← Book details Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 36

Sashe 27

Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ganin har lokacin Allah bai kaddara samun haihuwata ba sai nashiga damuwa sosai tsorona guda dayane kishiya Nabi na rame harma kakan iya fahimtar ina cikin damuwa dan duk lokacin da ma ch
yabani wayarsa to akallah sai naga messages na mata sunfi a kirga Amma abun mamaki bana taba ganinsa yana chatting dasu hakan yasa dai nakasa kwanciyar da hankalina na damu sosai dan gani nakeyi mai wadata irinsa ai karyane ace baya soyayya awaje shiyasa wata rana bayan mungama level 100 yayimun fada akan ban fito da wani abun kirki ba bayan da fari yaga na dage Nan nasaka masa kuka nace nidai danAllah dayake yana bin
ammata awaje gwara ya auro wacce yakeso.

Ranar yayi murmushi ya kalleni baice komai ba " daman nasan kana kule kulen mata dan ina ganin sakonninsu aci
in wayarka ai dole kayimun murmushi ai Nidai ko meenal ce kadawo da'ita da
inka tunda nasan yadda kake kaunar haihuwa ai." " Meenal ai tayi aure yafa
a yana kallona." Adan firgice nace wanne aure kuma." " Am serious yafa
a." Sai naji tausayin kaina kawai dan ganowa nayi idan nice ita ina zan samu wannan gatan sai shedan yashiga rayamun nima idan fa nayi masa wani karamin laifin zai iya aikani gida daga ranar na takure kaina duk da tante tana min fa
a sosai akan nadaina saka lamarin haihuwar nan akaina tunda anyi na asubutin anyi na gidan amma shiru.

Bankara shiga damuwa ba sai ranar da fannah tazo da yaranta guda hudu wanda ranar naga yadda mutullab yake masu saboda kauna dan yaran dady suke cemasa ma kamar yadda suke gayawa jalil duk da naso abani amira tana jaririya wanda har jalil din ya amsamin amma ganin yadda naga kamar fannah din bataso ba yasanyani jan bakina nayi shiru bankara magana ba bansan dalilinta nahaka ba shiyasa tsakani na da yaran wasa da alkhairi dan yadda mijina ke yimusu hidima ko yaransa karshe kenan dan sai yazamana ko umara zamuje hardasu yake biya amma ni ko da wasa bai taba yimun maganar haihuwata ba a wannan lokacin ne afrah ta haihu itama namiji akasa sunan uban mijinta ansha buduri badankarami ba dan ashekarar suka bar kasar ma suka koma London ita da mijinta da yaronta wanda da ki tayi sai da yan uwan suka sakamata baki, ganin yadda yaga inashiga damuwa wata asabar yadawo daga tafiya ya rukunkumeni yana fadin " DanAllah kidaina dagamin hankalinki mon amour Wallahilazim ko zamu shekara d
ari baki haihuwa ba ban tuhumarki nasan ubangiji babu ta inda baya jarrabar bawansa mu cika da Addu'a kawai sannan ina rokonki da Allah kidaina damuwa da matan da suke aikamin sako a waya dan ko inaso banaso sai sun aiko koda banda kudi Aicha kyauna da Allah yayimun kadai mata zasu iya bina ballatana kuma inada kudi dan haka kada kikara yaudarar kanki wai yammata basa sona amma inaso kisani bazantaba cin amanar aureba kuma ina rokon Allah yakareni daga duk wata fitina ta mata kwanaki da kikayimun magana nayi murmushi ne saboda rashin sanina da kikayi dan da kinsani bazaki ce wai ina kula kulan yammata ba Allah dai yakara tsareni." Tundaga ranar da mukayi maganar nan nasake sosai sai gashi na maida hankalina akaratu shikuma ashekarun baya zama sosai baga wannan kasar ba baga wancan ba gashi sau uku yake zuwa saudia umarar Azumi wanda dani dashi dasu jalil da yara harda tante da abba ake tafiya sai kuma ta maulidi shima dani ake zuwa aikin hajji ne akaje dani sau biyu nakarshen saboda karatuna ne bansamu zuwa ba.

Gyara zaman nayi akan kujerar inajin mugun mutuwar jiki dan dakyar natashi yau daga bacci daga na kwanta sai bacci danayiwa dada complain sai tacemin harda hutu kingama bokon nan ba dole ba hakan yasanya nima nadauka haka dan maganar aiki babu ita tun ina rokonsa har na hakura yanzu.

Matar walid da ita yaranta biyu yanzu itace ma take
an bani babbar tana wuni gurina harda kwana akwai lokacin dana zolayeta abarmin ita sai naga harda kayanta haka nacigaba da kula da yarinyar Amma sai na lura kamar kakar yaran bataso dan haka sai na mayar da yarinyar kawai bankara zancinba ita kuma bataki kawomin ita ba hakan yasanya nakejin sanyi araina sosai.

Duba agogon hannuna yasanya nayi saurin mikewa nashiga daki nayi wanka nan kamin nagama shiryawa nadan kishingida sai bacci ya kwashe ni nan gurin.
*****
Gaskiya bantaba ganin irin abokinka ba baban ammar " Murmushi yayi yace " Babu irinsa kaf duniyar nan mum ammar bantaba samun kyauta ba irin ta Mutallab saboda yadda yake kaunata kamar dan uwansa." " Wallahi nagani dubi motar nan fa mai kudi sosai ita yabaka kaduba kaga hidimar sunan ammar da yayi shiyasa nace maka da sunansa akasa." Murmushi yayi yace " MAM ai
an aljannah ne sunansa kuma next baby shi zansaka ai dolena su ummi ma bakiga yadda yake musu ba." " Kai Ai wallahi sambarka da haihuwarsa shidai kudinsa bai sanyashi tozarci ko wulakanci ba ni mamaki nakeyi da har yanzu bai kara aure ba ni nazata zai mayar da meenal ga shekarun sunja itama tanacan gidan mijinta wallahi Zargin matarsa nakeyi anya tabarshi haka kuwa." " Nima batun haihuwar nan yana damuna amma shifa ko ajikinsa wallahi kuma dakike batun matarsa shi aure yasan wani sirri naku na mata ne?" " kai Tabbijan kana wasa da mata wallahi ballantana ita daman kowa yasan asalunta." " Kada ki dauki zunubi abar maganar Addu'a zamu cigaba da tayasu shine abunda yakamacemu." " To Allah yabashi masu albarka."
*****
Sautin kukanta dake tashi a babban palon nata wanda manyan yaran mijin suna zaune kowannen su yana kallo batare da sun farga daga ku
an nata ba ko kuma nuna damuwarsu akan haka dayar tace " Nifa Anty mamaki kike ban wai baki daukemu amatsayin
anki ba." Namijin ne yace " Ke kada kikara sakamun wannan matar matsayin uwata tayaya ta'ina?" " Kada kasake kace zakayimun rashin kunya nagayamaka shikenan ni nazama ja
arku?

Kullum bautarku kamar jaka banida sukuni banida Nutsuwa duk abunda Nakeyi bakwa gani ahaka ake soyayya dazarar kunganni bangarena banda sirri sai kuce kunzo kallo." Tsaki dayan yaja maccen kuma tayi murmushi dan duk banza yanzu sun sakata kuka ai.

" Kada kakarayimun tsaki." " Nayi din..." Baba ne yashigo yana fadin
ai kai " Ameer?

Menene haka matar tawa?

Fitsara?." Da dan zafin kai irin na samarin dake tashen balaga yace " yanzu saboda Allah baba bamuda sukuni agidan ubanmu daga munyi abu sai laifi." Kuka maccen tasaka tana fa
in " Ni bamusan me mukayiwa anty ba baba bata sonmu kwatakwa bayan mumyn mu kamin taraso tana nuna mana kulawa daga zuwa bangarenta mu tayata hira ta rufemu da fada harda kuka baba danAllah idan laifi mukayi mata kace tayi hakuri maccen tafada." " Kai kai haba hanifa wanne magana kukeyi haka antynku na sanku kunji mamanku kuma ai
ar aljannace ita kunji Addu'a damu cigaba da yimata kutashi kitafi." Hanifa ce tace " Anty kiyi hakuri sai da safe." Kasa magana Meenal tayi saboda bakin ciki da munafurcin yaran .

Amma dai sau nawa zangayamiki ne akan banason ana takurawa yarana shekararmu nawa yanzu saboda Allah yakamata kisan abunda yake batamun rai shine naga ana wulakanta yarana suna kaunarki suna sonki Amma ke kina tozartamun su to bazan lamunta ba dan gidan ubansu ne nanan sunada ikon yin duk wani abunda sukeso nagayamiki banason hayaniya yau Alhaji mutallab asad zai dawo nagayamiki akwai kayan danakeson kwangila agurinsa nasamu zai ganni da safe kitayani Addu'a nagansa dan harka dashi akwai samu." Tana ganinsa yabar sashin nata hakan yasata shiga da
inta tana fashewa da wani rarraunan kuka mutallab kamar taji yace itakam tashiga uku.
Chapter 27 · 0% Book details