← Book details Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 36

Sashe 20

Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tabbas yau ta yarda jahilci na
awainiya da ita kuma Allah ya shiryeta ya ganar da ita, tayi maganar cikin zuciya kafin azahiri tace, "Kayi addu'a Allah ya bamu masu albarka m
ri, duk da ance haihuwa da wahala amma zan jure ko nawa kake so na baka." "Da gaske kikeyi A
cha." "Me zai hana tunda kana so kuma nima..." Sai ta kasa
arasawa tayi
asa da kanta, wata irin runguma taji ya kai mata yana sanya mata albarka sai kace ma tasamu cikin har ta haifar masa, murmushi ta saki tana sauke ajiyar zuciya kafin tayi
arin zare jikinta ha
e da cewa, "Ka taso ga abincin can na ha
a maka." Tami
e tare da ri
o hannunsa zuwa palourn tana danne
aci ran da take ji nasa a zuciyarta suka nufi wajen dining, sai data zuba masa yaci ya
oshi sannan ya kalleta ha
e da cewa, "I'm sorry A
cha da duk abubuwan dana tayi maki adalilinta, sai
aga baya na gano ashe sharri ne da makirci takeyi maki amma idanuwana suka rufe nakasa gane haka saboda yadda na
wallafa gina akan
an cikinta, sai gashi duka ban tsira ba sai data hanashi takowa duniya." "Ba komai haka Allah ya tsaro." Tafa
a tana
afarsa cin abincinta da takeyi.
*************
Buki ne na manya da
awatuwa akeyi a babban ball
in da hamsha
an masu ku
i kawai ne da suka amsa sunansu ke iya kama wajen da kuma manya-manyan
an siyasa da
usoshin gwamnati masu fa
a aji, duk inda ka duba jami'an tsaro ne tako ina suna faman mazurai dan ba ango da amarya kariya daga farmaki da aka ta
a kaiwa na sace Afrah, wanda ba dan dangin ango da suka matsa dayin program
in ba da babu wani shagali da za'a gudanar inji amarya Afrah dan ba
aramar tsorata tayi ba alokacin da aka dauketa, dan ma Allah yasa babu abinda akayi mata kuma ana bata ci da sha mai kyau acikin wuni biyu da kwana
aya da tayi awajensu.

Sosai ango da amarya sukayi kyau
an uwa da abokanan arzi
i sai tayasu murna akeyi ha
e da yimasu liki, musamman dangin ango da suka bu
e bakin aljihunsa cike da farincikin auren suna zubar da ku
i tare da kwasar rawa.

Ba'a watse bukin ba sai misalin
arfe goma da wasu mintuna ango da masu bashi kariya suka yowa Afrah rakkiya har gida, murmushi Afrah tayi lokacin da suka iso tare da kallon angon nata tace, "Sai da safe hubby, ka kula mani da kanka fiye da yadda kuka bani kulawa kai da jami'an tsaron ka." "Zanyi hakan har lokacin da kika dawo hannuna kulawar ta dawo hannunki dan ramawa kura aniyarsa." Lumshe idanuwa tayi tare da bu
esu akansa tace, "Ba kada matsala Allah ya kaimu lokacin".

Tana kai hannunta a jikin mabu
in motar sannan ta bu
e tafita, sanyayyar ajiyar zuciya Farouk ya sauke bayan gama
are mata kallon da yayi har tafita, ya zaiyi idan ya rasa Afrah dan wata irin soyayyarta yake ji mai tsanani na
ara shigar masa a zuciya da sam baya don abinda zai rabashida ita ko kuma ya ta
ata, wannan dalilin yasa ya
auki alwashin duk wanda keda sa hannu wajen
auke ta da akayi sai ya bincikosa ya kuma hukuntasa akan haka, saboda adalilin hakan ne duk wani tsimi da tanadin da sukayima wannan bukin nasu suka soke shi, wanda yana da tabbacin ba haka
in Afrah taso ba kawai ta tsorata ne shiyasa ta zabi daga program
in yau babu wani abu da zatmsu sakeyi sai
aura aure kawai ta tare
akinsa.

Yana wannan tunanin ne yaga ashe tuni sun fice daga gidan sun kama hanyar zuwa gida, alokacin ya tuna kuma da al
awarin da yayi na cewa zai bada miliyan
aya ga duk wanda yakawo labarin inda za'a samu Afrah, wannan yasa ya ciro wayarsa ya kira Aryan dake tare da Mahmoud daya zo bikin Afrah a palournsa suna cin abinci, sai da suka gaisa bayan ya
aga kafin yace, "Aryan ka turo mani account number dinka na turo maka ku
in da nayi al
awarin bayarwa ga duk wanda yakawo mana labarin inda za'a samu Afrah.

" "A'a ranka ya da
e, ai Afrah
anwata ce, banyi
an kabani komai ba tundaa wajen MAM ma aka samu duka baya nan " "No al
awari mukayi kuma ya zama dole mu cika, saboda haka ka turo mani da ita." "Shikenan ranka ya da
e godiya nakeyi bari nakira MAM ya tayani godiya." "No need don Allah Aryan ai anzama
aya." Farouk yafa
a yana kashe wayars." Shiru Aryan yai kafin ya kamo lambar Mutallab ya sanar dashi yana
arawa da cewa, "MAM da Farouk yabar ku
insa tunda cikin hidima yake kada ya takura." "Ba wani takura Aryan kawai katura masa tunda al
awari yai, amma kai kuma ka sa
a al
awarin mu tunda nace kada kafa
awa kowa." "Kayi mun afuwa kaina kasan dole na fa
a masa saboda alokacin shika
ai ne muke dashi da keda karfin tado
ansanda ba tare da ansamu wata matsala ba, kuma kaga ai alhamdulillah kwalliya ta biya kudin sabulu an amsota kuma ku
inka sun dawo." "Haka ne kuma, Nagode sosai daka kasance mai tsaya mani acikin lamurran akoda yaushe." "Commooon MAM, what a friend's means." Da haka suka ajiye wayar Aryan ya tafa account lamba
insa ya turawa Farouk." Dariya Mahmoud dake gefe sa yai ha
e da cewa, "Gaskiya gayen nan ya
wareka Aryan, ai dole ya baka ku
i tunda yai maka
wacen Afrah kana ji kana gani." Murmushi Aryan ya saki yana ajiye wayar agefensa ha
e da cewa, "Ba wani
wace haka Allah ya tsaro Mahmoud cewa tun can ba nine mijinta ba kuma itama ba matata bace, ko da muka rabu da Afrah akwai girmamawa tsakaninta dani shiyasa har yau nima nakeyi mata kallon
ara." "Haka ne." Mahmoud yafa
a yana dariya tare da bashi hannu suka tafe..
***************
Zaune take agaban Dady si faman kuka takeyi ya zuba mata idanuwa, dan shi yanzu gaba
aya al-amarinta yadena bashi mamaki tsoro yake bashi, shiyasa tun jiya da suka zo da ita gida bayan ansallamosu daga asibitin Jabir yai masu kwatance da aka kwantar da ita suka je magana bata ha
ashi da ita ba, ko washe gari da yazo gaisheshi bai yanka mata ba haka ma da zai fita tayi masa Allah ya kiyaye ko kallonta beyi ba sai yanzu daya dawo daga wajen Mutallab da a wannan karon da kanshi yaje ya sameshi jin lamarin har da saki yayi mashi bayanin duk kalar zaman da yakeyi da ita da cin kashin da takeyi masa.

Jiki a sanyaye ya baro wajensa cikin wata irin matsananciyar jin kunyar abinda
ar tasa tayi, shine ya bu
aci ganinta Mommy na zaune gefe ita kuma
asa tana kukan munafurci jin daga wajen Mutallab yake cike da tsammanin zai goya mata baya a wannan karon ma, yafi mintuna ashirin yana kallonta ya kasa cewa komai yana tallafe da fuskarsa sai can ya nisa yace, "Kin kyauta Meenal da suka abubuwan da kika yiwa mijinki da
an uwansa, ban ta
a jin kunya irinta yau ba da mijinki ya zauna yana zayyane mani mugayen halayenki, ban ta
a nadamar baki gata ba da sangartaki ba sai yau Meenal, tabbas kin cika
ar halak da kika sanya ni girbar abinda na shuka na hana baiwar Allah nan ta baki irin tarbiyar data dace ga duk wata
a mace da zata taimaka mata wajen zaman gidan aurenta." Ya
are zancen yana kallon Mommy jikinsa a sanyaye yaci gaba da cewa, "Ashe aikin da kike
arin sata tun tana
arama dan takoyi girki da iya tsaftace muhallinta gata ce kike yimata amma nake kallon haka a matsayin takura?

Ashe fa
a da kike yimata nata gyara kanta soyayya ce nake yimaki kallon bakya sonta?

Ashe hukuncin da kikeyi mata idan tayi makinmagana cikin rashin
a'a shine dai-dai da zai sakata ladabtuwa wajen iya tauna kalamai yayin magana amma nake kallon mugunta kike yimata?

Kai co!

Da nasan wannan rana zata zo da ban hanaki duka haka ba Hajiya Mariya, da akwai yadda zanyi na maida hannun agogo baya wallahi da nayi saboda na tayaki tarbiyar yarinyar nan tare da hukuntata, sai dai kash!
Chapter 20 · 0% Book details