← Book details Moon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 68

Sashe 47

Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Tabbas idan banga comment ba Wlh Wlh ALLAH! Sai nayi sati banyi new update ba_
9/12/21, 5:42 PM - Buhainat😝: *MOON*
_✍�49-50_

Accept yourself the way you are be kind your self

Baya Deen yay sbd yadda Moon ta faɗa jikinsa,a hankali ya jingina jikinsa da jikin motarsa yana buɗe manyan idanunsa a kanta Muryarsa dake nuna yana farin ciki yace "Easy,Easy Dolly" baki ta tura gaba tace "Dad!!" Ware idanunsa yay alamar "what again Wify?" Girgiza masa kai tayi sai kuma tace "I Missed you like a crazy Dad" Kallonta kawai yay ya ɗauke kansa kana ya zare ta daga jikinsa, Amira ce ta ƙarasu wajan su tana kallon Moon tace "Morning sir" idanunsa na can wani gefe yana kallon wani abu yace "Uhm" Amira kuma ta kalli Moon tace "Let's go dear" maƙe ka faɗa tayi tare da girgiza kai alamar ba zata ba, Amira tace "but we have to win this game" kallon Deen tayi taga waya kawai yake dannawa leƙa fuskarsa tayi ta ƙasa suka haɗa ido,da sauri ya janye idanunsa yana lumshe idanunsa,bata kawo komai a ranta ba tace "Dad za kaga ball ɗin mu yau" haɗe rai yay sosai ba tare kuma da yay magana ya kama hannun Moon ya nufi office ɗin principal da ita,Amira Juyawa tayi zuwa wajan ball ɗin a ranta tana mamaki jijji da kan Deen tare da isa da kuma izzar sa,a bakin ƙofa Deen yaci karo da Principal shida Faizak kallo guda Deen yaywa faizak ya ɗauke kansa, shiru ne ya biyo bayan gaisuwar da sukai a junansu, Faizak kam tuni ya juya ya nufi Ɓangaren sa sbd yau weekend ne babu karatu a yau ma yake son komawa MASARAUTAR TANZAN, Principal ne yace "Ai jiya ta ɗaga hankalinta,ita gida zata ta gaji da zamar makarantar,na lallaɓa ta dai daga ƙarshe kuma ta fara kuka kamar wata yarinya wai ita Dad ɗinta haka dai,bayan ga wani duk weekend sai yazo mata tace min dai Yayanta ne, Finally dai Dad is here congratulations Maimunatou Aliyou Deen" da sauri Deen ya kalli Moon sbd ambatan sunan wani da Principal ɗin yay,ganin ko a jikinta sai ma hawayen shagwaɓa da take ƙara matsuwa yasa ya ɗauke kansa,A karan na farko Deen ya ɗan saki fuska muyarsa can ƙasa yace "Just look at her, she's crying like a baby" Dry Principal yay yace "Ai Aliyou ma sha Allah! Allah ya baka ƴar a nan kawai taɓara,ranar daka aurar da ita akwai kallo fa,domin ina jin kullum sai an maida ita gidan miji sbd guduwar da zata nayi" ɓoye fuskarta tayi a jikin Deen sbd kunyar daya kamata sosai, Deen kaman a zuciyarsa cewa yay "She's mine,komai nata is belong to me ni Aliyou Eneye Ahuoyza the king of Nufaz" a zahiri kuma kallon Principal ɗin kawai yay ba tare da yace komai ba,can kuma ya ɗan saci kallon Moon yace "Hope zaka ban aronta?" Buɗe ido Principal ɗin yay yace "Why not? Ai weekend ne wasu students ɗin har gida suke zuwa ranar Friday Sunday sa yamma su dawo" jinjina kai Deen yay Sannan ya kalli Moon yace "jeki sa veil" marai-raice fuska tayi tace "Dad ba zaka gudu ba?" Kai ya ɗaga mata da sauri tai waje da ido kawai ya bita, lumshe idanunsa yay tare da fesar da numfashi mai zafi, yaushe ƴar rainon tasa ta girma haka? Komai nata ya fito more than his expected her brest waist komai ya buɗe,ga fatar tai wani fresh sai Shinny take, kyanta ya ƙara bai yana, ga wani girman jiki na abun mmki, Tabbas duk wanda ya gansa shi da Moon za'a ɗauka da gaske shine ya haifeta sbd farar fatar su da yazo ɗaya,uwa uba ya bata tazarar shekaru masu yawan gaske,wanda da ace auren yay zai iya haifar kamarta. Moon na fita daga office ɗin ta nufi coner ɗinsu a hanya ta samu su Yasmin tun kafin ta ƙarasa wajan Yasmin tabar wajan,da alama dai barin makarantar zatai domin yau sukai Finally exam ɗinsu, gaba ɗaya ƴan mate ɗinsu sai kukan rabuwa ake Yasmin da Sumy kam na tsaye babu wanda ya tsaya inda suke sai tsohuwar headgril da kuma wasu yara na primary section, ɗauke kanta tayi har zuwa cikin room ɗinsu,Zai ne ta sami Feenerh ganin farin ciki a fuskar Moon yasa Feenerh faɗin "what again? Something new?" Murmushi Moon tayi tace "Guess what?" "Tayaya zan sani? Just tell me" Moon na ware babban veil ɗinta tace "Dad na yazo yanzu fa" buɗe ido Feenerh tayi tace "kai haba? Na tayaki murna kuka ya ƙare" Moon bata ƙara magana ba ta sanya veil tai waje cike da nutsuwa take tafiya,komanta abin sha'awa ne, ta ƙara girma da kyau sai medical glass ɗin ya ƙara mata kyau,a nan ta ƙara shigewa tabar su Yasmin wacce takewa Sumy sallama, tana cikin tafiya taji ance "Maimunatou!!" Juyawa tayi ta buɗe Manyan idanunta tace "Yaya" Murmushi yay mata kafin yace "Cutie ina zaki haka?" Kai tsaye tace "Dad na yazo" taɓe baki yay sai kuma yace "Ina son gaya maki wani abu,ban san yaya zaki fahimta ba,but this is the right time daya kamata ace kin sani,kada ya zamana ina aikin banza" shiru tai masa shi kuma ya ƙara matsawa inda take tsaye idanunsa a kanta yace "Bana sa zaɓin zaɓawa abinda zuciyata keso,ko kuma abinda yafi dacewa da ita,amma zuciyata nada zaɓin son wanda taga ya dace dani" shiru yay sai kuma ya kama hannunta yace "Ina sonki Maimunatou,ina sonki sosai Moon bansan a dadin son da zuciyata take maki ba,na kasa komai sbd soyayyarki ina cikin aiki zan barsa nazo nan dan kawai na ganki,naji sauƙi abinda na keji a raina,bawai dalilin ƙanwata da take a makarantar nan nake zuwa ba, a'a am coming just of you Maimunatou Aliyou Eneye Ahuoyza,bazan maki dole ba amma ina jin idan baki amince min Tabbas zan iya rasa raina,kuma na san ba zaki so kiga wani ya rasa ransa sbd ke ba,kina da hankali kina da tausayi nasan zaki zaɓi abinda zuciyarki take so" with much shock Moon take sauraran abinda Farouk yake faɗa mata,banda rawa babu abinda jikinta yake,baya ta farayi yana biyota yana faɗin "No please kada ki barni please Moon accept me as your lover" bata tsaya taji mai zai ce ba ta juya da sauri ta nufi office ɗin principal,Farouk kam idanunsa ne yay jaa kawai ya bita da ido ji yake kamar ya tsaga zuciyarsa ya fito da abinda ya keji game da ita,bazai taɓa give up ba har sai ya mallaketa, da sauri Moon ta shige Office ɗin sai kalle kalle take, Deen dake bakin window ya ɗan kalleta sai kuma ya ɗauke kansa, hanyar waje ya nufa da sauri tace "Dad" cikin tsawa yace "shut up you Mumu!!" Yana faɗin hakan ya fice daga cikin Office ɗin, Yasmin na zaune a cikin mota tana jiran Farouk ya shiga a kasalance Farouk ya fara ƙoƙarin buɗe motar daga bayansa yaji ance "Ohh hello" juyawa Farouk yay domin ganin ai maganar, ganin Deen tsaye yasa ya saki Murmushi tare da miƙa masa hannu,bai musu ba ya bashi hannunsa suka gaisa,shiru ne ya biyi baya kafin Deen yace "Am warning you stop away my Daughter" ware ido Farouk yay yace "ai akwai daughter naka a school ɗin? Ko bayan ka gama aikin gadin ka samu daughter more explanation pls I don't understand anything" wani mugun kallo Deen yay masa lokaci ɗaya yanayinsa ya fara sauyawa,amma duk da haka he's trying to control his self bai son abinda zai saka a fahimci wani abu tsakaninsu, Murmushi yay shima yace "Whatever,bana magana ɗaya na maimaita sai dai na ɗauki ma taki akai,Ni abu biyu Ni ruwa ne kuma ni huta ne,lolacin da ban damu da Mutum ba wlh ko inda yake bana raɓa,inuwar dabba tafi min sauƙin gani a kansa, Lokacin da Mutum ya shiga safgata sai fahimci a zaba wacce bai taɓa tunani ba" ware kafaɗa Farouk yay yace "Oh Wow! Lokaci na farko ka birgeni but please do me a favour,ina son ka bani auren ƴar taka" ba tare da yay aune yaji Deen ya sakar masa naushi a baki, kana ya shaƙe wuyan sa yace "you're mad FAROUK BASHIR YAHYA GIDAN KUƊI you're so selfish,i told you and i still told you stay away from my Daughter, Maimunatou is belong to not urs dai nai sharini wani da Maimunatou gwamma na kasheta uban kowa ya huta,wlh wlh billahi dalili ɗaya zai saka na barka a nan ba tare dana karya maka wata gaɓa ta jikinka ba,kai kasan wane Farouk idan baka sani ba very soon zaka sani Soon, Ma rantse da zatin Ubangiji uhmm,ka jawa kanka masifa tunda ka shiga inuwar da ba naka ba" yana faɗin haka yay cilli da Farouk jikin mota ya fesar da numfashi duk jikinsa rawa yake,da sauri principal da wasu securities suka ƙarasu wajan, Moon kam jin muryan Dad ɗin nata yana sauke ruwan bala'i yasa ta fito da sauri daga office ɗin zata wajan, Faizak dake tsaye yay saurin kama hannunta yace "wait ina zaki?" Bakinta na rawa tace "Dad na" fuskarsa a haɗe yace "to me zaki masa,ki bari ya gama ihun mana" wani kallon baka da hankali tai masa tace "wake ihun? Ko kai da nake kulaka darajarsa kaci sbd mun haɗa sunan uba ɗaya dakai" Principal yace "Lafiya? Meke faruwa Aliyou" tufar da yawo Deen yay yana nuna Farouk da yatsa sai kuma ya juya kai ya nufi inda yaga Moon tsaye,yana zuwa ya fisgi hannunta zuwa motarsa,da wani irin speed yay mata yabar cikin makarantar,shima Farouk idanunsa yay jajirrr sbd baƙin ciki yama rasa mai zaiwa Deen ya huce,yana ganin yanzu lokaci yayi da Moon zata san komai da haka Farouk ya bar makarantar, Faizak ma office ɗinsa ya nufa yana jin gaba ɗaya zaman makarantar ya fice masa a rai ga wani haushin Moon daya cikasa ace maza har biyu suna faɗa akanta? Mtwsss what the fuck? Kamar wata karya.
Chapter 47 · 0% Book details