← Book details Moon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 68

Sashe 14

Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zafafe Deen ke taka ƙafafunsa,yana tafe yana fesar da numfashi ta cikin bakinsa kansa a ƙasa koda wasa bai yadda ya ɗaga kansa ba, ƙara jan alƙyabbar jikinsa yay tare da covering jikinsa da ita,gaba ɗaya baison takura wannan abar takurasa take,banda a yanzu bai shirya karɓar faɗa ba da babu abinda zai sanya ya amshi wannan kayan wahalar ya sanya a jikinsa,bai so dukkan wani abu daya dangaci sarauta ya tsani gaba ɗaya calture nasu komai a takure yake yinsa,yana son ya kansa shi ɗaya he won't be alone, bai son hayaniya, ƙara sauri yay wajan tafiyarsa kamar zai tashi sama,yana zuwa bakin FADA yaja ya tsaya kamar mai jiran ai masa iso,yana nan tsaye wasu Fadawa ne wajan goma suka ƙarasu wajan Deen suna masa busa tare masa kirari, haɗe rai yayi kamar zai sanya kuka kana yaja ƙwafa ya shige cikin fadar,a zaune ya samu OHINOYI (sarki but his real name is ENEYE) Deen na shiga ya zube a gaban mahaifin nasa tare dayin flat ya ɗaga hannunsa sama,cikin ƙasa da murya yace "Nwawo Abba (Sannu Abba)"Murmushi OHINOYI ENEYE tare da kaɗa gashin hannunsa kafin ya shafa a saman kan Deen, numfashi yaja yace "Nemba Wabeeh lafeeyanni(yaya kunxo kafeeya?" Deen na daga ƙwancan yace "Allhamdulillah"
Hannu Ohinoyi yasa ya ɗaga ɗan nasa kafin a hankali ya bashi side hug yace "wlcm Besty" ɗan shagwaɓe fuska Deen yay kafin ya ɗan yi gyaran murya,hakan yasa Ohinoyi ya fahimci abinda Deen ke nufi,gyaran murya shima yay tare da ɗan kaɗa gashin hannunsa,gaba ɗaya mutanan da suke fadar Sarkin fada,waziri, chiroma,Tiraki,Sarkin busa da sauran jama'a suka bar fadar,suna fita Deen ya shige jikin mahaifinsa yana lumshe idanunsa shi kaɗai yasan kewan gida da kuma kewan jikin mahaifinsa da Mahaifiyarsa da yayi,no place like home komai na gida daban ne,duk da ya tsani tsarin palace ɗin nasu amma dole yana son gida musamman wajan iyayen nasa wanda shi kaɗai suka mallaka a matsayin ɗa, Murmushi Ohinoyi yay yana mai shafa bayan Deen wanda ya lafe jikinsa ba tare da yace komai ba,wajan 10minutes suna haka kafin Deen ya miƙe da sauri yana duba agogon warist ɗin hannunsa ba tare kuma da yace komai ya zubawa mahaifin nasa idanu,gane abinda yake nufi yasa Ohinoyi haɗe rai cikin ya ransu na Ibira yace "kada kace zaka tafiya" langwaɓar dakai gefe yana ɗan ya mutsa fuska yace "Please..Abba" zike da zallar izza wacce ta gama bin jikinsa ya miƙe tsaye hana sanye cikin wata dakakkiyar alƙyabba ta sarakai sai manyan murjani a wuyansa da hannayensa,da kuma saman hular kansa,hannunsa ɗaya riƙe da sandan azufar ɗayan kuma da farin gashi irin na doki,ba tare da yace komai ba ya riƙe hannun Deen suka fice daga fadar,ganin haka yasa fadawan Sarki (Ohinoyi)suka rufa masu baya wani kallo Deen ya watsa masu wanda yasa dole suka tsaya,a haka suka ƙarasa cikin gidan sarautar baka ganin kowa sai bayi duk inda suka bi zubewa ake ana gaidasu, Deen kam baƙin ciki kamar ya fasa ihu,ciki Muryar sarauta Sarki yace "wannan shine mulki,indai jinin sarauta na yawo jikin ɗana dole a duƙa masa a ko ina" ƙara ɓata fuska Deen yay still kuma bai ce komai ba,bar suka ƙarasa wani babban flat na musamman gruds kusan ashirin ne a bakin flat ɗin sun turare ƙofar,suna ganin sarki suka zube ƙasa tare da ɗaga hannayensu sama,a haka aka sanya remote babbar ƙofar glasses ɗin ta buɗe kai tsaye suka shige ciki,nan naga ashe flat ɗin babba ne yana da side manya wajan 5,domin har side ɗin Deen a ciki,na Sarki kuma a can ciki wanda daban yake,sai na Mumyyn Deen mai suna NENE yana ce mata Mumyy,sai kuma side ɗin granny ɗinsa ta wajan Uba,a main parlour na tsakiyar sides ɗin Deen ya tsaya kafin ya fara zarya cikin parlour'n sam bai iya tsaiwa haka nan ba,wata blet Sarki ya danna babu jimawa Osohinoyi(matar sarki mahaifiyar Deen) ta fito cikin takun taƙama da izza tana gama kuyangunta na take mata baya sai ƙyalƙyali take cikin alƙyabbar ta,ganin Deen yasa tai murmushi tare da ware idanunta kamar amarki take ganinsa,can kuma ta ware hannayenta,da zafin nama ya ƙarasa gareta yana zuwa ya shige jikinta yana sauke numfashi, shafa kansa tare tace "wlcm Besty" turo baki yay kafin ya ɗan ƙara rungome ta, Sarki ya gyara murya hakan tasa gaba ɗaya suka kallesa waje Nene ta samu ta zauna shi kuma Deen yana tsaye domin bai iya zaman, Sarki yace "hope ka shirya barin wannan aikin naka wanda ban san mene kake aikatawa ba,rashinka na damuna dan haka kasawa ranka bakai ba ƙara barin gidan sarauta" da sauri Deen ya juya ya kalli mahaifin nasa kafin yace "what...!?" Cike da izza Sarki yace "i mean my words,me ur mother ur grandmother all muna buƙatar ka,wa like to stay with you nothing else,dan haka na rantse maka babu inda zaka ƙara fita" nan da nan jikin Deen ya fara rawa idanunsa suka sauya sukai jajirr jijiyoyin kansa sukai raɗa raɗa,bakin har kumfar masifa yake,ya riga ya san mahaifin nasa akan soyayyar da yake masa tun yana yaro kuma idan ya rantse akan abu babu wanda ya isa ya janyesa,kusan duk zafin zcyar da yake da ita na mahaifinsa ya kwashe tasss,cikin zallar bala'i yace "what the fuck...! Me..?ni za'a tirke kamar wani yaron goye,ni bana da ƴan cine eyeeeee? Ko anfi son a ganni a ƙwance saman bed naci abinci nasha ruwa aban fruit ai gaiding ɗina,nayi nan that stupid people ɗin can what did you call them? Ahaaa bayi or kuyangi sona bina kamar wata ta mace, never I'm adult niba baby bane dole zan fita" ya ƙare maganar yana dafe kansa tare da hargitsa gashin kansa,tunda ya fara magana suke kallonsa domin su san ransa ya gama ɓaci,idan ran Deen ya ɓaci idanunsa rufewa suke ruff ya manta wake kusa dashi ko wake yiwa masifar, Murmushi Ohinoyi yay domin ya san za'ai hakan kuma ya shirya amsar fushin ɗan nasa,dukkan abinda zai na wani lokaci ne dan yasan weakness nasa,Duk masifar da zaiyi rabin nasa bazai taɓa ba shi yasa masifarsa bata damunsa,damursa ɗaya yadda Deen zai kasance da mata,dole aƙwai matsala bai son yaya zai taken care na mace ba, he doesn't know anything about mace musamman budurwa, Nene tace "we're so sorry Besty,all this akan ka ne kawai muna buƙatar ka wajanmu,wannan tafiya aiki yay yawa,rabunka da gida wajan 9mnths haba,Ni banma san wanne irin aiki bane,look ka nemi mace kayi aure dukkan abinda kake we're ready to give you,idanma baka da budurwa zamu zaɓa maka cikin family wannan ba damuwa bane,idan kuɗi kake buƙata za'a baka komai kakeso za'a baka amma wannan aikin forget about it please Besty" kasa ce masu komai yay sai ƙafa daya buga yace "damn it..,da nasan haka za'ai bazan dawo ba sai nai shekara 5 baku ganni" ya faɗi hakan yana hulli da alƙyabbar jikinsa tare dayin flat ɗinsa da gudu, tagumi Nene tayi tana jinjina ƙarfin zcyar yaron nata,tashi sarki yay ya ƙarasa wajanta ya zauna yana zuwa ta kwanto jikinsa tace "ya rabb,see him.. protect him" ta ƙare maganar cikin damuwa, Sarki ya ɗagota jikinsa yace "don't worry I'll handle it,duk abinda da zarar na haɗa ido dashi zai waek,ko yanzu daya gama masifarsa bai kalli cikin idona ba" kaita jinjina masa tana shafa beard ɗinsa, lumshe idanunsa yay tare da kamo lips ɗinta ya fara bata wata lafiyayyiyar subma, Granny2 ta fito daga side ɗinta tana dugara sandan Zinare tace "Ni Yayandi wacce masifar ce ta saukar mana a wannan masarautar Yau BAFFA?,kai Allah dai wadaran naka ya lalace,duk wanda yay silar katsan bacci ban yafe ba,babu ruwana wannan ai ɗaukan hakƙine,nidai wlh an shiga haƙƙina indai ba'a ne ya fiya ba, a'a wlh wannan mugunta ce kawai aka shirya min" da sauri Nene ta janye bakinta daga na mijin nata tana sauke numfashi,Sarki ne ya miƙe yace "A'a Yayindi ur grandson coming back earlier" shiru tayi kafin tace "Mene? Aliyu gadanga ya dawo?yau na shiga uku shikenan zaman lafiya yay ƙaura a gidan nan, a'a wlh gidan Tiraki zan koma kafin wannan masifaffan ɗan naku ya tafi, bazai kasheni da raina ba"dry Nene tayi tana jinjina lamarin Yayandi kamar ba jiya take masifar baya gida an zuba masa ido ko kuma yana zuwa ita sukewa baƙin cikin ganinsa ohhhu? Nene tace "ai kam dai ya dawo,kuma bai ƙara tafiya" tagumi Yayinda ta rafka tace "amma wlh Baffa baka ƙaunata sam wannan bazan tare bane,ina dalili zaka jawo Nana mana tashin hankali haka kurum ka san halin ɗan naka da baƙar zuciya" baice mata komai haka tana kumfar baki ta koma side ɗinta, Deen na shiga flat ɗinsa ya shiga wurgi da dukkan abinda ya gani,daga ƙarshe ya ɗauki pack ɗin cigarette a aljihunsa da laighter ya kunna ya fara bata huta,banda tafasa babu abinda zcyar Deen keyi da susan muhimmanci dake bawa aikinsa da kuma kuɗin da yake kawo masa da ba'a ce masa haka ba,
Washegari tun safe ya rufe falt ɗinsa yana jin maid suna knowking amma yay banza dasu ko abinci yaƙi fita yaci,hatta Sarki da yazo da kansa kin buɗe ƙofa,gashi yau yana kwana na uku amma ko fita baiyi ba,anci Sa'a yabar ƙofar a buɗe,yana zaune yana operating system yaji an turo ƙofar,bai ɗago ba ƙamshi parfume ɗin kawai ya shaida masa mai zuwan,zama Sarki a gefensa yace "look at me Besty" ya faɗi hakan yana shafa sunar kan Deen wacce take ƙwance kamar ta Larabawa, tagwayen ajjiyar zcya ya sauke kafin ya ɗaga kai ya kalli Abban nasa cikin Sa'a suka haɗa ido da sauri ya janye idanunsa yana mai faɗawa jikin Sarki....
Chapter 14 · 0% Book details