← Book details Moon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 68

Sashe 25

Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaro idanu waje Dr Sufyan yay,tayaya ƙyakkyawan saurayi mai aji da ilimi mai taƙama da dukiya ace za'a cire idanunsa a sawa ƙaramar yarinyar, kasa cewa komai Dr Sufyan yay har yanzu ya kasa yadda da maganar DEEN kamar yadda ya kasa ɗauke idanunsa daga kallonsa,shima DEEN Dr Sufyan yake kallo ganin bashi da niyar magana yace "what again..,idan ba zaka iya ba zan meni wani Dr ɗin yay mata" girgiza kai Dr Sufyan yay kafin yace "nop! ba haka ba,amma bai kamata ace ka salwantar da idanunka akan ƙaramar yarinya like Moon ba,zata iya zama makauniya ka kula da ita da kuma komai nata,amma ba zaka taɓa zama makaho ta kula da kai ba,baza ta iya kula da kai ,kamar yadda zaka dinga kula da ita ba,ya kama dai kayi tunani before ka yanke hukunci,i advice to you as yadda friend zai bawa friend ɗinsa shawara" jinjina kai Deen yay bai ƙara magana ba sai Juyawa da yay sai da yaje bakin ƙofa sannan yace "ka shirya operation ɗin mutum biyu" sosai mmki ya gama kashe Dr Sufyan gani yadda Deen ke son kashe rayuwarsa akan ƙaramar yarinya, Dr Sufyan ya saki Murmushi yace "baka faɗi sunan da za'a saka a file ɗinta ba?" Fesar da numfashi Deen yayi yana ƙara hargitsa gashin kansa kafin yasa teeth's ɗinsa ya datse lips ɗinsa dashi kana ya ware bakinsa yace "MAIMOON ALIYOU" yana faɗin hakan ya fice daga cikin room ɗin, ya daɗe tsaye a harabar wajan kafin ya kalli agogon hannunsa mai ƙirar iphone yaga 11:30,da sassarfa ya ƙarasa bakin room ɗin da aka ƙwantar da Moon yana shiga ya samu ta farka tana ƙwance sai kuka take, taƙi kula kowa sai hannu take miƙawa zata sosa idanunta amma ta kasa sosawar sbd hannunta da Nana ta riƙe, jingina yay a jikin ƙofar ya harɗe hannayen sa yana kallonta, idanunsa yaja ya rufe ya shiga sauke numfashi ajajjere, ƙarasawa cikin yay yana shiga Salmerh da Nana suka miƙe daga saman bed,zama yay bakin bed ɗin still idanunsa na kan Moon,ganin zata kai hannunta saman idanunta yay sauri riƙe hannunta tare da murza hannunta kaɗan,kuka tasa tace "please leave me, zafi yake min wayooo Dad kace su cire min" kallonta kawai yake kafin ya sauke tagwayen ajjiyar zuciya, ƙasa yay da muryarsa dai-dai kunnanta yace "ur Dad is here, stop cry" da sauri ta miƙe zaune ta shiga lalubansa, hannunta ta sauke a saman idanunsa da sauri y lumshe idanunsa gudan kada ta tsokane masa idon da ake shirin maidawa cikin nata,cikin kuka tace "Dad kana gani na?kana ganin abinda aka saka min ko? Dad me nai masu suka saka mun wannan abun?dan Allah su cire min ban so wlh banso,dan Allah a cire min nima na ganka"rungome ta yay sbd wani tausayinta da yaji,tunda yake bai taɓa jin tausayin wani irinta ba, yarinya ƙarama ƙaddara ta faɗa mata,ko babban mutum yaya ya keji da makanta bare ƙaramar yarinya,yasan ba zata jure ba sbd bata saba zama cikin duhu ba,ta saba ganin komai a zahirance,ta saba yiwa kanta komai,da ace a haka take tun asali abin bazai dameta haka ba,amma lokacin ɗaya abun ya sameta tabbas kafin ta jure rashin ganinta za'a sha wahala, ajjiyar zuciya ta dinga saukewa,kanta yaci gaba da shafawa,kanta ta ɗaga tare da shafa fuskarsa tace "Dad ta tsaneni ko?" Shiru yay mata dan bai fiye son surutu haka nan ba,amma ya fahimci tunda ta tsinci kanta a wannan lalurar shikenan ta fara surutai marasa ma'ana ta zama kamar wata parrot, Moon ta kwaɓe baki zata saki kuka yay sauri sanya mata yatsansa cikin bakinta yace "shiiit.."shiru tayi ta shiga tsotsar yatsarsa kamar ta samu sweet, lumshe idanunsa yay yana jin yadda take tsotsar yatsarsa kamar zata zugo jinin dake jikin yatsarsa, turo ƙofar akai Dr Sufyan ya shigo hannunsa riƙe da File yana zuwa ya ajjiye files ɗin ba tare kuma da yay magana ba ya shiga haɗa injection ɗin da zai mata daman jira yake tai breakfast sai yay mata,shima Deen ɗan ware idanunsa ya shigayi tsigar jikinsa ya shiga tashi,daurewa kawai yay sbd su Nana dake wajan,a hankali Dr Sufyan ya nufi wajan lap ɗinta ganin yana tattare rigar wajan yasa Deen ɗan haɗe rai ba tare kuma da yace komai ba,santaleliyyar cinyarta ce ta bai yana fara tassa sai baƙin gashi da yaywa farar fatarta ƙawanya sunkai ƙwance lufff, ɗauke idanunsa yay lokacin da Dr Sufyan ya gama janye rigar wajan ya maida Kallonsa zuwa kan fuskarta har bacci ya fara ɗauke ta,zare yatsarsa yay a hankali, kwaɓe fuska tayi tare da turo jajayen laɓɓanta wanda sukai jajirr kamar an shafa masu jambaki, slowry Dr Sufyan ya sanya kan injection ɗin saman fatarta wani ihu tasa tare da manna fuskarta saman faffaɗan ƙirjinsa bakinta ya samu damar sauka wajan nipple ɗinsa Kasancewar gaban rigar a buɗe yake,jin tsinin abu yasa ta haɗe teeths ɗinta ta sakar masa ciwo,runtsa idanunsa yay da ƙarfi sbd zafin ciwon da yaji ga kuma ihun da take bai san lokacin daya haɗata da jikinsa ba,ya marai-raice fuska kamar zai kuka sam bai son ganin injection ɗin,a haka Dr Sufyan ya gama yi mata injection ɗin, kuka ta sanya tana rirriƙesa tace "Dad ka gansa ko zai cire min bombom ɗina,bapiiii ban so" kanta ya shafa bai iya cewa komai ba sai "sorry" a haka har bacci ya ɗauke ta,zame ta yay a hankali ya ƙwantar da ita a saman gadon, tsura mata ido yayi ganin yadda take sauke ajjiyar zuciya a wahallace, Dr Sufyan ne ya kallesa yace "kuje waje zamu duba idanunta nida wasu sabbin likitoci da mukai,sannan ina sa magana da kai, Deen miƙewa yay yana lumshe idanunsa yana jin yadda nipple ɗinsa ke masa zafi sbd cizon da tai masa,ficewa yay hakama su Nana da Salmerh,yana fita ya nufi compound ɗin asibitin,kai tsaye wajan motarsa ya nufa yana zuwa ya shiga ya jata da wani irin speed bai tsaya ko ina ba sai airport, ticket ya yanka na jirgin yamma wanda zai tashi da ƙarfe biyar na yamma,yana zuwa ya yanki ticket bai koma asibitin bai sai ya zarce gida,yana zuwa ya nufi part ɗinsa a parlour'n sa ya samu Damus zaune shida Ovasi yana masa bayanin abinda ke faruwa,sosai Damus yaji baƙin cikin abun domin idan har Moon ta nakasa to tabbas sun samu naƙasu a cikin plan ɗin da suka shirya,domin duk matan da suke kawowa babu wacce ta kama Moon a ƙyau da kuma tsarin a hakanma tun tana ƙaramar ta, duk sanda ta zama adult ba'a san yadda zata koma ba,dan haka ya kira shugaban su take ƙasar Pakistan ya faɗa masa a abinsa yake faruwa,dake kusan a ƙashashe goma suke da ƙungiyar trafficking BANGLADESH, PAKISTAN, THAILAND, CHINA, INDIA, TAJUDDEEN shine shugaban duka a ƙasashen da ake trafficking ɗin kuma shine yake bada oder a kan komai,hatta Moon shi yaba da details ɗinta da photonan ta,da kuma bayanin inda za'a sameta,kuma ya naɗa Deen matsayin wanda zaije safararta,wannan dalilin Deen ya sanya ya tafi neman Moon ido rufe,haka kuma ya nemi gadi a gidan su FAROUK bayan ya samu gidansu Moon,ya shafe wata biyar ciff ko mai kamar Moon bai gani ba,idan ya gaji yakan kiran TAJUDDEEN ɗin,shi kuma zai tabbatar masa da Moon na cikin gidan ya ƙara jira,rana ta farko daya ganta shine ranar data fito siyan ice cream, kuma a ranar a kashe iyayenta,gaba ɗayansu babu wanda zai iya cewa da idanunsa ya taɓa ganin TAJUDDEEN sai dai muryarsa,amma sanadiyyar abinda ya samu Moon yace a haɗa masa meeting da Deen nan da 1week,shigesu Deen yay a parlour'n ko kallonsu bai ba,yana shiga ya faɗa cikin bathroom ya sakarwa kansa shower ko kayan jikinsa bai cire ba,sai da ruwan ya dakesa sosai kafin ya shiga zame kayan jikinsa,bayan yay wanka ya sanya kayan cikin warshing machine,kana ya ɗaura alwala, fitowa yay ya nufi wajan wardrobe wata black ɗin jallabiya ya ɗauka ya saka ba ƙaramin ƙyau taiwa farar fatarsa ba, gashinsa wanda ya jiƙe da ruwa ya sauka har ƙasan wuyansa,wasu kuma suka ƙwanta gaban goshinsa ya zama kamar wani balarabe ko bature ba lalle Lokaci ɗaya ka iya fahimtar da wanne yake kama ba, but sosai Deen yake handsome mai aji da ilimi both boko da Arabic,kai tsaye idan ka ganshi ba zaka taɓa cewa yasan wani abu a cikin ilimin addini ba,sai wanda yay masa mugun sanin nan,babu kuma wanda yaywa Deen mugun sani sai iyayensa, fitowa yay kansa a ƙasa a nan ya ƙara barin su Damus ya nufi masjid ɗin dake cikin gidan, bayan yay sallar zuhur ya dawo cikin part ɗin,samu yay maid ta gyara sa tsaf sai ƙamshi yake ko ina,zama yay saman duguwar kujera kana ya danna telephone ɗin side ɗin masu kitchen,suna ɗagawa ya basu oder,babu jimawa wata maid ta danna ƙarar rawar part ɗin Deen, buɗe mata yay kana ya koma ya zauna,a hankali ta dinga turawa ƙaramin daining ɗin abincin har sai ta shigo cikin parlour'n, durƙosa tayi tace "evening sir"bai kalleta ba sai ƙasa daya ƙarayi da kansa,na lurar wannan yana ɗaya daga cikin habit ɗin sa koda yaushe kan Deen a ƙasa yake,maid ɗin kam tsayawa tai tana kallonsa domin gani take kamar bashi bane,sai ware manyan idanunta take a kansa,tsaki yay sbd yana lura da kallan da take masa, Murya kamar ba tasa vay yace "out..you mumu" da sauri ta fita daga cikin parlour'n tana tafe tana ƙara juyawa tana kallonsa harta fice daga cikin parlour'n,lunch ɗin ya fara dubawa yaga Sinasir Recipe wanda aka haɗa da shinkafa fara ta tuwo,sai yeast sai backing powder,da suger da kanwa ungurnu da albasa, ɗaya warmer ɗin ya buɗe yaga rice and chicken breast, a plate ya zuba Sinasir ɗin ya fara ci kaɗan yaci ya cakalkala ya tashi,bayan 5minutes maid ɗin ta dawo sosai tai mmki ganin babu abinda yaji daman dai wahala kawai yake son sata kwashe komai tai ta gyara kana ta fice daga cikin parlour'n,bayan sallar Asr Damus ya shigo a zaune ya samu Deen hannunsa riƙe da gwangwanin Cork yana sha,yana zaune daga shi sai 3gauter wannan karan ko singlet ɗin da yake sawa babu, faffaɗan ƙirjinsa a buɗe sai gashi da yay ƙwance sai kyalli yake ga brest ɗinsa da suka bai
Chapter 25 · 0% Book details