← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 35

Sashe 13

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya lau dija ya karatunki " ? Yafada yana sata a jikin shi yana bala,in tausauyin yarinyar kasan cewarta marainiya batasan iyayenta ba. Shikam dan dai nene tafi karfi shine amma da babu dalilin da dija zata zauna babu cikakkiyar makaranta wallahi ya kewa yaran wasu ma ballantana wannan daya ke jin kamar shine ya haife ta

Itama dijan kwanciya tai a jikinshi ,tace " abba karutu alhmdulilah"

Na'ima dake gefe tace "abbah ni an manta dani ko?

Tafada da yanayin shagawaba. Murmushi abbah yayi yace "nina,isa zo nan mai babban suna nimatullah ya fada yana mika mata hannu shi

Cikin dariya taje itama tace "abbah an dawo lafiya ya fama da jama,a?

"Alhmdulilah mun gode Allah "

Nene kam baki tasaki tace "o ni "yasu "!

"Haka ka ke wa yaran nan bashir iyi "? dariya abban yai yace "menayi musu nene "?

"Yo ai duk abinka mata ne ko wacce aure zakai mata ato in banda abu irin na zamani ai mu bama kallon "yan yanmu mussaman nafari"

Murmushi abbah yayi sabida yasan za,a rina yasan halin nene duk da itama fada kawai take domin itama tana da bala,in son yayanta dan dai tana da kawaici ne kawai

Yace "shine dalilin dayasa nake jansu a jiki ai nene ganin basu da wani sai ni gashi ko wacce miji ya na zuwa aure zan yimata "

Dole in tausaya musu,,

Yafada yana kokarin tashi daga gun yace "nene zanje inwa watsa ruwa magariba ta na neman yi "

"To a sauko lafiya" nene tafada hankalinta na kan tv da suke kallon

Ummi ce ta fito daga khicin tace " naji kamar abban yara ya shigo ko?

"Eh yanzu ya hau sama "

Itama saman tabi shi cikin sauri ,,

Yana shiga dakin itama tashiga

"Sannu da dawowa abbah"

Juyowa yayi yace " yawwa dama kina kasa ashe "?

Tace "shiga ta khicin kenan naji shigowar ka"

An dawu lafiya?

"Lafiya lau "ya fama da hidimar mu" yafada yana mata murmushi

"Alhmdulilah Abbah ai akin lada ne" tafada tana kokarin Shiga toliet tasan wanka yake son yi

Ruwa ta hada masa tafi to mai da duk abinda zai bukata

Sannan ta fito yana zaune gefen gado yana cire a gogon dake daure a hannusa tace "abbah an hada ruwa wanka jikin sef din dake manne a bangon dakin ta nufa ta ciro mai jallabiya mai yankaken hannu ta a jiye a gefe.

Yace "sannu uwar gida uwar Aliyu haidar zakin fama,

Yafada da murmushi a fuskarsa ,itama murmushin take tace" abbah kenan"

Yace "akwai magana ne " "ehe ai gaskiya na fada dariya tayi tace" to wa yace ma kayi karya"

"Yawwa akwai maganar dana keso mu tattauna zuwa anjima game d Aliyu ne"

Kallonta abba yayi yace "wani abin ne??

"A,a akan maganar siyama ne?"

Tafada tana kokarin barin dakin sabida ta daura musu Abinci shida Alin tunda bata yadda yaci na asabe wannan tsarinta ne

Bai ce komai ba shima ya mike yashege toliet din

Sakkowa ummi ta taddasu suna zaune har yanzu tace "Na'ima bakuji Kiran sallah bane yakamata kutashi haka "

"Eh ummi yanzu zamu tashi ai"

"Ba ruwana wallahi Ali ya fito yattada ku anan kar wacce ta nemeni" Ummin tafada tana kokarin shiga khicin

Cikin sauri Fa,iza ta tashi. Tace "ai kam dai dan dazu nene ce ta cece mu. Daba dan itaba da sai munsha rankwashi ko ya murmurde musu hannaye haka yake musu in suka yi wani abin

Tace "Dija muje muyi sallah ko"

Tashi dijan tayi tace "muje dakin nene muyi a can"

Kai tsaye dakin da nene take suka nufa

Ita kam Nai,ma tanan zaune to bata sallah prieod take sabida haka zama ta gyara wayarta ce a hannuta nema layin siyama take sai ace busy

Tsaki tayi a karo na biyu ta kara gwada kiran wayar

"Hello Siyama"

Daga bangar siyaman itama tace "ya akai ne kanwata " tafada tana dariya dan tasan Na'ima n ta tsani ta ce mata kwanwarta

Cikin bacin rai Na'ima tace "wai ke dawa kuke waya ne tun dazu nake kira busy"

Dariya siyama tayi tace "Wata friend dina ce wallahi iyabo damu kayi skull tare "

"Ok. Ya Ali fah yadawo dazu"

Ihu !! siyama tayi tace "da gaske kike?

"Ba yace sati biyu zai yi ba" ?

"Eh wani aiki ne yata so musu ya zama dole sai dashi shine dole yadawo tare ma suka tawo da nene"

"Kai sistar naji dadin labarin nan naki wane tukwici zan baki?"

Dariya Na'ima tayi tace "kedai kin shiga uku akan namiji kike haka wanda bai san ma kinayi ba"

"To ya zan yi Na'ima Allah jarrabeni da son yayanki shikam naga kamar baya ra'ayina"

To itama Na'ima tasan gaskiya siyama tafada ya Ali baya ta tata sabida haka cikin rarrrashi tace "ki kara hakuri komai zai yi daidai kinsa ya Ali al'amarinshi sai shi wani baudandan mutum ne sabida haka ko yana son ki baza nuna ba"

"To ya zanyi don Allah kidinga shigar dani a gunshi kinji sistar na " siyaman tafada cikin kwantar da murya

Dariya Na'ima take tace "rufan asiri in mutu maza su kaini"

"Wai ance wargi ma guri shika samu ke dai din da kikaga zaki iya bissimillah mu dai. "Yan addu'a ne"

Daga daya bangaran siyama tace "haka zamuyi dake ko?"

"Ai anyi angama ma wallahi bazaki sani a jarfar ya Ali ba a yanxu ma ya , aka kare
Kizo kici gaba da kafa gwamnatinki ko Allah zaisa a dace"

Ka she wayar Siyama tayi tace "mara mutunci nasan ta inda zan bullo muku da ku da ya Ali"

Kai tsaya dakin Momyn ta ta nufa ta tadda ita a zaune gefan gado tana waya da kawarta hajiya ladidi, ta zube kan bed din tana sauke nuffashi,Momy tayi saurin kashe wayar tana kallon "yar tata tace"ya aka yi ne naga kin shi go kina bacin rai ,nifa na tsani in ganki cikin damuwa my daughter"

Siyama ta mike zaune tana ya mutse fuska ta ce "Momy kinji ya Ali ya dawo ko ,yanzu wane shiri za muyi"?

Momy ta aje wayar kan mudubi tana kallon "yar tata tace"ai tashi zakiyi ki shirya ki cancada kwalliya ta ban mamaki ki dira a gidan domin naga yaron nan in ba haka mukai masa ba a kwai Matsala na lura yana da taurin kai"

"Humm! Wallahi momy har narasa yadda zan bullo masa duk wani dabaru na a kanshi sun kare"Siyama tafada tana tausayawa kanta

"Ai baza mu yi kasa a gwiwa ba ki ci gaba da kokarin a kanshi ,in yaqi zamu bullo masa ta bayan gida kawai,tunda shi yace dan taurin kai ne"

"Yawwa momy dama haka kukayi masa wallahi domin zuciyata tana azabtuwa da so da kaunarsa ,shi ko nunawa yakeyi kamar bai damu da ni ba"

"Ai yanzu nan muka gama magana da Hajiya ladidi a waya tace min tana kan hanya ,zuwa nan, zamu shirya yadda komai zai zo mana cikin sauki"

Farin ciki ya lullube Siyama ta rungume Momy nata tana fadin "shiyasa nake sonki momcy na wallahi sabida kina son abinda nakeso"

Dariya Momy tayi tana farin ciki ganin diyar ta tana farin ciki tace"ai duk inda zan shiga in fita zan shiga ,domin in ga kin auri yaron nan ko da zanyi yawo tsirara sai burinki ya cika ,kuma da ke kadai zai zauna babu kishiya ,kamar yadda nake zaune ni babu kishiya"

Siyama ta riqa murna tana ganin burinta ya kusa cika zata auri gwarzon maza Aliyu zaki mazan fama ,mutukar ta aureshi tasan ta gama dacewa,kuma tasan halin momynta inda tace zatayi abu za tayi

Sabida haka mikewa tayi cikin qwarin gwiwa tace"Momy bari naje na shirya kawai na tafi"

"Yawwa dota kiyi sauri kinji ko kiyi wanka sosai yadda zaki dauki hankalinshi"

Dariya Siyama tayi lokacin da take kokarin fita saga dakin momyn nata,tace"sai momyna wallahi Allah ya bar minke"

Momy ma dariya tasa tamkar wata ma haukaciya

Cikin wata atamfa ta fito da gani a tamfar mai tsada ce sosai, amma dan iskanci anyi mata wani mutsiyacin dinki ,wanda ya fito da sassan jikinta ko ina gashi nan mussaman kirjinta duk sun bullu tso ta saman rigar ,da ta daga hannu hammatar ta a waje sket din ya da meta sosai ,kanta ya sha karin gashi kafarta sanye da wani takalmi mai tsayi ,ta fito hannunta ruqe da key din motarta sai karamar jakarta pose sai taunar cingam take klas!kas!las!

Cikin farin ciki Momynta tace"gaskiya kinyi kyau my douhter ,kin ga yanzu ko shi waliyi ne dole in ya kalleki ya kwadaitu dake ,dama nasan yarinya ta bata wasa ba ce"

Siyama sai dariya takeyi cike da farin ciki yadda momynta take kwarzanta kyawunta

Har har waje nomyn ta rako ta sai daga taga motarta ta fita daga gidan sannan ta koma ciki tana tafiya tana magana ita kadai tamkar wata shashasha

lokacin da siyama tashiga gidan ana tafaman kiran sallahr isha'i bayan baba mai gadi yabude mata get din kai tsaye danna hancin motar tayi cikin far fajiyar gidan

Tana kokarin gyara faking shi kuma Ali fitowarsa kenan da nufin zuwa massalaci
Hannu makale da carbi irin mai dannawa nan kallo daya yayiwa gun ya fahimci motar siyama ce

Tsaki yaja ya wuce aransa yace wannan yarinyar bata da hankali meya kawuta da wannan daran oho

Mikawa baba mai gadi hannu yayi suka gaisa ya ce " Abba yafito ne?

"Eh ai bai shigo ba yana jiran ya sallaci isha ne kasan cewar tun fitarsa sallar magariba bai shigo "

Bai ce komai ba shima ya nufi ma sallacin

Ita kam siyama ta ga lokacin da ya fito sai taji wani bala,in tsoro da fargaba ya kamata kasan cewar taga ko kallo bata ishe shiba

Cikin sanyi jiki damutuwar jiki fito da ga motar jikinta a sanyaye ta nufi cikin gidan,,

Duk suna zaune. A falon har jameel ana ta hira sai dariya ake
Chapter 13 · 0% Book details