← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 35

Sashe 24

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh gwara ki ci mun mutunci tunda kin ganni A gidanku 'duk A binda kukayi min ba laifin Ku ba ne 'nawa ne tunda ' ni na kawo kai na,
Wai kamar ni Ali' zai zage ya Zane da blet A gaban yara, Wannan 'wulakanci da me yayi kama "

Wata dariya CE ta su6ucewa 'Na'ima ba shiri ta dinga kyakyatawa dama ta Dade tana kunsheta' taki yi ne don' kar Siyaman taji haushi 'Amma yanzu Kam ba zata 6oyo ba

Sai da tayi mai isarta su Dija suna taya ta ita Da fa'iza. Domin ita ma A gaban idon ta komai ya faru

Kallon Siyaman tayi tace " Allah ya baki hakuri sis kinga da tun lokacin da nake tashin ki ne kin tashi da duk haka ba ta faru ba'' gashinan" kinsa A n Zane ki babu Gaira babu dalili "

Banza Tayi da ita da ta fuskanci 'zolayar ta take

Ta yun kura ta tashi 'tashi ga 'toliet domin jikinta yai bala'in zafi da radadi da take Mata dama fatar ba wani kwari ne gare ta ba kasan cewar tasha 'bleecing da sabulai Masu masu karfi da ta ke Amfani dasu

Sai da suka tabbatar ta shige 'toilet din suka kyalkyale da dariya, Dija har da faduwa daga kan gado, tana gwada yadda Siyama Ta dinga Gan tsarewa lokacin da yaya Aliyu yana dukanta

" Zan ci ubanki 'Dija wallahi in baki bar wannan Dariyar ba duk ba ke kika jawo mata iye"?

"A,a wallahi ya'Na'ima ita CE dai ta jawo wa kanta da taki tashi tayi sallah da kuma Al hakina bata na jin dadi back jiya A n dake Ai Allah ba Azzalimin sarki. Bane 'gashi Allah ya sakamin Nima"

"Kwarai kuwa hakane Dija"

"Ammafa 'INA kuma gargadinki' kirage gashin kunya da tsiwa kinji ko kuma daga yau 'kar ki kuma ,raina ta ' tunda ba sa'arki bace ita "

"To ya Na'ima bazan kara ba in sha Allah ' in kawai ji nayi na tsaneta wallahi shiya na ke raina A mma daga yau bazan karaba "

"Yauwa kanwata. Daga yau 'tsanar da kike yi mata ma ki dai na kinji ko' domin,(Annabi Muhammad Slw ) yace duk inda musulmi yake Dan uwan musulmi ne yace kada musulumi ya 'kyamaci" Dan uwansa musulmi ' sabida haka ki dai na babu kyau ki dinga karrama 'Dan Adam ko Da ko baki San . Shi ba"

"To ya Na'ima in sha Allah Bazan karaba '' "yawwa shiyasa nake sonki kanwata sabida kina jin magana ta ' ku kuma kuyi kwanciyarr ku zuwa bakawai Sai in tasheku ke fa'iza kin San A kwai skull ko"?

"Eh ya Na'ima" " to'kar kiyi bacci mai nauyi ''Na'ima tafada tana gyara kwanciya ita ma domin ita kam Allah yasa mata son bacci A rayuwarta '. Domin wani lokacin ko karyawa batayi da safe tana can tana faman bacci Sai ta tashi sannan. Take kar yawa wani lokacin kuma sai dai taci Abincin ' rana kawai

To Aliyu' bayan fitarshi daga dakin su Na'ima kai Tsaye sama ya nufa dakin Ummi A gurguje domin 'karfe shida ta wuce tun dazu yana fitowa daga masallaci' ogansu' yake ta waya ,ya fito da wuri Domin baya San takwas tayi basu bar garin ba.

A gurguje suka gaisa da 'ummi tana ta yi mishi Addu'a tace " baza ka tsaya ka karya ba sanan "

"A,a ummi nasha lipton ya isa kamar ya ,isa" "tsaya in dauko maka shauran dabun nama da ma yau nake cewa ' zan hada wani sai kata fi dashi'"

"Ok ' ummi da kin barshi ,bazamu rasa A binda za muci ba" " A'a gwara kata fi dashi' in kai baza kaci ba Ai Akwai masu ci tun da kuna' da yawa
ko"?

"Hakane ummi" yafada yana duba A gogon da ke daure A hannushi "

"Bari mu gaisa da Nene " yafada ' yana kokarin sauka daga kasa itama bayansa tabi suka sauka tare cin karo sukayi da Abba ya dawo daga massalac dama shi ka'ida ne ' baya shigowa sai gari yayi haske sai yayi Azkar sosai A massalacin 'sannan yake dawo wa gida A kwai mabukatan,da suke kawo masa kukan rashi da na wannan yanayin rayuwa da muke cikibna tsabarta lauci da rashin Abinyi' don' haka " yana zama' yayi ta' rabon kudi' dan wani' lokacin ma har kayan Abinci yake sawa 'A fita r dashi ga mabuka ta

Kai tsaye ummi kchin ta nufa ta barsu suna Anan suna kara gaisawa "har ka fito kenan?"

Abban yafada yana mika wa Ali hannu domin suyi musabaha

"Eh wallahi' in banda 'lyara nan sun tsayar dan Ai da tuni mun yi nisa A hanya
Rigama natarar dasu sunayi har da ko kawa''

Kallon sa Abbah yake yana mamakin wane yara ne suke rigima har da kokawaA junansu' shidai ya san ba tarbiyarsu Na'ima bace haka

"Wan yara ne wannan?" Abban ya fada yana kallon Alin ,tsaki Ali yaja yace " waye in ba wannan ,yarinyar ba ita da Siyama sosai rigima suke tun jiya taki karewa"

Cikin mamaki Abba yace "Siyaman ce take ko kawa da 'Dija' dan zubar da girma'?

Tabe baki Ali yayi yace "kwrai kuwa " "to' meya hadasu"? In jiAbbah murmushi Ali ya yi shifa Dija ta birgesh wallah da tayiwa Siyama haka yaji dadin watsa mata ruwa da' tayi in ban da' rashin tarbiya kamar Siyama A ce bata yin sallah A kan lokaci' sai da rana ga tse ga tse

Tsaki ya dan ja kasa - kasa yace ''ita Dijan ce ta watsawa ,siyama ruwa wai ta tashi ' tayi sallah, kowa ya tashi to shine siyaman ta hau dukanta''

Dariya Abbah ya saki yace" Amma yarinyar nan ta burgeni'Ai haka Ake ma' irinsu Siyama suka qi tashi' ta dadi' rai' in suka ji su' A cikin danshi Ai kaga sa tashi dole ko''

Girgigiza kai 'kawai Ali yayi bai ce komai ya kama hanyan dakin Nene

Tana zaune A kan sallaya haannuta rike da carbi ' ya shiga dakin' cikin' sallama' gyaran murya tayi tayi masa Alama ya zauna tana nu na masa ta kusa kammalawa

Murmushi yayi ya samu gefen daddumar da take kai ya zauna hade da ciro wayarsa faruk yakira bugu daya ya daga ya ce "ya akayi ne' kafito ne"?

"Eh gani Akan hanya kaifa''? Faruk din yafada

"Ga nin gurin Nene bata gama sallamata ba' har yanzu'' Alin yafada

Dariya faruk din yake yace kami kamin gaisuwa gun uwar gidannan ka"

"Ok ' zata ji in sha "Allah nima yanzu zan fito' in sha Allah "

Kashe wayar yayi yana kallon Nene wacce ke kokari cire hijab din da tayi sallah da shi' tana kallonsa tace " badai har ka fito ba"?

"Eh man ')Ai lokaci ma ya kure' mun so mu fita cikin dare ko da A subah hakan bai yu wu bah "

"Hakane Nene tafada tana girgiza kai tace wannan Ai kin naku Ai sai Addu'a da ku wane' lokaci kuna tsaron rayukan jama'a ni ban san wanda yafi' wani taimako ko da ma'aikatan 'Asibiti
Allah dai ya tsare ma na ku A duk inda zaku shiga"

"Amen ya Allah my love dina " Alin yafada fuskarsa cike da da riyar da ya dade bai yi irin ta ba'

Harara Nene ta maka masa tace '' wace ce kuma my love A na zaune 'lafiya"? Dariya ya saki yace "Ai kinji irinta ke baki iya soyayya ba dan na ce miki my love kike harara ta ina da wata ne bayan ke"

"A'a bana so Ni ba Ar ni ya bace ka dai na ki rana da sunan Arna to kaji'"!

Me Ali zai yi in ba dariya b sai da yayi mai isar sa sannan yace " toum shikkenan kada 'in kawo Amarya ta kiji 'l ina kiranta da haka kice, ban miki A dalci ba babu ruwa "

Ita ma dariyar take tace"e naji din kuje ku karata da in dai za kai Adalci Ai shi kenan"

Girgiza kai yayi yana 'cigaba da dariya shi kam yana bala'in kaunar kakarshi Nene kamar yadda take kaunars da damuwa Al' amarinshi' shiyasa baya iya sakewa da kowa' in ba ita ba zai zage yai ta zaulayarta yana kwasar dariya' domin ' ita ke ganin dariyarshi' A arha

"Kin ga kin zaunar dani zaki sa na kara bata lokaci na ko gaisawa,ba muyi ba kin fara rigima "
Yafada yana kallon A goga hannusa

"Ka tashi ka tafi ga faruku can' yana jiranka ko bada shi' zaku tafi bane ?"

"Tare zamu muna da yawa sosai Ai ba shi kadai bane " yafa da yana mikewa ita ma mikewa tay' ta biyo bayanshi tana ta faman yi masa Addu'a iri -iri

A gurguje ya karbi tarkacen kayan da ummi ta hada masa naci kamar wani ,yaro shi kanshi' yana mamakin,yadda umminshi take kula,dashi sai ta tabbatar da yaci Abinci hankalinta yake kwanciya shiyasa bashi da'Abinda zai saka wa da iyayenshi da shi' sai Addu'a

Sai da suka rakashi har gun motarsa suna yi mishi Addu' a sannan suka koma cikin gidan

*to Aliyu haidara Allah ya tsare Allah yabada nasara*

Misalin bakwai da rabi Aliyu ya shiga brack din nasu dukkanninsu suna tsaye ,A jere ogan yana kuma horar dasu cikin sauri yayi faking din motar ya fito yakarasa gurin ,Akaciga ba da yi dashi

Sai bayan sun kammala sannan sukayi Addu'oi suka dau hanya cikin shirin ko 'lta kwana, jikin su sanye da bindigogi

To A can gida kuma Cikin sanda'Dija ta ta shi tana yiwa Siyama dariya har da gwalo bayan ta tabbatar da bacci ya dauke Na'ima sarai siyama ta fahimci Abinda take mata Amma sata kyale ta cikin ranta tana saka irin hukuncin da zata dauka'Akan Dija dominwallahi ko za tai yawo tsirara sai ta sabautawa Dija rayuwa sai taga da wanda take'taqama, A doran duniyar na

Fita tayi Daga dakin tana cigaba da Dariyar da take babu Abinda yadameta dakin Nene ta nufa tana cigaba da dariyar cikin walwala

Cikin mamaki Nene take kallon Dija"tace ke kuma meye yakawo ki inda nake har kin gama gabar da kike dani?"
Chapter 24 · 0% Book details