← Book details Moon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 68

Sashe 41

Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ƴar mace tun sun bai yana sai raguwar girman,fesar da iska yay a hankali kuma ya zameta daga jikinsa ya kalli principal ɗin kamar bazai magana ba sai kuma yace "okey! Dama akwai su?" Girgiza kai principal ɗin yayi yace "ko kusa ko alama bata taɓa yi ba sai yanzu"taɓe baki yay bai ƙara kallon principal ɗin ba ya nufi wajan wardrobe ɗinta shi kuma Principe ɗin yay waje abinsa,wasu fararan kaya ya ɗaukar mata masu kyau riga da wando,gefen gadon ya zauna tare da jawota jikinsa ya zare mata rigar jikinta yana jin yadda ta sauke ajjiyar zuciya duk abinda yake idanunsa a lumshe suke bai yarda ya buɗe ba,sai da ya sanya mata kayan kana ya ɗauke na jikinta ya ajjiye can gefe guda,tsaye ya yi a kanta yana kallonta ko ƙifta ido ba ya yi, agogon warist ɗin sa ya duba yaga time yaja ko Isshā baiyi ba, durƙosawa yay ya shiga yi mata karatu idanunsa akan fuskarta sai faman haɗe rai take tana turo baki gaba, tattausan tafin hannunsa yasa ya shafa mata addu'ar,hasken ɗakin ya kashe ya ƙaro gudun ac sosai Sannan yaja masu ƙofar ya fita. Washegari da safe ya kasance weekend Moon basu da class tun safe data farka take ta mmkin yadda kayan bacci yaje jikinta, zuciyarta cike da tsoron Allah yasa Dad ɗinta ba tafiya ya kuma yi ba,bayan tayi sallah tai wanka ta ƙara komawa bacci, Feenerh kuma tana shirya wa ta nufi wajan Amira domin tayi mata kitso,can cikin baccinta taji ana ja mata hanci slowly ta fara buɗe idanunta tana rufewa a haka harta samu damar buɗe idanunta sosai a saman fuskarsa,waro ido waje tayi mmki,yana sanya da wani tissue ɗin boyal black wanda akaiwa ɗinkin riga half body mai ƙaramin hannu,ya ɗura wata half ɗin jaddara mai shegen kyau,sumar kansa ta sauka har wuyansa yay wani bala'in kyau tunda take bata taɓa ganinsa a shigar manyan kaya ba sai yau,hatta ga ta kalmin ƙafarsa jaaa ne shima half covert shoe mai gashi,ga wani watch ɗin iphone dake maƙale a hannunsa, idanunsa ya ɗauke a kanta yana faɗin "stop staring at me" turo baki tayi tace "Dad you look like Akbar na film ɗin Joda & Akbar" shiru yay mata ita kuma taci gaba da faɗin "Dad Allah kuna masifar kama sosai" taɓe baki yay yana miƙewa tsaye can kuma yace "ke kika san shi" sakkowa tayi ta kama hannunsa tace "Dad zaka tafi dani ko?nifa na gaji da Wannan makarantar" waro manyan idanunsa yay waje idanunsa a ƙofa kamar da ita yake maganar yace "Au! Lawyern fa?" Hawaye na ya fara sakko mata tace "to stay with me please Dad" Tofa anzu waje,shi yama rasa me zai farayi ga message ɗin Besty saya samesa jiya da yake cewa _Besty i missed you soo much,Nasan kana fushi dani ne but Aliyou ni nasan nai maka gata ne,ina son idan harni na haifeka ba riƙon ka aka bani ba,ba tsintar ka nayi ba to kazo gobe bai ɗauke maka ba, your father *~ENEYE AHUOYZA~*_ Abu na gama message ɗin da Damus yay masa inda yake faɗin. _Oga Deen kayi good 2years amma babu wani impormation about the girls,Oga Taju yace yana buƙatar yin meeting dake a Zoom tomorrow by 12pm zaku tattauna akan ɓatan yarinyar Moon dan kai yake zargi,dan haka ka tanadi hujjarka idan har baka dashi yana iya sanyawa azo tunda daga PAKISTAN zuwa Niger ai cire masa kanka kasan wannan ƙaramin aikin Taju ne, babban kuma zai iya ɗaureka a hankali ya dinga yankan nama jikinka, zan tura baka sa code na meeting ɗin tare da link_ Ga kuma rabuwa da Moon da zai yi yanzu,dole ya sassauta fuskarsa ya tattaro duk abinda ya iya ya bata nishaɗi kafin ya tafi, ajjiyar zuciya ya sauke kafin yace "Lolly ƴan mata sai Aure" ƙafa ta fara diddorewa tana sakin kuka "Dad ni bazan aure babu kyau fa" buɗe ido waje yay yace "laaa injiwa??" Turo baki tayi tace "kawai nidai,bayan ance wasu basu riƙe Aure da daraja, inaji Amira tana faɗin sister ɗinta ko good 3mounth ba tayi da Aure ba mijin ya saketa,wai baya bata abinci sannan baya sauke mata haƙƙinta" fito da idanu waje yay sosai yace "meye haƙƙi" shiru tayi kamar bai tunani sai kuma tace "nima ban sani ba" haɗe rai yay sosai kana yace "look at me Dolly,bana son kina zama kina jin wannan zantukan kinji ko, kuma ko wanne zai maki wani wakan kici masa uwa, bance rashin kunya ba a'a babu kyau rashin kunya gana gaba,ki zama kamala da nutsuwa,ki zama mai hqr da jajircewa,ki zama mai ra'ayin kanki kuma kaifi ɗaya,kada ki yadda wani yace zai sauya maki ra'ayi,ki zama tsare mutuncinta gida da waje, And ki rage wannan surutun naki" ya faɗi maganar yana sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya ya daɗe bai magana bai tsayin wannan ba,kana ya ɗura da faɗin "ko hannu mace ta bari wani ƙaton ya riƙe mata to ciki take ta haihu,wata ma ta mutu"da sauri ta zaro ido tana dafe ƙirjinta dry taso bashi dake bata damesa ba ya haɗiye abarsa yace "Eh! Sosai fa,dan haka ki kama kanki ki riƙe al'ƙawari dukkan wanda ya saɓa al'ƙawari bayan ya ɗauka to shi da Allah!,akwai hijab ɗin dana sauyae maki na makaranta kada ki ƙara sanya wannan guntun hijib ɗin understood?"ya faɗa ya fito da ido waje,kaita gyaɗa masa sakin fuskarsa yay yace "I'm coming Lolly, please keep the promise kada ki saɓa"kuka ta saka masa da sauri ya lumshe idanunsa yace "I'll be back Dolly, tabbas zan dawo a ko wanne lokaci kisa wannan a ranki Dad ɗinki na tare dake" kuka tasa masa tare da maƙale sa,shiru yay yana bubbuga bayanta cikin nutsuwa Kuma ya fara rera mata waƙa;
Chapter 41 · 0% Book details