← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 35

Sashe 25

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zun bura baki dija tayi tace "yaushe nake gaba dake kece Ai nace kiyi hakuri ki barni kin ki sai da kika sa wannan mugun ya daken kina kallonshi baki hana shi ba"

Dariya Nene tayi tace" ai naji ' dadi daya zane miki ' jiki 'ai rashin kunyar ki tayi yawa babu babba babu yaro duk baki kyale ba''

Shan kunu Dija tayi tace "Ai shima nai masaAllah ya'isa ban yafeba tunda ni ba jaka bace da zai ai ta duka na dan yaga ni marainiya ce kuma itamaSiyaman Ai ya dake ta dazu da Asubah sauran Ya Na'ima itama sai nasa dake ta tunda ita ce taje ta kirashi A lokacin"

Cikin mamaki' Nene take kallon Dija " tace kina nufin kece kikasa Aliyu ya daki Siyaman'?"

"Eh man kin tashi tayi tai sallar Asubah kowa ya tashi ni ko naje na watsa mata ruwa shine ta tashi ta hau zagina ta hau kaina ta dinga duka ''

"Ni kuwa nai ta kurma' ihu har sai da yaji',ya shigo dakin shine ya Na'ima take gaya masa shine ya zane ta ita ma " Dija' ta karasa maganar tana ta kyalkyala dariya har da kwanciya

Sakin baki Nene tayi tana mamakin Dija hannuta Akan ha6arta tace yanzu Abinda ki kayi kenan ko D'ija"

Tana cigaba da yin Dariya tace "Allah ne ka wai ya sa kamin Ai bani na kirashi' ba da kuma Alhakina''

"Umm "!to Allah ya shirya ki Dija" Nene ta fada tana kara mamakin Abun

"Nene Amma kin hakura da tafiya ko? " "Aa gobe ko jibi' zantafi' ke ai tunda kin nuna kuna son zama anan din Ai shikkenan gaki ga'Aliyu' nan in kika cigaba da wannan halayen naki duka zaki dinga ci A gurinshi babu Abinda ya dameshi to" kaji"

Ta6e baki Dija' tayi tace "yo' ni ina ruwana da shi Ai ba kula shi nake ba ,ni din ce kawai ya tsana yake duka na ai baya dukan su fa'iza' da ya Na'ima"

"Ke ma bai tsane ki ba halayenki ka kwai ya tsana kuma ki sake ki cigaba da yi mishi fitsara da rashin kunya da kai na zan sa shi ya zane ki "

Shiru Dija tayi bata ce komai ba 'Amma fuskarta babu walwala

Nene taciga ba da cewa "kuma saura A saki a makarantar kije ' ki yi ta shirme da shiri,rita wallahi ki tsaya kiyi karatu da kyau' domin baki da gatan da yafishi
In kuma kika qi dama 'Alin zan dinga sawa ina daga' can ya dinga zane' miki jikinki to' kaji"

Nene ta fada tana sauke numfashi'

Zumbura baki' Dija tayi tace "duk kun bi kun tsaneni Yanzu harda ke Nene 'l kin dai na sona yanzu kinfi son ya'Ali yanzu"

Harararta Nene tayi tace "Ai se kiyi Ai tun ba yau ba nake miki fadan yawan fitsar da rashin kunya da kike tunda yanzu na samu mai ladabtar min dake Ai haka na ke so"

Sai da Nene tagama tsorar da Dija A kan cewar in dai bata dai na haleyenta ban tanabdaga can zata dinga yiwa Ali waya ya dinga dukanta duk Abinda tayi

Sannan ta mike tayi tafiyarta falo ta bar Dija cikin wasuwasi da faduwar gaba tana jin ko kawai tabi Nene su kuma can domin tana bala'in tsoron dukan da yaya, Aliyu yake mata gami da murmurde mata hannaye da yake' wanda duk sanda yayi mata wannan A zabar hannuta yana dadewa bai daina radadi da zo gi ba

Wata zuciyar tace Ai ba kula shi kike ba kuma in ya da ke ki ba sai kiyi masa Allah ya isa b

Haka tagama saqe - saqen ta ta tashi tabi bayan Nene falon domin tun dazu take jiyo hayaniyar su Na'ima da siyama kamar masu fada

Suna zaune kan dannig kowa yana kokarin hada Abinda zai ci yayin da' fa'iza ke tsaye cikin unipom tayi shirin zuwa 'skull

Kallonta Abba yake har ta karaso gurin yace ''zo nan'' Dija zuwa tayi ta dur kusa tana gaishe shi ,cikin sakin fuska yake Amsawa yana kara jin son yarinya A cikin zuciyarsa shi duk wani ' rashin kunyar ta' da ' Ake fada bai da meshi ba tunda ya tabbatar da kuruciya ce in ta girma zata dai na

"Ummi ina kwana" Dija tafada "lafya lau Dija kin tashi lafiya?"

"Lafiya kalau ummi '' "A she ba bacci kike ba' Ai nazata bacci ki ka koma ganin tun dazu ' Nene ta fito daga dakin"

"Bacci ne yaki zuwa shiyasa na fito ummi " 'Dijan tafada gyara kujera tayi ta zauna itama tace '' ya Na'ima ina kwana''

Cikin mamaki Na'ima take kallon Dija' yau ita Dija ke gaisarwa ta6 lallai za'ai ruwa da kankara

Ita ma 'Na'ima cikin sakin fuska ta Amsa tace "yau ni kike gai sarwa kuma lallai nasamu babban matsayi' yau A gidanan"

Zumbura baki Dija tayi bata ce,komai ba ta dau cup tana kokarin hada tea

Dariya Abbah yake yana kallon Na'ima yace " da bata gaisheki ne? Bana son sharri fa"

Tana Dariya tace "ta6 Abbah Dija ce ta ke gaisheni Ai ko zuwa mukayi gidan Nene bata min magana har mu baro garin sai taga dama take kulan tafi kula jameel sai kawarta kaga ko dole inyi mamaki Abbah"

Da murmushi A fuskarsa ya dago kai yana kallon fa'iza wacce ke tsaye kusa da Dija suna magana kasa,kasa yace "fa'iza na me kika tsaya jira maza ga Haruna can yana jiranki kar ki makara " kallonsa fa'iza n tayi tace "to Abbah " kamar zatayi' kuka tace yaushe za akai Dija skull din iyi?"

"Mondey insha Allahu jameel zai je yagama komai ki kwantar da hankalinki Auta na kinjiko" dariya fa'iza ta saki tace "to Abbanmu" sannan ta kama hanya ta tafi'

"Allah ya Bada sa'a "
ummin tafada Nene kam ranta A bace yake ganin,irin Abinda Dija tayi yanzu ta gaida kowa Gurin ba ta gaida siyama ba wannan, Ai raini ne sabida haka cikin bacin rai ta kalli Dijan tace "ita kuma siyama, me tayi miki da baza ki gaida ta ba duk da dukan da kika sa,A kayi mata da sanyi safiyar Allah ko kuma kuna kallonta baza kuce komai haka zan tafi in barta sai Abinda taga dama zata yi kuna kallonta kun zuba mata ido Ai ko A gurina ban yimata irin wannan tarbiyar ba" tafada tana kallon Abbah da Ummin

"Kwarai D'ija baki kyautaba yanzu nake so na yi mata fada wallahi sai kika yi magana " ummi tafada

Ta6e baki Nene tayi tace "da nai magana ba Ai Amana ce A gurinku kuma A mana daya ce''

"Kwarai kuwa kiyi hakuri Nene Allah ya bamu ikon rike Amanar da kika bamu"

Abbah kam murmushi' yake yace "Nene kenan to Ai itama Na'ima ba gaida ta take ba sa'a taci yau ko baki ji Abinda Na'ima tafada ba Akwai kuruciya A tattare da Dija yanzu ki kwantar da hankalunki in sha'Allah zakiyi mamakin Dija kwanannan'' " to Ameen dai " Abunda Nene tace kenan tacigaba da shan kunun gyadarta

"Da yau nake so in tafi Ai " tafada tana kallon Abbah wanda ya mike shima daga gurin da nufi tafiya ofis dama A shirye yake

"A,a kibari zuwa gobe in sha Allah sai na kai ki da kaina " Abba yafada yana kallonta

"To babu komai Ai yau da gobe duk na Allah ne Allah ya kaimu lafiya"

"Ameen ya Allah" yafada ya ce "to sai na dawo ko"

"To Allah yabada sa'a "Nene tafada ummi kam bayanshi tabi kamar ko da yaushe suma su Na'ima Allah ya kikyaye su kai masa gaba dayansu har da Siyama wacce tun zamanta A gurin kanta yake' A sunkuye gaba daya ta mu zanta tana mamakin waye ya gayawa su Nene yaya Aliyu ya dake ta duk kunya ta isheta tasan Dija ce zata gaya musu kuma ta san sai tafadi dalilin da yasa ya dake ta

To haka dai Siyama ta karaci jin kunyarta ta dena ita ko Dija babu Abinda ya dameta ko kallon siyama bata kuma yi ba' taci ga da sabgarta babu Abinda' ya sha mata kai ummi kam ta ci Al washin zatayiwa Aliyu magana kar ya kuma dukan siyama duk lalacewar mutum fada Ake masa ba duka, ba gashi' ita zai Aura in ya saba da dukanta haka, zaije yai ta labtar yarinyar mutane...............................

To washe gari ranar Nene takama hanya bayan sun sha kuka ita da Dija Na'ima sai dariya take yimusu tace, "Nene babu fa dole ki kama hannunta kitafi da ita tunda kukan rabuwa take dake kema haka ina dalili kun sanyamu agaba sai koke koke kuke yi"

Hararata Nene tayi tace "ina ruwanki in nace zan tafi da ita zaki hana ne' iye? Zare ido Na'ima tayi tace " ni Asuwa " "to rufemin baki " Nene tafada shiru Na'ima tayi tana dariya kasa kasa ita ko Siyama Nene take rarrashi ko Kallon Dija batayi ba itama Dijan ko kallonta batayi Ahaka Abba da ummi suka sauko suka same su

Cikin mamaki ummi take kallo'Nene tace "lafiya naga sai koke koke Akeyi"?

"Wai Dija'take ta yawa kuka ,,shine nace kawai' in taga da matsala ta kama hannuta tai tafiyarta da ita" Na'ima tafada tana dariya

Harararta ummi tayi tace "ke kam Anyi babbar kwabo wallahi ni matsa kibani guri " ummi tafada

Kama Dija tayi ta rungume tana rarrashinta tace "kiyi hakuri duk sanda Akayi hutu sai A dinga kaiki kinayi Acan gurin Nene kinji ko"

Shi kam Abba babu Abinda yace musu ya kalli Nene yace "to Nene sai tafiya ko? "In sha,Allah'' Nene tafada tana tashi daga inda take zaune gabadayansu suka rufa mata baya har gun motar shima jameel fitowa yayi domin hayaniyar da yaji idonsa A kan Nene wacce ' ke kokarin shiga mota yace "ina zuwa Nene "? cikin Dariya Na'ima tace " tafiya zatayi wai" "
kamar ya tafiya zatayi ina ce ta dawo nan da zama ko sanja shawara Abban yayi "? "A,a tace ga Dija nan Anan tabarta' ita kuma tace bazata zauna ba" cikin mamaki jameel yake kallon Nene yace " wai don Allah da gaske tafiya zakiyi''?
Chapter 25 · 0% Book details