin karshe

Shigowa yai yace "ummi wanan mutumin ya dawo zai farasaki wahala ko?

Yafada yayin da yake zama shima a gefen Ali,,
Chapter 10 · 0% Book details