← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 35

Sashe 30

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani kallo ta watsawa faruk din jin sunan da ya Am bace ta dashi wai uwargida ita fa tsani a danganta ta da wannan sunan wallahi dama bawani shiri' suke da faruk din ba, tunda matarsa basa shiri gashi Aliyu bashi da wani Amini sama da shi kuma ta lura yana daukar shawarshi wallahi ya sake yasa Aliyu yayi mata kishiya sai ta lalata masa rayuwa ta bar mai Abin kwatance A duniya yabar ma wani rawar kai

Yana kallon irin kallon da take watsa masa cikin ransa yace nasan za ki Ai kata shashashar yarinya kawai A fili kuwa sai ya cigaba da janta da zance A daddage ta dinga Amsawa kamar me ciwon baki barin gurin yayi ya karasa can babban falon yana fadin " wai ina Nene ne"? Ga kawarta na kawo su gaisa" yafada yana zama gefe Aliyu "Ayya Ai Nene ta tafi tun she karan jiya" ummi tafada tana kallonsa' "ta tafi " faruk din ya mai mata maganar yana dariya ummi tace "kwarai kuwa girgiza kai yayi yace "lallai Nene A she da gaske take dama dariya ummi take tace "kasan in dai tafadi magana to babu ja Aciki" girgiza kai yayi yace "ita tace A kawo mata'Nafisa su gaisa A she babu rabo" "Ai kam dai sai An hadu wataran A gaisa tunda ba dai na zuwa tayi ba" "hakane" faruk din yafada yana gaishe da ummin cikin girmamawa'

Ita ma cikin mutumci ta Amsa tana tambayarsa mutanen gida da Sauran" yan uwa yace wallahi kuwa lafiya lau ummi yawwa masha,Allah ummi tafada sannan ta juya suka cigaba da hira ita da Nafisa Na'ima ce kawai ta dawo falon ita kam Siyama daki ta nufa so take ta hada " yan ko matsanta yau take son barin gidan domin tafara' zuwa ta Ai watar da Abunda ta shirya

"Kai mutumin kana hutawa" faruk yafada yana mikawa Aliyu hannu hannushi ya mike masa suka cafke irin na Abokai Ya yunkura ya tashi daga ki shingidar da yayi yana mai da wayarsa Aljihu ya kalli faruk din yace "har ka gama zubar da girmannaka kai duk inda kaga taron mata ka dinga rawar qafa kenan ko kunya ba kaji ka tsaya gemai gemai da kai A gaban wadan can yaran kana wa she baki wai kai wane irin jinsin mutum ne' A cikin jerin mutane'iyi"? Yafada fuska babu walwala hararasa kawai faruk din yake ya marasa tace wa wai shi yake cewa shi wane irin jinsin mutum ne' baya duba kanshi shi A cikin wane jerin jinsin mutane nen zai saka kansa sai da ya mula sannan cikin murya kasa-kasa yace dan ba yasan ummi taji' wane topic suke yace "An tsaya din kasa kani A jerin duk jinsin mutane da kaga dama An so matan dan iska kawai kai har kana da bakin da zaka yi wannan zancan" faruk din ya fada A kule shiru Aliyu yayi ya bar maganar tasha ruwa yace "tashi mutafi" yafada yana duba A gogon shi "Anki din wai me ma zai kaika gurin dr hashim ne''? Gaka dai radau da kai kace kuma baka da lafiya ko wa zaka raina wa hankali oho'' faruk din yafada tana dauke idonsa daga kan Aliyu

"yaya Aliyu ina kwana" kallon Nafisa yayi A karo na farko tun zamanta A gurin yana ya mutse fuska yace "yanzu kikaga da mar Gaishe ni ko ko kema ya koya miki halin nasa"? tana murmushi tace " yi hakuri Oganmu Ai bai isaba shi din me' Ai nazata bacci kake ne danaga idon ka A rufe " "ina kallonki da ido daya tunda kika zauna gurin bacci da safiyar nan sai kace wani irinki " yafada yana mata murmushi "Ayya Nima bana baccin safe ya Ali'' harararta yayi yace "kin mata sanda naje nai ta bugu na kai A wa daya A tsaye baki bude ba sai da mijikin yadawo ya haura sannan muka taddake kina ta bacci ko"? Cikin mamaki Nafisa tace "yaushe hakan ta faru yaya'Aliyu bansani ba" still' da murmushi A fuskarsa yace "kin manta dai yarinya ki zauna ki tuna ko ki tambayi mijinki gashi nan A zaune shi be manta ba Ai"

Faruk ko haushi duk ya qume shi ganin yadda Aliyu yake ta shirma Nafisa ita kuma takasa ganewa sai biye masa take kallonta yayi yace "yaushe ki ka koma marokiya ne iyi sai faman yi masa banbadanci kike harda cewa wani oganmu' oganki ke kadai dai ni wannan ba oga na bane'' yafada yana gyara kwalar rigarsa kin tsaya kina biye ta tashi kamar baki san karyarshi ba wallahi sai ya mai dake mahaukaciya yanzu in dai Wannan ne yafada yana dukan ka fadar' Aliyu ransa A 6ace

Me Aliyu zaiyi in ba dariya a ba ya dinga yi yana kallon faruk din wanda yaci mur yaki ya kalli inda yake balle ya tan kamasa sai da yayi mai isarsa sannan ya kuma kallon faruk din hade da kara kallon Agogo dake daure A hannushi ya mike tsaye yace "in kagama shan mur din ina jiranku A waje " ya sa kai ya fice daga falon bayan yayi wa ummi sai ya dawo

Kwafa faruk din yayi yana kallon Nafisa wacce suka kacame da hira da Na'ima dan Ummi ta tashi daga gurin yace "tashi mutafi in kika samu hira ba kya gajiya ke Dariya Na'ima tayi tace "kai yaya 'faruk yaushe rabon damu hadu kasan in muka hadu sai Allah" Sakin fuska yayi yace "Ayya yanzu zamuje hospital ne kibari zan kawi miki ita ta yini har sai kin gaji tana dariya tace "kafin kama kawota ni na zo dan nasan fada kake" dariya yayi yace "haka dai kika ce "yafada yana kokarin fita yace in ummi ta sauko kya gayamata mun wuce kinji ko "ok zan gaya mata in sha Allah"

A cikin mota suka tadda Ali' ya zuro kafarshi daya waje daya na ciki yana sauraron wakar mutuniyarshi janeefer cikin wakarta me taken (na nanaye) idonshi A rufe motsin mutum yaji yasa shi bude ido daya yana kallon faruk din wanda yake kokarin bude motar ita kam nafisa tuni ta kame A kujerar baya gyara zama yayi yana mika wa faruk din key' din motar yace "waye drever ka kar6i key' kaja matanka ka bani wannan kujerar da kake zaune banza faruk din yayi masa yasa hannushi can kasan motar yana laluben jarida" fuska babu walwala "kar6i mana Alin ya kuma fada A karo na biyu yana dariya kallonsa faruk din yayi A karo na farko ' yace "wai kai meyasa baka da mutunci ne iyi"? A gaban iyalina kake yi min wannan Abun sai kace wani yaron ka " "to da meye" Aliyu yafada yana kokarin tashin motar faruk din yace "kar kayi dreving din mana wallahi sai na rama" 'kai kasani" murmushi Aliyu yake yace "sai dai karame'' Alhaji" yanzu ma A rame kake sabida kasa jaraba cikin ranka banza faruk din yayi masa ya ciga ba da duba jaridarsa haka dai suka je Asibitin Aliyu yana ta faman jan Nafisa da zance faruk kuwa yi yayi kamar bai san yanayi ba kai tsaye ofis din Dr hashim dama Aliyu yayi mishi magana tun jiya yace zai zo misalin takwas ko tara yana zaune yana duba wasu takkadu sukayi sallama tashi yayi tsaye yana dariya yace " mazaje mazaje," wannan in ki yarsu ce tun suna yara hannu Aliyu ya bashi suka tafa suna Dariya haka shima faruk din' kallon "Nafisa yayi yace "Aa madam bissimilla mana'' yana nuna mata kujera fuska A sake zama tayi tare da gaisheshi lafiya kalau "ya jikin naki"? "Alhmdulilah doctor" "to masha Allah" ya fada

"Kai mutumin haka Akayi A she"? Yafada yana kallon Aliyu " naji dadin nasara da A kasamu wallahi na kawo karshe wannan badaqala data ki taqi cinyewa sai ta sanadinka jiya na saurarin jawabinka A tv sosai naji dadi sosai Allah ya kara daukaka Ameen"

Hade baki sukayi gurin Amsawa da Aliyu da shi faruk din cikin farin ciki sosai 'Aliyu ne yakalli Doctar hashim yace" kai gashinan fa iyalinshi ya kawo ka dubata yadda ya kamata kasan yakusa zama dady" yafada yana kallon faruk din yana dariya

Dariya Dr yayi yace " kai sai yanzu kasani Ashe? ka zauna Kai Ai kowa ya wuce ka kazauna kana faman tuzuranci sai faman banka wa kanka kwaya kake da ranka da lafiyarka' sannan da kuruciyarka''

"Rabu dashi da Allah hashim kana batawa kanka lokaci ne Ai baya ro bane shi daza A dinga faman magana daya babu ji babu gani kar yayi Auran mana lafiyarshi Ai bata wani ba"

A dage Aliyu yake kallon faruk din yace " Ai ni ban isa Aure ba da kake cewa ni ba yaro bane yaro ne mana A kanka tunda ni ban san Abinda Ake yi ba har Asamu ciki"

Yafada yana sosa kunnesa da key din mota dariya hashim kawai yake yace "kai fa baka da mutunchi Aliyu har yanzu kuna nan da halinku ko daga kai harshi faruk din" "dallah inzaka rabu da shi karabu dashi malam" faruk din yafada A kufule idanshi A kan doctor yace "kaje ka duba miin mata kun zauna kuna
faman wani zance " kallonsa Aliyu yayi yace "sorry baban boy' me ka keso Ayima iyalinna kane"? Duka faruk din ya kaiwa Aliyu yace "yafa isheka wallahi " wai yau dame katashi da shi ne iyi" ? dan iska kawai me fuska biyu wataran sai kayini ba kayi wa mutane magana ba sai kace wani kurma yanzu kuma kana nema ka' buwayi mutane "

Tashi dr yayi ya nufi kujerar da Nafisa ta ke kai yace "Ai kun saba dama kai faruk man tawa kayi ko lokacin da muna pramary' skull haka kuke yi ha A dunga tunani fada kuke' A class sai daga baya A ka fahimci ba haka ba ne"

Kallonsa Aliyu yayi yace "don Allah duba mana ita da kyau tana yawan kwanciya ga shi bata san cin Abinci yace ko ba haka bane "? idanshi A kan faruk yace " ka tambayeta mana gata nan Ai A gabanka ok "
Chapter 30 · 0% Book details