← Book details Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 36

Sashe 24

Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni anan babu kokarin da banyi ba Allah yasani har mahaifinku dai da yace natafi gida akan ina sakaki akitchen wai kada na
ona masa diya Allah dai yagani duk wanda yazageni zai sakamun dan nikadai nasan faman danasha dake akan girki daga karshe mahaifiyarki har takowa tayi tayimun kashedi!" Saroro meenal tayi batare datace komai ba tana rarraba idanuwa kamin kuma tace " To ai sau daya nata
ayin tuwo amma bamu iya ci ba." Wani kallo na takaici mumy tayi mata tace " Tayaya zaici tsakani da Allah ai duk kyan mace da isarta to wallahi taisa a tukunya dan darajar da girki ke karawa mata wallahi ba
adan baniba dan duk wata ta
ama da akeyi da isa da kwalliyar har soyayyar har ita kanta saduwar sai anci an koshi za'ayi yadda yakamata Amma miji ya auro macce babu abunda ta iya Narantse da Allah yayi hakuri da lamarinki meenal gashi da wadatar komai ai duk arzukin miji idan yan aikinki sun kai su goma acikin gida to yakasance girkin mijinki hannunki naciki shine cikarki macce." " To Ni mumy saboda Allah..." " kinga yaisa ni dan naga ke sai nayi da gaske kan batunki Yanzu wannan baking powder din dakika dakko fa?

Me zakiyi da'ita?

" kallonta meenal tayi tace " To mumy ba aciki zan saka ba." A dan hasale mumy tace " Ni nace miki kisaka baking powder acikin nama?

Wai meenal meke damunki ta'ina kika tabajin haka cake zamuyi ko tsami zamu cire malama maza ki ajiye ki dakko kayan spices dinnan." Zumburo baki tayi tana ajiyewa sannan ta dakko kayan spices din zata fara afawa aciki mumy tayi saurin tsayar da'ita tana fa
in " Dakata dakata kada ki juye mana haka zaki zubasu kwaya kwaya aciki?

Idan mijinki bayason ya taunasu fa?

Kinga wancan
an cardamon din ko star anise ko cinnamon su ake iya jefawa aciki shima irin su shinkafa jallop fried rice sauces da sauransu shima idan mijinki bayaso ki taunasu sai ki daka ki watsa ko in kingama dafawa ki cire.

Su kayan kamshi dandano da sirrin girki suke karawa sosai Amma kuma suna lallata abinci idan ba'a zuba bisa ka'ida ba.

" " To mumy wanne zan saka." " Tunda bamuda spices din zoki hadamana akwai dakko abun nima sai ki hadama spices na Nama da kifi da kaza duk abunda yashafisu sai asaka ko gashine ko farfesu ko pepper chicken koma dai menene.

A dan gajiya meenal ta kalleta tace " wallahi nagaji mumy please bari naje na kwanta." Dallah mata harara tayi tace " zaki shige kiji ki karasa ko sai na batamiki rai ." Tana turo baki ta dakko abun niqa.

Ga abubuwan da zaki zuba nan mumy tafara lissafo mata (BEEF,CHICKEN,FISH SPICES)
CITTA 1 TEASPOON
STAR ANISE HALF TEASPOON
CURRY HALF TEASPOON
GARLIC DRY 1TEASPOON
BAY LEAF 3PCS
CUMIN HALF TEASPOON
BARKONO 1TABLE SPOON
THYME HALF TEASPOON
CITTA MAI'YAYA HALF TEASPOON
DRY ONION 1TABLESPOON
CORIANDER 1TABLESPOON
BLACK PEPPER HALF TEASPOON.

Nan meenal tashiga zubawa tana fa
in kinji kamshi mumy har ta Nika mumy tasakata ta dakko wata roba ta zuba aciki kamin kuma tace mata " Zuba 1teaspoon acikin naman sai ki dakko tafarnuwa ki jajjaga kisaka da maggi knor da curry ko." Sai datayi yadda mumy tace sannan tadawo tana fadin " To mumy ai curry yakarefa." " Subhanallahi namanta jiya da ragowar nayi amfani Ai munada tumeric din ko?" " ni bansanshiba.

Bu
e lokar tayi tace " gashinan ki zuba abun nika
CURRY
CORIANDER 1TEASPOON
CUMIN 1 TEASPOON
BAY LEAVE 3PIECES
PEPPER (BARKANO) 5SPICES
GINGER (CITTA)1PCS
WHITE PEPPER (FARIN MASORO) 1TEASPOON
TUMERIC (KURKUR) HALF CUP
CARDAMON 5 pieces
CLOVE (KANIN FARI) 1 ki hada ki markada mana sai kizuba acikin container.

" Meenal ce tace " Gaskiya mumy kinyi wallahi kinga duk kin hada abunki da kanki." Banza tayi mata har suka cigaba da aikin batace da'ita komai ba sai da suka gama duk sannan tace shige ki kai abinci kan dinningsannan kizo ki hada lemo sai data kai abincin tanajin jikinta kamar ba nata ba sannan ta salalla
a ta gudu da
inta tana shiga ta rufo kofarta ha
e danna mata key tana jan tsaki tana fa
in " wallahi baki isa ki kasheni ba muguwa kawai dan ba diyarki bace ba kuduba aiki sai kace wata jaka wayarta ta dauka tashiga kiran numbar Mutallab amma bata shiga hakan yabata mutukar mamaki takira yafi sau goma amma bamata shiga kwatakwata.

Nan tashiga aika masa da text tana fadin " Idan kagama fushin naka kazo ka daukeni malam dan bazasu kasheni da aiki kamar jaka ba ta aika tana zaune tana jiran reply amma taji shiru kiranta dataji abba yanayi ne ta bata fuska tana fitowa hade da fadin tana tafe " Wakika barwa yagyara gidan?" Da dan mamaki ta kallesa tace " Nifa Abba ko agidana bana aikin nan tsakani da Allah tayaya zan iya wannan bautar??

Nidai gaskiya bana iyawa tafa
a..." saukar mata da da lafiyayyan mari yayi yace " idan nakara gayamiki mai yakamata kiyi agidannan sai na zaneki wallahi nagayamiki ki kama kanki kije ki gyara gurin yafada yana jan tsaki.

" tana kuka haka ta dakko mofa tashiga aiki.

Bakaramin shagali akayi asunan fannah ba ta inda yarinya taci sunan Mahaifiyar su jalil Ana kiranta da Anam.

Fannah dake tsaye tana kallon Aicha tace yanzu saboda Allah sai yanzu zaki shigo?

Tun yaushe nake jiranki tunfa ranar suna baki kara lekomu ba." Murmushi Aicha tayi tana zama tace " Yi hakuri mum anam wallahi abubuwan sunmin yawa sai da nasamo house help amma dattijuwa ce sai
ar karamar yarinya ga school nafara zirya kuma kinga su dada sai jiya suka tafi ga batun mai gidan duk da sun tafi umara yau sudasu tante da dada kuma nasan sati biyu zasuyi, Nariga nasaba sai bayan kwana niyu yake gurina yanzu kuma kinga kullum ne." " Ai wallahi kokarinki yana burgeni yadda baki hada mijinki da kowa Anty A
cha shiyasa nake koyi dake wallahi " To ba dole ba inada wanda yafeshi ne ai ko ciyarwar nan Anty fannah bakaramin abu baniba ballantana ga muhalli ga wasu hidindimun yau da gobe ba zagi ba duka ai kam sai abun agirmama idan kika biye ta batun kishinsa saboda
an mata bazaka taba zaman lafiya ba fannah dan wallahi Namiji ko mahaukaci ne akwai macce dake sonsa da haukansa shiyasa kullum nake addu'a ina fa
in Allah kada yabawa wacce macce sa'ar sabawa Allah kokuma sakashi acikin fitintunan nan na zamani." " Hakane anty Aicha nima Wallahi Bana damuwa da wasu yammata nasan mijina yadda yake dole asamu masu sonsa Allah dai yabarmu tare dasu yakuma tsare mana danAllah Abani sirrin da zanyi yanzu mana yar'uwa ." Murmushi Aicha tayi tace " wanne sirri." " Kai anty aicha." Dariya tayi tace " Kinyi ciccibi?

Kada
anta tayi alamar A'a nadaiji ummata tanafadin data iya datayimun dan ana fa
in kyansa sosai." " To ki samu kiyi ciccibi ki aika gurin masu nama kice abaki gaban saniya su wanke su gyara miki ayanko miki daga can sai ki dorashi akan wuta ki bashi wuta sosai dan yanada wahalar dahuwa sai ya dakko hanyar dahuwa kiyi jajjage ki zuba sannan ki daka ridi ki zuba ki zuba minannans sannan ki saka maggi kayan kamshi ki zuba nonon rakumi idan kina dashi ki barsu su game ruwan ajiki.

Ciccibi sai kici." Kallonta fannah tayi tace na matse fa." ai ciccibi yana matsi sosai fannah sai dai kikara da wannan asiyomiki alimun amma shi
adan ake sakawa da kaninfari da bagaruwa da sassaken bagaruwa da
an gishiri da ganyen magarya ki dafasu kiyi sati kina shiga ciki zaki ban labari." " aikam wallahi Nagode sosai sai tsumi danAllah tafada tana karya wuya." Wai ...." " DanAllah nidai ki bani mijina yanason kulawa da shinfida wallahi shiyace ma nagayami komai asiyo inyi gyara bayaso in zauna haka ban kula da jikina ba." " To fannah ai sakarar macce zata zauna bata gyara wallahi ai jikinmu sai da kulawa idan bahaka ba sai asamu matsala ai dole mutum ya dage ya kula bama bayan haihuwa.

Kinsam cucumber maganin mata ce sadidan a zamanance har ma da likitance to kisameta ki samu abarba ki samu kankana ki samu minannas ki samu kaninfari kisamu cinnamon kisam ki ha
esu ki dafasu sai ki markada ko ki murje kisha zakiga ikon Allah fannah." " NAgode sosai wallahi Allah yabarki da oga." " Bari naje inda aji karfe 2 sai nadawo tafa
a tana barin gidan.

Ni wallahi umma kidinga alama idan zakiyi kashi akan wane dalili zaki dinga kashi awando gaki da nauyi ke jidda Asiya tafada tana fadin wallahi Nagaji sai dai ki gyara dan ni ba baiwarku bace ba haba fitsari anan kashe ma hakama fa jiya ina bata abinci dai amai kuma ajikina." Harararta jidda tayi tace " Ai nayi aikina naga da safe wallahi ke zakiyi." Anty Amarya dake jiyosu tace " Menene hakan kukeyi saboda rashin tarbiya?

Ba mahaifiyarku bace ba idan bakuyi mata ba wazaiyi mata kamar naku?

Bakwaso rayuwarku tayi albarka ?

Duk lallacewar uwa uwace kuma wallahi sai Allah yayi fushi daku ahakan zaku samu naku masu tausayi ko abunda kukeyi zakujo dadi idan yaranku keyi muku shi?

Narasa gane
anku kwana biyu aikin ladafa kukeyi ko dankunga abba baya gari to sai na sanar dashi ta waya, Ai yanzu yakamaceku ace kun tausayamata kun dubata bawai ku tsya haka ba kuna ganin dai Alhaji mutallab Abba ya lallabasa yafito da Jamil daga gidan yari gashi can asubuti shima yana fama da jinya yakukeso tayi saboda Allah?

Ita kuwa kome tazama girmamata akeyi sai kuyi hanzarin gyara gurin Nan kunji yan albarka ke Jidda bakincemun zakije gidan afrah ba." " To ai babu mai kaini Anty." " Ki shirya kije akwai driver gidan yayanki sai ya kaiki ai kema yakamata kicigaba da makarantar idan ya dawo kisameshi ki lallabasa kinji." " Allah dai yabiya yaya mutallab gaskiya munyi dacen
an uwa wallahi." Jidda tafada tana nufar gurin zata gyara nan asiya tace " A'a bari nagyara ke jiki taya anty Aiki.
Chapter 24 · 0% Book details