← Book details Moon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 68

Sashe 44

Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Ke hakan na nufin babu wata halitta data isa ta cutar dakai a yayinda kayi Wannan addu'ar,koda ta cutar dakai bawai wayonsu ya sanya hakan ta faru ba,haƙiƙa Ubangiji yay mana gata da yayomu a musulmai kuma masu riƙo da addininsu, Uwa ba kuma yadda da ƙaddara,koda su Yasmin sunyi min wani abu ni nasan cewa hakan wata sabuwar ƙaddara ce data bijiromin,kuma ance ƙaddara lokaci gareta wani lokacin sai dai ka bata labarin abinda ya shuɗe,dan kuma ka shiga cikin wata masifar hakan ba yana nufin wai ƙarshen rayuwarka ne yazo ba, a'a nan ma wani lessons Ubangiji yake nuna maka mai hankali ance shike gane ɗin gishin ƙwaɗo,to thank God! Ni Maimunatou idan har addu'a na zama gari ya to tabbas ta zama gari ya gareni domin babu abinda su Sumy suka isa suyi min" gaba ɗaya suka kalleta can kuma Amira tace "Amma wacce damuwar ke hanaki cik abincin?ina lura dake sam baki son cik abinci" murmushi kawai Moon tayi idanunta cike da hawaye tace "wata damuwa tana zama dole kayi ta,domin baka san lokacin da take faɗa maka ba,ji nake kamar zan yi rashi ina jin kamar Dad na bazai dawo gareni ba". Da mmki Feenerh tace "kmaryay?" Ka faɗa ta ɗaga masu ba tare kuma da tace masu wani abu ba,ganin time na tafiya yasa suka miƙe gaba ɗaya su kowa ya shige class ɗinsa,a last prioud ɗin su Ass-headgril ta kalli Moon tace "Teacher Faizak yana kira a office nasa" juyawa fararan idanunta Moon tayi kamar ba zata ce wani abu ba sai kuma tace "kuma at this time?" Girgiza kai tayi tace "no yace after class" ɗauke kai Moon tayi tare da gyara farin glass ɗinta,suna gama class ta nufi office ɗinsa ta rataya school bag ɗinta,a zaune ta samesa yana operating system ɗinsa shiru tayi masa shi kam duk abinda take yana kallonta ta cikin system ɗinsa,kamar daga sama taji muryarsa yana faɗin "you look like familiar Maimunatou!!" shiru tai masa tana kallon fuskarsa amma a zahiri tunaninta yana ga Dad ɗinta,can taji yace "Yeah! Kina kama da Mai martaba sosai,ban san me yasa ba,ko ni ɗaya nake ganin kamar ohhhu! Amma duk wanda yasan Mai martaba kuma ya ganki dole zai ga kamar" da ƙyar ta buɗe bakinta tace "Ohhh! ALLAH! sarki" miƙewa yay tare da nufar inda take a gabanta yaja ya tsaya, lumshe idanunsa yay yace "su waye samarin jiya??" Idanunta wanda yake ƙara jan hankalinsa ta juya masa kafin tace "samari kuma?"kai ya ɗaga mata yace "Uhm" shiru tai masa ganin hakan yasa yace "da farko kin tsaya da wani har ya riƙe ki,na biyu kuma wani ya ɗauke ya fita dake daga cikin makaranta" sarai ta gane mai yake nufi sai kawai tace "Ohhh! He's my father" taɓe bakinsa yay still looking in to her eyes yace "Tab, babu kama abin" da rashin fahimta ta kallesa tace "Kamarya?" Ka faɗa ya ɗaga mata yace "nothing" kafin yace "what about your family?" Kai tsaye tace "shi ne ko mai nawa ai, family, friends siblings anything" da sauri yace mata "Out" kamar jira take yana faɗin hakan ta fice,shi kuma saman sofa ya faɗa yana jin zuciyarsa nayi masa zafi,yabar baƙin ciki a can gida,tunda ya kalli Moon yaji soyayyyar ta kamashi amma ya fahimci abubuwa da yawa a tare da ita,me zai mata? Dole ne ya nemi mafita dole ya jawota jikinsa, Moon a coner su ta haɗu da Sumy da Yasmin sun sanya wata yarinya a tsakiya sai shafata suke, Sumy na ganin Moon ta saki yarinyar ta nufi inda Moon take tsaye, harɗe hannayenta tayi tana jiran zuwa Sumy,da farin ciki a fuskar Sumy ta ware mata hannayenta alamar ta isa gareta,wata uwar harara Moon ta watsawa Sumy dry Sumy tayi tace "Yasmin zoki riƙe min ita" da sauri Yasmin ta nufin wajan Moon kafin ta ƙarasa Moon ta saka wata gigitacciyyar ƙara da gudu ta nufi inda Yasmin take tana zuwa ta jata ta haɗa kanta da bango,wata gigitacciyyar ƙara Yasmin tayi sbd zafin daya ratsa ta,nan take kuma kanta ya fashe ganin hakan yasa Sumy tayi waje da gudu domin neman ɗauki,Moon na ihu Yasmin na ihu haka Moon ta danne Yasmin sai duka take.

Kuyi share É—insa please fisabilillahi
9/12/21, 5:42 PM - Buhainat😝: *MOON*
_✍�47-48_
Chapter 44 · 0% Book details