Sashe 29
Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
young,me zata tsare masa, Yarima ɗa nane,inaji ko ke da kika haifesa baza ki taɓa yi masa soyayyar da nake masa,shi kaɗai nake dashi shi kuma kaɗai na mallaka,ina supported ɗinsa akan komai na rayuwarsa,amma a wannan karan bana tare dashi kuma akan wannan mgnar tabbas zai iya ganin fushi na wanda bai taɓa ganinsa ba, bedside ma I'm not interested bana da ra'ayi akan wannan maganar,yaje duk yarinyar da yake so,Nufe,kanuri, Igala,e.t.c ya nema cikinsu ni kuma nai masa alƙawarin a yau basai gobe ba zan aura masa ita,kai daga yau ma ya daina fita ko ina zan sanya a tirkemin sa"yana faɗin haka ya saki ajjiyar zuciya tare da miƙewa ya nufi can cikin part ɗinsa,Nene kam kasa mutsi tayi ita dai harga Allah tana jin tausayin rayinyar amma bata masa sha'awar aurenta,abu kamar wasa yau ƙwanan Deen uku ciff a cikin place hankalinsa yay mugun tashi domin bai taɓa tunanin reshe zai iya zama mujiya,kullum cikin roƙan Abban nasa yake amma fafur yace sam bai yadda ga wannan yarin IZE babu irin sin babu irin son da ba tai masa yaƙi kulata, tashin hankali kenan, lokacin da Deen ya gama haɗa kayansa zai bar gidan kasawa yay bai kuma san dalili ba, yau yana zaune saman sofa daga shi sai 3gauter ya rame ya faɗa sosai amma farinsa na nan sosai,kallo guda dai zakai masa kasancewa yana cikin damuwa,sallamar da yaji yasa ya ɗago kai kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa tare da rufe idanunsa, ƙarasa shigowa cikin parlour'n tayi,wata budurwa ce aƙalla zatai shekara 30 ɗin nan,tana sanye da duguwar wacce ta matseta duk surar jikinta ana gani, jikinta na rawa ta zauna kusa dashi tare da shafa fuskarsa tace "baby wai wacce yarinya ya wacce ta nifi?duk kabi ka tashi hankalinka,ko wani ataimaka wanda kake tunanin ni bazan maka ba?wlh komai kakeso zan maka"shiru yay mata kamar ba dashi take magana ba,jin shirun yay yawa yasa tace "dawowata kenan daga Dubai Mami ta kira ni take gayamin abinda ke faruwa, hankalina ya tashi sosai duk yadda akai asiri tai maka nasan my man ni kaɗai ce a gabansa"still bai kulata,zamuwa tai ta zauna saman cinyarsa tare da shafa beard ɗinsa tace "i know your problem baby"ta faɗi hakan tana nufar bakinsa domin yi masa kiss,da sauri yasa hannu ya hankaɗeta,kafin ya zare belet jikinsa da niyar dukan ta kuma sai ya fasa ya cillar, Murmushi tai tace "what!? Da nufinka duka na zakai?"a hasale ya sanya hannunsa cikin sumarsa kansa wacce take a hargitse ya ƙara bajeta saman fuskarsa ya fara Safa da marwa cikin parlour yana fesar da numfashi, hannunsa ya dunƙule ya kai wa cenema ɗin parlour'n duka,duk girman ta da ƙwarinta amma sai ta fashe jikake tartsatsa tassss,da hannu ya shiga nuna Ize cikin wata murya yace "ke daman jaka ce bani da labari?ni zaki sawa tsatstsaman bakinki a nawa, over my death body wlh,banda wari da ƙazanta mene a bakinki?bari kiji ko zan mutu banyi aure ba wlh tallh nafi ƙarfin ni ALIYOU na aureki,bare har kiyi tunanin haɗa jiki dani,oyaa leave my room Ize Sharif Saleh"ganin yadda jikinsa ke vibration yasa ta miƙe da gudu tai waje,a babban parlour na tsakiyar sides ɗin ta samu Nene wacce suke ce mata Mami tana zuwa ta faɗa jikinta tare da rushewa da kuka,cikin kukan take faɗin "Mami wlh sunma baby asiri,na shiga uku yaya zanyi da soyayyarsa?"bayanta Mami ta shiga bubbugawa tare da faɗin "kada ki damu Hubby yace a yau za'a ɗaura maki aure dashi,yanzu haka suna can suna shiryawa a fada,dan haka tashi maza kije kiyi wanka ki shirya a wannan karan dukkan abinda zaki masa dole ya hqr tunda kina ƙarƙashin inuwarsa ne"wani sanyi Ize taji a zuciyarta tama rasa how happy she's,da sauri ta miƙe ta nufi part ɗin Mami,bayan sallar Asr, Ohinoyi ya shigo cikin side ɗin sanye Da Kaya na alfarma kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki,bai yadda ya shiga plat ɗinsa ba, Jakadiya yasa ta kira masa Deen,tana zuwa plat ɗin ta samesa ƙwance saman Italian carpet yana sauke numfashi hannunsa riƙe da saitin zcyarsa, rusunawa tai tace "Allah ya taimaki Magaji ya ƙara maka lafiya Ohinoyi yana kira"tana faɗin hakan ta fice da sauri,sai da ya shafe 10 minutes sannan ya miƙe yana layi haka ya fice daga plat ɗin nasa,a zazzaune ya samesu Abba,Mami, Yayinda,Tiraki,yana zuwa ya zauna chan nesa dasu tare da sunkuyar da kansa,gyaran murya Ohinoyi dan maganar da zai faɗa bazai iya jira sai wani ya faɗa ba,kallon Deen yay yace "ALIYOU" shiru Deen yay sai da Ohinoyi ya ƙara faɗin "Aliyou"sannan ya buɗe baki kamar mai kuyan magana yace "yes Abba"tunda Ohinoyi yaji Deen yace Abba yasan cewa ba ƙaramin fushi yake dasu ba, Murmushi yay yace "da farko nidai uba ne a gareka,ko yarda ko karka yarda i don't care,ina da ikon da zantar da hukunci a kanka,ka zagi ƴar Mutane akan kawai tace tana sonka,to albishirinka?a yau basai gobe ba an ɗaura auranku dakai da yarinyar,da sauri ya ɗaga kanka yana kallon Abban nasa,sai yau ya ƙara tabbatarwa baya tausayinsa,a rasa dawa za'a haɗa shi aure sai da tsohuwa,ƙwafa kawai yay yaci gaba da sauraran abinda Ohinoyi ke faɗa "wlh koda wasa naga ka ɓata ran yarinyar nan sai naka ran ya ɓaci tabbas,babu ruwana da kana sonta ko baka sonta tashi kaban waje stubborn friend kawai"babu musu Deen ya miƙe tsaye daga shi sai 3gauter da farar singlet ya nufi hanyar barin side ɗin gaba ɗaya,da sauri Nene tace "ina zaka kuma Besty?"tsayawa yay muryarsa fes babu tashin hankali yace "wai zan bar maku gidanku ne,bari kuma na har abada,kunyi aure ko?to Tabbas da kanku zaku warwaresa,zanje inda na saba rayuwa dama nazo ne wajanku a matsayin ku na wanda suka haifan,ina tunanin zaku share hawaye ne ku tauyamin ashe ba haka bane,nai kuskure da har na yarda zaku iya tayani neman abinda nakeso,amma babu komai kuna da iko akai na,amma wlh wlh nida zaman gida nan uhm..,"bai ƙarasa faɗa ba yay ficewarsa waje,wani kallo Ohinoyi ya bisa dashi yana jin zcyrsa na bugawa kafin ya saki wani Murmushin takaici ya miƙe tsaye tare da shigewa plat ɗinsa,kuka Mami tasa tana faɗin "wanne irin zuciya Aliyou yake dashi ne? Allah kai ka bamu wannan stubborn son ɗin Ubangiji ka daidaita maza zafin zuciyarsa".a chan asibiti kam Dr Sufyan ne cikin wani hali ganin har anyi ƙwana biyu babu Deen babu labarinsa,daman da wahala ace saurayi kamar Deen zai iya salwantar da yaruwarsa akan wata ƙaramar yarinya,yay trying number sa amma ko shiga ba tayi kullum a kashe,sabon Dr ɗin da yazo ne ya shigo cikin office ɗin tare da neman wajan zama ya zauna,kallon Dr Sufyan yay yace "what's the matter?"Dr Sufyan ya sauke numfashi yace "maganar yarinyar Moon kada ai saken da idanuwan ta zasu sulwanta" kallonsa kawai saurayin yay kafin ya miƙe yace "a shirya operation yanzo"yana faɗin haka ya fice daga office ɗinsa yana shiga ya Zara farar rigar jikinsa ya sanya wata green ta aiki tare da sanya facemask ya rufe fuskarsa,kai tsaye ɓangaren tiater ta nufa lokacin har an shigar da Moon,su Nana na tsaye bakin ƙofar,bai kulasu ba ya shige cikin tiater room ɗin,suna tsaye wasu likitoci suka shiga cikin tiater room ɗin sanye da kayan aiki,suna tsaye aka kunna wutar taiter, miƙewa Nana tayi ta fara addu'a Salmerh kasa zama gaba ɗaya addu'ar ta bai huce Allah yasa ai aiki lafiya ba, almost 2hours kafin a kashe wutar,chan kuma aka buɗe ƙofa ƙyakkyawan Dr ya fito ba tare kuma daya kalli su Nana ba ya shige office ɗinsa,wasu likitoci ne suka turo gadon Moon zuwa ɗakin hutu,tana ƙwance samɓal idanunta duk aduga da bandeji,bayansu sukabi har zuwa special room ɗin da aka ajjiye Moon,wani Dr ne ya kalli Nana yace "Dr yace na faɗa maku nan da ƙwana biyu za'a cire bandejin, congratulations aiki yay ƙyau"hamdala sukai atare kafin su nufi Moon,tana ƙwance amma fuskarta a kwaɓe kamar mai shirin yin kuka, sun nan tare da Moon har tsahun ƙwana biyu,a ranar ƙwana biyun da safe sabon Dr ya shigo,sanye da fararen kaya na likitoci idanunsa sanye da farin glass yay ƙyau sosai kamar Bature,hannunsa duk suna cikin aljihu,kallon su Nana yay yace "zaku iya jira a waje"fita sukai sudai basu san me ake ba sai kukan Moon da karaɗe ward ɗin tana kiran sunan Dad,bayan kamar 20minutes Dr ya leƙo da hannu ya kira su Nana kana ya koma ciki,da idanu Moon tabi Nana dashi tana mussiƙe idanunta sai kuma ta ƙara fashewa da kuka tace "i can't see it sosai komai dishi²"Murmushi yay mata yace "amma kina gani ko yaya?"kai ta gyaɗa masa, yace "Are u sure?" Nan ma kaita gyaɗa masa, wani ɗan ƙaramin box ya buɗe ya ciro wani siririn farin glass medical ya fito dashi a hankali kuma ya nufi manyan idanunta wanda sukai jaaa,kana ya maƙala mata, wow! Ya faɗa a ransa ganin yadda glass ɗin yay masifar yi mata ƙyau, ɗan washe baki tai tace "ma sha gani na ya dawo gareni" kallonta gaba ɗaya suke, itama kalle² ta fara kafin tace "where is my Dad?" Shiru sukai mata shi kuma Dr juyawa yay ya fita domin ɗauko mata wasu magunguna, fashewa tai da kuka tare da sauka daga kan bed ɗin ta nufi fita daga cikin room ɗin, Salmerh ce tabi bayanta tana "come back Moon,ur Dad is coming soon"tana buɗe ƙofar domin fita shi kuma yana buɗewa domin shigowa,karo sukai da juna kanta ya bigi ƙafafuwansa, ƙara ta saki tai baya sai kuma ta buɗe Murya da ƙarfi tace "Dad..!! Dad.."sai kuma ta faɗa jikinsa tana sakin sabon kuka, lumshe idanunsa yay yana jin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, miƙewa su Nana sukai tare da barin ɗakin,gaba ɗaya sunyi mmkin ganin sa kamar an kurosa daga shi sai 3gauter da farar singlet,yadda dake kuka sosai yasa a hankali ya miƙe da ita tare da nufar bed da ita,zama yay yana jin jiri na ɗibansa, kallonta kawai yake with much surprise ya kasa tantance abinda idanunsa suke nuna masa,jin yay mata shiru yasa ta ɗago kai tace "Dad..."sai kuma ta ƙara fashewa da kuka,rasa me zai mata yay kawai sai ya haɗe fuskokinsu waje guda ya shiga sauke mata