← Book details Moon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 68

Sashe 12

Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Moon tun tana wasa da teddyn ta,har ta gaji da zama ta fara zirga-zirga a makeken ɗakin,gaba ɗaya zama ita kaɗai ɗin ya gundireta,a hankali ta fara kuka tana kiran sunan Dad,tun tana kuka har ta rasa bakin kukan sai ajjiyar zcya take saukewa a jajjere,sai da ta shafi 3hours ita ɗaya a ɗakin tana faman sauke ajjiyar zcy ta kiran sunan Dad,a haka bacci yay gaba da ita,abu kamar wasa Moon na ƙwance saman floor ita ɗaya taja teddynta ta rungome,duk da cewa bacci take amma hakan bai tana ta sauke wasu wahalallun ajjiyar zcya,a haka har akai kiran sallar fari, a hankali ta fara musawa kafin ta ware manyan idanunta ta shiga juyasu a ɗakin,da sauri kuma ta miƙe a tunaninta zata ganshi saman bed,a babu shi, tsayawa tai tana ƙara kallon bed ɗin,kafin ta zauna a gefe gadon,babu jimawa wani bacci ya ƙara ɗauke ta, 7 dai-dai ta ƙara musawa a wannan lokacin ta daina kukan sai yunwar dake damunta,wata hanya tabi tana zuwa taga wani haɗaɗɗan bathroom,komai na cikinsa pink color ne,wajan sink ta ƙarasa tare dayin alwala cike da nutsuwa,bakinta ta wanke da wani sabon brush data gani,kallon mirror ɗin bathroom ɗin tayi kafin buɗe jerarrun fararan haƙoranta, cikin siririyar murya tace "Mummy Mummy!" can kuma ta ƙara cewa "Yes my dear" tsayawa tayi kafin ta ɗura da faɗin "where are you?" Haka taci gaba da shirmanta tai magana as her mother kana tai magana matsayin kanta,a haka ta ɓata lokaci a bathroom ɗin, fitowa tayi zatai sallah sai dai babu abin sawa a kai, bedroom ɗin ta fara binkawa a haka harta kai ga wata ƙofa,tana buɗewa taga wani ƙawataccen parlour, ƙarasa fita tayi tana bin bango kamar muna fuka,a hankali kuma ta juya nan tai ido biyu da Deen wanda ya juya zuwa direction ɗinta sbd mutsin da yaji, yana zaune saman kujera jikinsa babu riga,an naɗe cikinsa da bandeji,Dry Damus yayi tare da ƙarasa juye wani abu a cikin glass cup ɗin,yace "weldone baby,kin hutarmu" Moon bata kalli Damus ta nufi inda Deen yake,tana zuwa tasa hannu ta ware hannayensa tare da shigewa cikin jikinsa,da sauri ya runtsa idanunsa sbd tsananin a zaba da zugin da cikinsa ke masa,amma ƙarfin irin na Deen ko mutsi bai yi ba,daga ƙarshe ma tashi yay da sauri haɗi da cilli da ita,ya nufi wani part, "ohh sorry baby" Damus ya faɗa yana zuwa wajanta yace "Dad ne?" Idanunta wanda suka kawo ruwa ta juya masa,kanta ya shafa yace "ok bari na kaiki,amma shanye tea ɗin nan yanzu" tea ɗin tabi da kallo,ita dai bata saba ganin tea haka ba, kasancewar ita yarinyar ce babu brain ɗin tunani mai ƙyau,yasa ta amshi cup ɗin da sauri kuma ta miƙa masa cup ɗin idanu na kawo ruwa tace "no thanks" haɗe fuska damusu yay kafin yace "ok yi zamanki nan Dad ya tafi ya barki" da sauri ta amshi glass cup ɗin tare da nufar bakinta dashi....

MOON... MOON... MOON
Am so sorry guys I'm not feeling well ne, Ku sanyani cikin addu'oinku🤲🏼🤲🏼👏🏻.

Gashi nan bani da lafiya haka nai maku,kun san dame zaku saka min basai nayi magana ba okey.

Share sbd Allah da Manzonsa👏🏻🤲🏼

SARAUTA👑
9/12/21, 5:34 PM - Buhainat😝: *⚡MOON�*

_✍� 17-18_
Elegant online writers

_Dukkan Zuciyar da take ambaton sunan Allah safe da rana babu wani rai da zai iya cutar da ita,haka kuma ya yinda mai sharri yake shirya makircinsa,haka ita kuma addu'a take rusashi,hakan na faruwa ne yayinda kaima baka nufi kowa da sharri ba, Allah ka cire mana son ZCY, da son abinda ba namu ba,da son abinda bazai amfane mu, Allah ka datar damu🥰🤲🏼_

Harta kai glass cup ɗin bakinta sai kuma ta tsaya tana ƙarewa cup ɗin kallo kamar mai nazartar wani abu,a hankali kuma ta ɗura cup ɗin abakin ta cikin nutsuwa ta fara shanye haɗaɗɗan tea ɗin wanda yasha suger,milk, bonvita,duk zafin shayin bai hanata shanye wa tass ta ajjiye cup ɗin tana kallon Damus a ɗan tsorace ,dry yay kana ya amshi cup ɗin yace
"Good beauty, kinyi aiki mai ƙyau"
Da ido kawai take kallonsa harya fice daga cikin ɗakin,yana fita Deen ya fito tare da neman kujera 3seater ya zauna akai, Moon tsayawa tayi tana kallon sa sbd yadda lokacin ɗaya ya sauya daga yadda ake ɗazo zuwa yanzu, idanunsa sunyi jajir sun janye kamar mai jin bacci, jijiyoyin kansa suyi raɗa raɗa a saman goshinsa,jikinsa banda ɓari babu abinda yake,sai fesar da wata zazzafar iska ta cikin bakinsa yake,ganin yasa Moon ta fashe da kuka still idanunta na kan Deen, runtsa idanunsa yayi sbd har tsakiyar kansa ya kejin kukan nata, ganin bata da alamar yin shuru shi kuma bai wani abu lallashi ba,yasa yaja tsaki tare da miƙa mata hannunsa alamar tazo garesa,abinda take jira kenan tana ganin hakan ta nufi wajansa ta gudu tana zuwa ta haye saman kujerar tare da shigewa jikinsa ta rirriƙesa, yatsansa ya ɗura saman lips ɗinta a hankali cikin iriyar murya yace
"Shiiiiiit...!"
Shuru tayi ta fara sakin ajjiyar zcya akai-akai kamar wacce ta shekara tana kuka,shuru shima yayi yana sauraran bugun zcyarsa da kuma yadda take sauke ajjiyar zcya mai ƙarfi,mutsi gudu yay sai ta ƙara ƙanƙamesa,Damus na fita ya nufi wani special side kai tsaye ya danna telephone line dake sama,wata maid ce ta ɗaga tana ɗagawa yace "haɗa ni da Eki"
Jikinta na rawa tace "okey sir"
Da sauri ta kiran line É—in side É—in su Eki babu jimawa aka É—aga kiran tayi Sa'a kuma Eki ce tayi picking call É—in, haÉ—e kiran tayi waje guda kana ta shaidawa oga Damus Eki tana kan line, Eki tace
"Good morning Sir"
Daga can ɓangaren yace mata
"Mrng,ina yarinyar nan kaya sun kammalu aiki yana wajanki"
Fari tayi da idanunta kafin tace "Sir daman umarnin ka ake jira,yanzu za'ai komai a gama"
Damus yace "okey good,kizo ki amsa yanzu,alrdy na gama da yarinyar"
Eki tayi dariya tace
"Baka da ƙyau sir"
Tana faɗin hakan ta ajjiye kan wayar ta shige bedroom ɗin data fito,zaune ta samu Nana tana gyara gashin kanta,tana sanye cikin wata duguwar riga,mai ƙirar buba amma duk da faɗin rigar hakan bai sanya jikinta ya ɓoye ba, bayan ta gama ƙare mata kallo tace
"My dear bari a kawo maki breakfast,naga acan baki sakewa tare damu"sosai hakan yaywa Nana daɗi domin a cikinsu jinta take a takure bata iya sakewa taci abincin yadda ya kamata, murmushi saman leɓe tai mata tace "ok! Thank you"
Juyawa Eki tayi a hanya suka ci karo da Salmerh haɗe rai tayi kafin taka waje ta tsaya tace "da wasa naga kin shiga part ɗina wajan NANCY saina haɗaki da oga,kin san punishment ɗinki dai wallahi yanzu za'a haɗaki da ƙarti biyar" ita dai Salmerh bata tanka ta ba tayi shigewarta aiken da granny tayi mata.

Yana zaune Moon na jikinsa baice mata ci kanki ba har bacci ya ɗauke ta,ganin hakan yasa ya miƙa tare da ajjiye ta a kan sofar ya nufi cikin wani bedroom,duk yadda yakai daya samu nutsuwa a wannan lokacin kasawa yay sbd zuciyarsa da yaji tana zalzalashi zuwa ga abinda bai yi niyyar sa ba a yanzu,gaba ɗaya tunaninsa ya goshe wani duhu yake gani a cikin idanunsa,dole zaibi abinda zuciyarsa take kwaɗaita masa,da gudun daya gama zama jinin jikinsa ya ƙarasa shiga cikin bathroom ɗin dake cikin bedroom ɗin part ɗinsa,wanda aka ware masa daban a cikin gidan,yana shiga ya zare kayan jikinsa ya sakarwa kansa shower,a zafafe yake wanka da ruwa mai sanyi duk da irin sanyin da ake busawa a ƙasar,yana kammalawa ya juna handrayer ya budar da kwantaccen gashin kansa,kafin yay brush ya fito,kansa ya tsorawa idanu da jikin makeken madubin dake maƙale a dressing mirror,gaba ɗaya Deen yabi ya birkita kansa kamar kumurcin zaki,bai wani damu da shafa mai a jikinsa ba,ya ɗauki body spray ya fesa a saman fresh skin ɗinsa,wajan wardrobe ya nufa ya ɗauki wani blue black ɗin crazy jeans ya saka tare da riga armless,bayan ya gama ya ɗauki facecap ya sanya saman sumar kansa,kai tsaye ya ƙarasa wajan trolly ɗin sa ya ɗauki ticket daya yanka tare da wayoyinsa Wada wasu muhimman bayanai,yana gamawa ya fice daga cikin bedroom, tsayawa yay yana kallon harya ɗaga ƙafa zai ƙarasu inda take sai kuma ya juya da gudu yabar part ɗin,bai tsaya ko ina ba sai harabar gidan,wata ash ɗin mota ya shiga drever yaja da sauri ya nufi airport dashi.

Nana na zaune Eki ta shigo hannunta riƙe da babban tray, ƙaramin table ta janyo gaban Nana ta ajjiye tray ɗin akai,tace mata "Bisimillah ga breakfast"
Nana ta kalli tray É—in kana ta kalli Eki tace "Moon fa?"
Waje Eki ta samu ta zauna tace "manta da ita,nan rayuwar Æ´an ake"
Da mamaki Nana tace "kamarya na manta da ita? Ƙaramar wacce gaba ɗaya bata ƙarasa 11yrs ba ita zatai rayuwar ƴanci a nan ɗin,ko bana da labarin a nan mahaifiyarta take ne?"
Eki tana latsa wayarta tace "kusan haka,kema ba kawoki akai ba?so tana wajan da yazo da ita"
Shuru Nana tayi badan bata da tambayoyin da zatai ba,sai dan ranta ya fara ɓaci, miƙewa tayi zata fita da sauri Eki tace "breakfast ɗin naki fa?" Ba tare data kalleta ba tace "Allhamdulillah"shangabatan tayi tace "kee wasa nake maki fa, Moon bacci take yanzu tunda ɗazo aka shiryata tai breakfast shine take bacci yanzu" ɓoyayyiyar ajjiyar zcya ta sauke,kafin ta koma ta zauna, warmers ta fara buɗewa kusan duk abin ciki basuyi mata ba,hakan tasa kawai ta fara haɗa tea ɗin da aka ajjiye mata,bawai wani son shayi take ba amma a wannan karan yafi tasha da wannan tarkacan da aka ajjiye mata,a cup ta shaɗa shayin ta fara sha.
Chapter 12 · 0% Book details