← Book details Moon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 68

Sashe 7

Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zameta yayi daga jikinsa ya nufi cikin bathroom wanda yake cikin ƙaramin ɗakin da yake, tsayawa yayi yana kallon bathroom gaba ɗaya kansa ya ɗaure bai san mene zai mata ba wanda zai sanya taji sauƙin ciwon da take ji a yanzu,bai saba ba haka nan bai san ta ina zai fara ba.
Tunanin haɗa ruwan zafi ne yazo masa kai,a zafafe kamar yadda yake tafiya a ko yaushe ya ƙarasa gaban jakuzzie ya faɗa mata warm water,cikin sauri ya juya ya nufi cikin bedroom ba tare da wani abu ba,yana zuwa yasa hannu ya ɗauke cak ya nufi cikin bathroom ɗin da Ita,sam bai damu daya zafin ruwan yake ba,burinsa bai huce yaji ta daina masa ihu a ka ba,yana daka tsayen ya cilla ta cikin ruwan, ƙara ta saki mai ƙarfi gaske ga yanayin buguwar da kanta yayi ga kuma zafin ruwan daya ratsa ta wanda ta keji tamkar naman jikinta zai kwakkwaɓo sabida zafin ruwan.
Da sauri ta yun ƙura zata miƙe ya sanya tafin ƙafarsa ya dannata cikin ruwan,a'a dole ta koma taci gaba da kukan a zama,ganin ta zauna ya juya da sauri yabar cikin bathroom ɗin.
Yana fita ya faÉ—a saman bed da rufda ciki.

Ajjiyar zcya Moon ta shiga saukewa,a hankali kuma zafin ruwan ya fara ratsa mata cikin jikinta Zuwa ƙashin ta ta naman ɓargwanta,wajan 20minutes jinin jikinta daya daskare sanadiyar zaman parlour'n da tayi sanyi ya gama ratsa ta fara sinkewa.
SICKLE
ciwo ne mai haɗarin gaske,wasu da susan ciwo wasu kuma basu san shi ba,ciwo ne da yake a cikin jinin mutum,ciwon na tashi a sanadiyar wata ƴar ƙaramar ƙwaya daza tazo tsakiyar jijiya ta tsaya,hakan zai sanya jinin mutum ya daskare yaki tafiya ya cure waje guda,jinin nayin hakan ciwo zai tashi,wasu lokacin kuma jinin ke lanƙwashewa yay kamar lauje,idan kace Zaka ɗaga wannan laujen zai iya karewa idan kuma kace Zaka bassa a wajan zai iya sanyawa naman wajan tsatsa har takai ga wajan ya kumbura ya fara ruwa.
To aduk sanda ciwon ya mutsa sai dai a dinga ruwan zafi ana shafa man zafi tare da shan magani irinsu ibuprofen diclofenac sodium da sauransu, wasu lokotan kuma ana injection ne a yayinda maganin yaƙi aiki a jiki.
Ciwon sickle babu inda baya kamawa ƙafa, hannu,baya,ciki,ƙirji,kai, haƙori da sauran,wani lokacin ƙafa ko hannun mutum na iya karyewa haka kurum ba tare da wani ciwo ko rauni ba.
Da yawan lokota ba'a gane ciwon sickle a jikin ƙana nan yara,wasu lokacin sai anyi gwajin jini na genotype a nan za'a fahimci wanne kalan jini gareka AA,AS,O, SS, SS shine cikakken sickle,AS kuma kamar aƙwai amma bamai ƙarfi ba,da blood group a nan kuma shine B+ da sauransu.

MOON gonotype É—inta ya kasance SS cikakkiyar sickle gareta,yayinda blood group É—inta ya kasance B+ (nayi maku bayanin hakanne dan ku fahimci ciwon dake damun Moon).

Deen na ƙwance har akai kira na biyu,da ƙyar ya mike a ɗan zafafe ya fice daga cikin bedroom ɗin cikin parlour ya nufa yana zuwa ya nufa wani part kai tsaye bathroom ya shiga ya zare kayan jikinsa tare da sakarwa kansa shower,wata iska mai zafi ya fesar daga cikin bakinsa kafin a hankali yasa hannu ya hargitsa gashin dake ƙwance saman fuskarsa sbd ruwan daya jiƙasa,yana gamawa ya ɗauki bathrobe ya sanya a jikinsa,kana ya ɗaura alwala tare dayin brush,a ɗan gurguje cikin tafiyarsa ta hanzari yabar cikin part ɗin,wata farar T.shirt ya sanya tare da wani dark blue ɗin crazy jeans, parlour'n ya koma ya ɗauki ladduma ya tada salla,bayan ya idar ba tare da wata addu'a ba ya miƙe ya nufi bedroom ɗin Ovasi knowking yayi,wajan 20seconds Ovasi ya buɗe ƙofar da sauri ya zube ƙasa yace "nyene? (ina kwana?)" Kallonsa kawai Deen ya ɗauke kai sbd baka safai ya yin magana da yaran nasu ba,sai ya zame masa dole, sai da yaje tsakiyan parlour'n sannan ya tsaya tare da zura hannayensa cikin aljihun wandonsa wajan 30 seconds ya fesar da iska yace "jeka tada mota" ya na faɗin hakan ya nufi cikin bathroom ɗin.
Yana daga tsayen ya ɗauko pack ɗin cigarette a aljihunsa da laighter ya kunna ya yay mata duguwar zuƙa yana lumshe idanunsa,sai da ya sha mai yawa sannan yaje ya ɗauki wata sweet ya cilla bakinsa tare da fesa parfume,yana tsaye yaji ana knowking ƙofar murya can ƙasa da kuma ɗan sauri yace "come in" Ovasi ne ya shigo yace "oga na gama" nuni yay masa da wasu akwati da sauri Ovasi ya ɗauka ya nufi waje, mayan idanunsa ya juya a cikin bedroom ɗin kamar me neman wani abu, ribbon ɗin ya ɗauka ya ɗaure gashi ƙansa kafin ya ɗauki wata ficap yasa a kan,kai tsaye ya fice daga cikin ɗakin.
Sai da yaje compound zai shiga mota ovasi ya kallesa yace "oga ina yarinyar" tsaki taja cikin ransa yace "damn it" da ɗan gudu ya koma ciki ya fara duba saman bed amma babu ita can yaji numfashinta a cikin bathroom, taɓe baki yay sbd shi shaf ya manta da babun ta, shiga yayi ya ganta ƙwance cikin ruwan da ya gama yin sanyi,kallon yadda gashin kanta ya sha ruwa yay ƙwance a gefen fuskarta da kuma bayanta,kallon fararan kayan jikinta yay wanda sukai datti domin kusan ƙwana 2 sune a jikinta, ƙara sawa yay ya ɗauke ta ya juya da sauri-sauri yabar wajan,back seat ya zauna itama ya ƙwantar da ita,ganin yadda jikinta ke rawa alamar sanyi ta keji ya sanya ya zare t.shirt ɗin jikinsa,kana ya ɗaga ta ya zuge zip ɗin ƴar duguwar rigar jikinta,shafaffan brest ɗinta ya tsurawa Idanu kafin yaja idanunsa ya rufe,can zcyarsa mamaki abin yake bashi yanzu wata rana ita zasu raina harta zama cikakkiyar mace mai taƙama da kyawun halittar ta,a sanyaye ya sanya ƙaramin ya tsanta zuwa kan nipple ɗinta ya shafa,saurin cije lips ɗinsa yayi sbd wani murmushi dake shirin ƙwace masa,yana saka mata rigar sa ya zameta daga jikinsa ya hankaɗe ta can gefe, reverse yay da motar kana yaja ta gudu yabar wajan kai tsaye suka nufi airport ɗin dake kusa dasu.

Suna zuwa airport aka basu ticket É—insu, MOON Deen da Ovasi,suna shiga babu jimawa jirgin ya É—aga zuwa Abuja,30 minutes ya kaisu Nnamdi Azikiwe International Airport (IATA: ABV, ICAO: DNAA) is an international airport serving Abuja, in the Federal Capital Territory of Nigeria. It is the main airport serving the Nigerian capital city and was named after Nigeria's first President, Nnamdi Azikiwe. The airport is approximately 20 km (12 mi) west of Abuja, and has an international and a domestic terminal that share its single runway.

Suna zuwa ya amshi wata blue ɗin sweater ya saka, kafin ya karɓi wata ash ya sanya Moon wacce take ƙwace dai raba fararan idanunta take kana ganinta kasan she is in serious sick, parking sukai Deen agogon hannunsa ya duba yaga 10:20 ɗan tsaki yaja sbd ya tsani a ɓata masa lokaci, yana daga cikin motar ya hangi wata farar budurwa mai ɗan tsayi da kuma jiki,gefenta wata matashiyar mata ce da wani magidanci, Nana khadii ta kalli mahaifiyarta tace "Inna duk wata zanna dawowa fa,ki ƙwantar da hankali albashi na farko dashi za'ai maki aikin ƙafarki, kin san har yanzu ƙarfen yana jikinki kuma nuna muna buƙatar kuɗi masu yawwa" magidanci dake gefenta yace "muna maki fatan alkairi Hadiza,ki tsare mutuncinki domin shine darajar ki,ki zama mai biyayya ga iyayen gidanki, Allah ya tsare ya kare" Nana tace "Ameen Baffa" Inna tace "to gashi har yanzu shuru ko?" Nana zatai magana taji anyi sallama tsaye ta kansa Ovasi yace " "Nwawonin (Sannun ku" Nana tai murmushi tace "Nwawo (sannu)" da mamaki ya kalleta sbd sam Babu kamanin ibira a tare da ita,yace "yawwa idan kin shirya zamu tafi,Mama Abba sannunku" gaba ɗaya suka amsa da "yawwa" tare da bashi amanar Nana khadii a hannunsa domin duk tunaninsu shine ya sama mata aikin, sallama sukai ya ɗauki akwatin Nana ita kuma tabi iyayenta ta rungome,har bakin airplane ɗin ya kaita sannan ya bata ticket ɗinta.
A cikin jirgin ta ga Deen da Moon zau ne a wajan guda,sai Ovasi a gefe da hannu Ovasi yay mata nuni data zauna, sanarwar akai kowa ya sanya belet Deen ya saka wayoyinsa a airplane mood kana ya juya kaÉ—an zai sanya belet yaji Moon ta ware hannayensa tare da shigewa cikin jikinsa jikinta duk rawa yake sbd tsananin sanyin da take ji,da blue eyes balls É—insa ya kalleta Kafin da sauri yakai hannunsa zuwa ga...

_Ma sha Allah ina gdy da comments ɗin ku sosai,amma kusani a duk inda mutum yake ina buƙatar comments ɗinsa da kuma share, Littafin nan FREE BOOK ne so dole ko kyautata min🤗domin abin zaifi armashi,kuyi share kuyi share kuyi share ina buƙatar ku turasa dukkan grps ɗin da kuke, WATTPAD, WHATSAPP, FACEBOOK, TELEGRAM KUYI COMMENTS DAN ALLAH👏🏻👏🏻 Wattpad kuyi vote kuyi following_

👯🏻‍♀️👯🏻‍♀️YANZU AKA FARA

COMMENTS
SHARE
VOTE
08119237616

SARAUTA👑
9/12/21, 5:33 PM - Buhainat😝: I just published "11-12" of my story "MOON (human Trafficking)". https://www.wattpad.com/1088156761?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=nimcyluv&wp_originator=g%2ByfJg8JAAG%2FVFDDEu8HcCIHCzUVIsN3bAKdkdq8YymoNRpsPzPt6PFCPW6eRNwPYocWl6SJRO%2FFc177KTwOtInYUIZMRKTEA%2B%2B1rbltMPBt3Es3213q%2F%2BLu8PTECIHt

_⚡MOON⚡_

_✍� NIMCYLUV_
11-12

ELEGANT ONLINE WTITERS

Belet ɗin dake maƙale da jikin kujerar ta,ya zameta yay a jikinsa kana ya ɗaura mata belet ɗin,kallonsa kawai take tana ɗan lumshe idanunta wanda sukai kumbura sbd kukan da tayi jiya,lafewa Deen yay jikin kujerarsa tare dajan idanunsa ya lumshe,a hankali baturiyar cikin jirgin ta fara faɗa kowa ya shirya jirgi zai tashi,Nana dake kusa ta Ovasi ta kalli Deen wanda ko inda take bai kalla ba, kuma tana da tabbacin shine ya bata offer ta aikin,a haka jirgin ya fara shawagi a ƙasa kafin a hankali ya fara yin sama-sama har cikin gajimare Moon dake zaune tana rarraba idanu tayi saurin ƙanƙame jikinta sbd karkarwar ba jirgin yay a hankali jirgin ya ɓace cikin gajimare.
Chapter 7 · 0% Book details