← Book details Moon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 68

Sashe 58

Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina dada jadda cewa yanayin abin ci da da abin sha da sanyi ko yanayin zafi suna tasiri matuka, dukkan abinda ba'a fahimta ba dangane da yana yin zuwan jinni ko daukewarsa yarinyace ko babba to kamata ya yi ayi tambaya cikin gaggawa lura da yadda muka yi bayan da cewa yanada alaka da hukunce hukunce, kina yin jinkiri sai salloli su kubuce miki, kuma wannan yana nuna cewa mace da aka saka zata iya kammala idda akasa da watanni uku. Idan yarinya ta ga jinin kuma jinin ya zama shine zuwansa na farko sannan ya tabbata cewa jinin al'adane to ta sani ta balaga, dukkanin hukunce-hukuncen musulunci sun hau kanta, idan ta yi salatin Annabi za'a rubuta bata lada idan kuma ta bari samari suna jagwalgwalata ita za'a rubutawa zunubi, ba wanda yace wai sai ta yi aure sannan za'a fara yi mata rubutu, kenan har azumi sai ta ranka wanda ta sha.

Tabbatuwar Jinin Al'ada: Shifa abinda ya shafi jinin al'ada al'amari da Allah madaukain sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai girma, Allah yana cewa: Kuma suna tambayarka dangane da al'ada, Kace: Shidinnan cutane, ku ninci (saduwa da) mata a lokacin al'ada, kada ku kusance su har sai sun yi tsarki (Jinin ya dauke) idan suka tsarkaka (suka yi wanka) to ku je musu ta inda Allah ya umarceku, Lalle Allah yana son masu yawan tuba kuma yana son masu tsarkaka. Bakara, ayata: 222. Haka kuma ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yace; (Wannan) Wani abune da Allah ya dorawa mata 'ya'yan Adam. Ashe ba shaci-fadin da ake cewa bane ai sanadiyyar da yasa mata suke al'ada shine wannan ganyan bishiyar da Nana Hawwa'u ta ci a gidan aljanna, amma Annabi Adam mala'ikane ya rike masa makoshi (makogaro) sai ya amayar da abin shi yasa maza basa yi. Wannan labarin bashi da kanshin gaskiya domin ayoyin Alkur'ani sun tabbatar da Annabi Adam ya ci itaciyar. Shifa jinin al'ada kada amanta jinine da yake fitowa daga can cikin mahaifa a lokuta sanannu, Allah madaukakin Sarki ya haliccishi domin ya zama abin ci ga yaro a lokacin da yake cikin mahaifiyarsa domin inda zai yi tarayya da mahaifiiyar ta shi a abincin da take ci to da karfinta ya ragu sosai, sa Allah ya sanya shi ya zama abinci ga reshi, shi yasa dakyar kaga mace tanada juna biyu (ciki) kuma tana al'ada. Idan kuma ta haihu sai Allah ya zamar da shi nono jaririn yana sha amatsayin abin ci, shi yasa kadan ake samun matan da suke shayarwa kuma suna al'ada. Idan ya zamana mace bata da juna biyu (ciki) kuma bata shayarwa sai ya kasance ba inda zaii je to shine sai ya taru a mahaifarta, shine mafi yawancin lokuta yake fita a kowanne wata cikin kwanuka shida ko bakwai, ya kan karu ko ya ragu akan hakan kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah- gwargadon yadda Allah ya tsara halittarsa.

STORY CONTINUES BELOW

wannan yadda jinin al'ada yake kwarara kenan daga jikin wata baturiya

Karkasuwar Mata: Mawallafin littafin Akhadari ya kasa mata zuwa kashi uku dangane da jinin al'ada, kashi na farko; itace wacce ta fara, kashi na biyu kuma; wacce ta saba, sannan sai kashi na uku; mai juna-biyu (wato mai ciki), ga bayanansu kamar haka:

É—igon Jinin al'ada

1. Wacce Ta Fara: Ita wacce ta fara al'ada ya zama yinta na yanzu shi ne ganin al'adarta na farko a rayuwarta, to abinda dake kanta zata zuba idone ta ga kwanaki nawa zauka kafin ya yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha-biyarba, idan ko ya wuce sha-biyar to abinda ya doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al'adaba, kenan mafi yawan kwanakin da zata saurara sune kwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewa kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama (Isthala) cuta sai a nemi magani, anan nake cewa iyaye su kara sa ido akan 'ya'yayansu mata su dungu tuntubarsu suna fahimtar da su tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci ya yi yarinya ta ga jini ta fashe da kuka, ko makamantan haka, wata babbar macece amma bata san menene jinin al'adaba ita dai kawai tace tana ganin jini a wani lokaci bayan wasu kwanaki kuma sai ta daina ganinshi.

2. Wacce Ta Saba: Abinda ake nufi da wacce ta saba itace wacce ta gabatar da al'ada sau uku a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi al'adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai ya yi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shima kwanaki biyar, to wannan sai muce sunanta wacce ta saba domin ta saba akan kwanaki sanannu. Amma idan ta yi al'adar karo na farko kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar karo na uku kwanaki shida to ba za'a kira wannan wacce ta saba ba, domin ba ta da tsayayyun kwanaki.[5] Ita wacce ta saba wato wacce take da sanannun kwanakin al'ada to wadannan kwanakin sune kwanakin al'adarta, idan kwanakin suka cika al'adar kuma ta dauke sai ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada, amma idan kwanakin suka cika al'adar kuma bata daukeba sai ta kara kwanaki uku, haka zata dinga kara kwanaki uku har kwanaki shabiyar su cika, misali idan al'adarta kwanaki biyarne sai kuma jinin bai daukeba a kwanaki biyar din sai ta kara kwanaki uku na sauraron daukewar sun zama takwas kenan, idan ya dauke shikenan sai wanka, idan kuma bai dauke ba sai ta kara uku akan wadancan takwasdin sun zama sha-daya idan bai daukeba sai ta kara uku sun zama sha hudu idan bai daukeba sai ta kara kwana daaya, ya zama goma sha-biyar kenan, sai ta yi wankan kammala al'ada ko ya dauke ko bai daukeba domin kwanakin al'ada makurarsu shine kwana goma sha-biyar kuma sun cika, abinda ya ci gaba da zuwa ba sunan shi jinin al'ada ba sunanshi jinin cuta (Istihadha) sai a nemi magani.

Adukkan wadancan kare-karen kwanaki da aka yi inda ace bayan ta kara kwana uku na saurare sai ya dauke a kwana na daya cinkin hukun shikenen sai ta yi wankan tsarki. Mu sani kamar yadda bayani ya gabata shi jinin al'ada bai wuce kwanaki goma sha- biyar ga wacce ta fara da wacce ta saba.

3. Mai Juna-biyu (Mai ciki): Galibin mata masu juna biyu basa al'ada, sabo da haka da zarar mace tana da juna biyu (ciki) sai kuma ta ga al'ada to kada ta yi sakaci wurin tuntubar likita . Idan al'ada ta zowa mace mai junabiyu to idan cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zata iya yin al'ada ta kwanaki sha-biyar zuwa ashirin, idan kuma cikin ya kai watanni shida to al'adar zata iya daukar kwanaki ashirin zuwa ashirin da biyar, kada a sha'afa wurin tuntubar likita idan ana da juna biyu kuma aka ga jini. Tanbihi Na Daya: Idan mace jini yana mata wasa wato ya zo yau gobe sai kuma ya dauke bayan kwanaki uku sai kuma ya dawo to abinda zata yi anan shine, ta tsaya ta yi karatun ta natsu, sai ta lissafa kwanakin da jinin ya zo sune kwanakin al'ada sai kuma ta ware kwanakin da jinin bai zoba sune kwanakin tsarki domin da hakane zata cika kwanakinta na al'ada, misali kwanaki tara; sai ya zo a rana ta farko da ta biyu sai bai zoba a rana ta uku da ta hudu sai ya zo rana ta biyar amma bai zo ba a ta shida da ta bakwai sai ya zo a ta takwas da ta tara. To anan sai muce ta yi al'adar kwana biyar a cikin kwanaki goma, wannan matar ita ake kira (Al-Mulaffiqa) alarabcin mata masu al'ada. Idan ya zama an sami tazarar kwanaki takwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsa da dawowarsa to na biyun zai zama sabon jinine kenan, ba na dane ya dawaoba. Alamar Daukewar Jinin Al'ada: idan jinin al'ada ya dauke akwai alama da shara'a ta sanya domin ya zama shine manuniya akan cewar al'adarki ta dauke, wadannan alamu sun kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin kantane, sune kamar haka:

STORY CONTINUES BELOW

ï¿?
1. Bushewar Gaba: Abinda ake nufi anan shine mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin gabanta ta fito da shi busasshe ba wani jini a tare da shi, to da zarar ta ga haka to ta tabbata al'adarta ta dauke.

2. Farar Kumfa: wannan wani ruwane fari mai laushi da yake zuwa karshan al'ada, idan mace ta ga irin haka a karshan al'adarta to ta sani ta kammala. Wadannan alamomi su suke nuna daukewar al'adar mace, idan mace bata taba ganin al'adaba sai a wannan karon sai ta fara ganin bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki ba sai ta jira farar kumfaba, amma idan wacce ta saba ganice sai ta ga bushewar gaba to malamai sukace zata zata dan saurara kadan domin jirar faran kumfa, amma jinkirin ba zai kai ga fitar zababban lokacin sallah ba. A dunkule dai kowanne daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu yana nuna samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu alokaci gudaba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata sai ta yi wankan tsarki domin ta ci gaba da ibada, domin idan bata yi wankaba ko da jinin ya dauke mijinta ba zai sadu da itaba ba kuma zata yi sallaba, da dai sauransu. Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi ko diddiga-diddiga bayan daukewar jinin al'ada to kada ta damu ta ci gaba da harkokinta na ibada, dama matsalar idan ta ganshi a farkon jinine, amma idan a karshen jinine to wannan ba komai, Ummu Atiyyah medakin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) tace: ((Mun kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi- fatsi da diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani abune)). Abu Daud Hadisi Na: 307, Nasa'i, Hadisi Na: 368, Ibnu Majah Hadisi Na: 647, Darimi Hadisi Na: 865. Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar asuba, amma ba'ace ta tashi cikin dareba domin ta duba.
Chapter 58 · 0% Book details