← Book details Moon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 68

Sashe 46

Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ne yake naɗa masa rawani mai bala'in kyau wanda ya kasance mai dai-dai ci,bayan an kammala aka miƙa masa Sandar girma,can kuma aka ɗauko wata zabgegiyar takobi a cikin gidanta, Lokaci da za'a bashi Takobin sai da kowa na fadar ya miƙe tsaye har da Eneye Ahuoyza,cikin girmamawa aka bashi Takobin kansa a ƙasa yasa hannu ya karɓa yana karɓa ya shigar zagaye kansa da ita,sai kuma ya durƙosa har ƙasa tare da miƙa Takobin gaban goshinsa sai kuma ya dawo da ita wajan bakinta ya sumbata,a hankali ya miƙe tsaye tare da komawa wajan kujerar ya zauna, ɗaya bayan ɗaya Mutane suka dinga zuwa gabansa suna zubewa tare da kai masa gaisuwar ban girma, lumshe idanunsa yay sbd nauyin da yaji yana masa,ashe haka sarauta take? Haka take sawa Mutum yaji wata izza da girman kai na musamman,sai yaji bakinsa ya ƙara yi nasa nauyi fiye da ko yaushe, ɗan gyaran murya yay kaɗan tare Mutsa sandar hannunsa, Sarkin fada ne yace "Ma sha Allah kamar yadda kowa ya sani yanzu King Aliyou Eneye Ahuoyza shine sarki,kuma nan da wata uku cif za'ai bikin rantsar da shi kamar yadda akewa ko wanne sarki,muna gdy ga dukkan wanda yazo wannan taron sai kuma ALLAH ya nuna mana ranar da Za'ai bikin rantsar dashi tare bashi sandar girma na gold" daga nan zaman fada ya watse, Deen na ganin mutane sun ragu a fadar ya miƙe da sauri kamar zai tashi sama,da sauri shima Eneye ya miƙe yabi bayan Deen, kai tsaye flat ɗinsa ya shige ya shiga fatali da alƙyabbar jikinsa ya shaddar kawai ya bari,bai tsaya ɗaukan komai ba sai A.t.m ɗinsa da abubuwa masu amfani a garesa, kayansa yasa a trolly sannan ya fito Wata Jakadiya sai kirari take masa,a haka ya nufi babban parlour,a tsaye ya samu Nene da Eneye murmushi Besty yay yace "kana tunanin zan habaka hanaka zuwa wajan matar ka ne?tun ka amshi buƙatata zaka iya zuwa duk inda kakeso but make sure ka dawo before 3mouths" jinjina kai Deen yay sai kuma ya nufi wajan iyayen nasa a hankali ya rungomesa yana basu peak,suma peak sukai masa Nene tace "Allah ya ƙarawa Sarki lfy" Fuska ya kwaɓe ya kalli Besty a marai-raice yace "Abba ka ganta ko??" Dry yay yace "rabu da ita ƴar adawa ce Allah ya tsare ya kiyaye, Allah yasa matar kada tayi fushi dakai"shi dai bai ce komai ba ya kama hanya zuwa harabar Masarautar,nan ya samu fadawa tsaye suna jiransa,samun kansa yay da tafiya a hankali amma ba can ba Sannan kuma bai hana fadawan binsa ba,kansa a ƙasa har zuwa wajan motarsa kai tsaye back seat ya shiga sai kuma driver yaja motar suka nufi Airport.Moon ce tare da Amira suna tafe a hankali domin zuwa wajan football ɗin su kasancewar yau Sunday shine ranar da suke game, Amira ce tace "Moon ke a tunaninki mene yasa ya kashe maki wayar??" Shiru Moon sbd kukan daya tawo mata,tsaki Amira tayi tace "uhm Allah ya kyauta,komai yay zafi maganinsa ALLAH!" Hawaye ne ya sakko daga cikin idanunta cikin ƙasa da Murya kamar zatai kuka tace "He far away for me Amira,wa nake dashi a duniya sama dashi? sai dai naga a zuwa ganin wasu Amma babu ni,he promised to me zai dawo but he broken his promised Amira,kina ganin Yaya Farouk duk sai yazo ban wani ƙalla halaƙa dashi ba amma baya gajiya da zuwa gare ni,why Dad zai manta dani?" Ta kai ƙarshen maganar tana sakin kuka,tsayawa sukai a wajan dake gaba ɗayan su sanye suke da kayan ball na Amira farare na Moon pink,wando da riga ne sai ƙaramin hijab,ƙafarsu sanye da combus da duguwar Safa mai kauri,gaba ɗaya wandon da ƙyar ya huce cinya,ganin sun tsaya yasa Faizak sakin murmushi a hankali ya ɗauke camerar wayarsa daga kan Moon kai tsaye yaywa Mai martaba sending na vedio'n Moon da yay mata, Juyawa Amira tayi sbd ƙarar camera da taji Maimakon taga Faizak sai idanunsa ya sauka akan Deen wanda yake jikin mota ya harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa,gashin kansa ya sauka har gefen fuskarsa yay bala'in kyau sbd saloon ɗin da akai masa,ya ƙara fari da ƙiba ga ƙirjinsa daya ƙara faɗi sosai ya zama wani Jibgege, bakin a Amira har rawa yake wajan faɗin "Moon look your Dad is here look at him" da sauri Moon ta juya nan idanunsa ya sauka akansa akaci Sa'a suka haɗa ido,bata san lokacin data saki dry ba sai kuma hawaye ya shiga sakko mata,da sauri ta yarda ball ɗin hannunta ta nufi inda Deen yake tsaye,shikam idanunsa a lumshe suke yana mmkin yadda a kullum ƙara girma take, ga wani shegen hijab data saka,har wani ball take salon a buɗa masa mata, Moon wani ihu tayi ta shiga faɗin "Dad!!Dad!!" Tana zuwa wajansa ta faɗa jikinsa tana sakin kuka.
Chapter 46 · 0% Book details