Sashe 26
Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
yana nipples ɗin sunyi jajirr,zama Damus yay yace "oga Taju tace a haɗa masa meeting dakai,amma dai bai faɗi venue ba,sai zuwa jibi yace zai faɗa amma bana jin zai zo nan sai sai a ɗauki jet zuwa PAKISTAN" shiru Deen yana jin wata faɗuwar gaba,mutumin da babu wanda ya taɓa ganinsa shi ne sai zai zauna dashi for what reason?kamar Damus ya shiga zuciyar Deen yace "about Moon's problem" da sauri Deen ya kalli Damus saurin ɗauke kansa Damus yayi yana jin gabansa na faɗuwa domin shima sai yanzu yay dana sanin gayawa Taju abinda ke faruwa, kaɗan daga cikin aikin Taju yace a maida Moon Pakistan da zama, miƙewa Deen yayi ba tare daya cewa Damus ci kanka ba ya bar wajan.misalin 4:00 driver yay parking a harabar asibitin yana gamawa ya fito da sauri ya buɗe ƙofar motar, Deen ya fito sanya da wata black suit masu ƙyau sai red ɗin butterfly sumar kansa a ƙwance har wuyansa dan ko ɗaurewar da ribbon yau bai ba,ya sanya fararan ƙafarsa cikin half covert shoe mai ƙyau wanda ya kance red, hannunsa riƙe da wayoyinsa ya fita daga cikin motar zuwa cikin asibitin,har ward ɗin ya shiga kai tsaye kuma ya nufi office ɗin Dr Sufyan,zaune ya samu Dr Sufyan shida wani suna magana,bai zauna ba ya tsaye tare da harɗe hannayen sa a saman ƙirjinsa ya ɗan lumshe idanunsa,yana tsaye suka gama maganar har mutumin ya fita a office ɗin, Dr Sufyan ne ya kalli Deen yay Murmushi yace "ai ka nemi waje dai ka zauna ko kafi fahimtar Abinda zan faɗa maka"kujera yaja ya zauna kana ya kalli Dr Sufyan alamar shi yake saurare,zame glass ɗin idanunsa yayi kana yace "bayan fitarka wani babban likita ya zo,ya ƙara mata scanning sosai,yace a yau ba za'a iya yi maku operation har a sanya mata idanun ba,yace sai nan da ƙwana biyu,yanzu dai ya bada wasu eyes drugs za'a dinga ɗiga mata kafin lokacin operation yayi,dan haka saika shirya nan da ƙwana biyu za'ai sauyan idanun" tunda ya fara magana Deen yake kallonsa,sosai yake mmkin yadda wasu mutanan idan suka fara magana basa ko haɗiyar yawo, jinjina kai kawai yayi kafin yace "okey" A.t.m ɗinsa ya fito dashi ya bawa Dr Sufyan yace "ku cire duk kuɗin da kuke buƙata, I'll travel now, And sai lokacin aikin yay zan dawo in sha Allah" Dr Sufyan yace "ai basai ka bayar ba, abinda kuna nan idan an gama komai kayi payment ɗin" bai ƙara magana ya ɗauki a.t.m ɗin ya saka cikin pocket ɗin sa,room ɗin ya nufa,shiga yay ƙamshin sa kawai ya sanar masu cewa shine tun kafin ya shigo, Salmerh dake Sallah tai shiru sai Nana ta amsa masa sallamar wacce yayi ta ƙasan maƙoshinsa,wajan bed ɗin ya ƙarasa tana ƙwance tana bacci numfashinta na fita a hankali ta kwaɓe fuska kamar zatai kuka,farinta ya ƙara ƙaruwa, tattausan hannunsa ya sanya saman lips ɗin ta yana ɗan buɗawa,fari fat yaga lips ɗin nata,harya kai hannu zai taɓa idanuny ya manta ansa cotton a idanun,kafin Deen yay magana Dr ya shigo da sauri yace "i almost forgot, za'a sanya mata blood idan ka amince a saka mata wani shkknan daman amincewar ka ake nema, ɗan ɓata rai Deen kana kuma yay shiru, Dr Sufyan yace "ina da marasa lafiya fa"kallonsa Deen yayi sai kuma yay ƙasa da kansa yana ɗan rage gudun drip ɗin kamar wani likita kana yace "muje ka ɗauki nawa"gaba ɗaya suka kallesa har Salmerh dake addu'a,bai kallesu ya kalli Moon kana ya kalli Nana yace "take care of her" Nana tace "I'll" idanunsa akan Moon kana ya juya yabar room ɗin da sauri, bayan Dr ya gwada jinin Deen an tabbatar da lafiyarsa kuma za'a iya sanya Moon jikinsa kasancewar jininsa O ne,ya ɗauki jinin leda biyu kana aka kawowa Deen maltina da milk kaɗan yasha ya miƙe ya nufi waje,back seat ya zauna ya lumshe idanunsa a haka drive yaja zuwa airport,jirginsu bai wani daɗe ba ya sauka a kogi,a airport ɗin yaga motocin palace ɗin su na jiransa,tun kafin ya shiga mota aka bashi wata lafiyayyiyar Alƙyabba da hula mai ƙyau ya sanya,sai ya ƙara girma kwarjinin da da haibarsa suka ƙara fitowa,gaba ɗaya fadawan suka zube suna gaidashi,bai kulasu ba ya nufi wata mota ƴar ƙarama yana shiga suma suka shiga motar wajan motocin goma sha haka suka marawa motar Deen baya suna tafe a hankali da jiniya a haka suka shiga palace,ana gama parking da motarsa ya fito da sauri harda gudu ya haɗa zuwa cikin gidan Sarautar lokacin Ohinoyi yabar cikin fadar sbd dare yayi,a babban danning Area ya samesu, yana shiga parlour'n ya cilli da alƙyabbar jikinsa kana ya nufi wajan OHINOYI yana zuwa ya faɗa jikinsa yana sauke numfashi,kansa Ohinoyi ta shafa tare da faɗin "meke damun Besty ne? Nene dake zaune kusa da mijinta tace "what wrong Besty? Shiru duk yay masu yana fidda numfashi a hankali zcyarsa na bugawa da ƙarfin gaske,ganin hakan yasa Ohinoyi ajjiye knife ɗin hannunsa wacce yake yankan nama da ita hannunsa ya wanke tass,sannan ya ɗaga Deen daga jikinsa shima ya miƙe tsaye, rungome sa yay sosai shima Deen ya rungome Abban nasa,da sauri shi ya saki Deen sabida wani a zababban zafi da yaji yana fita ta cikin jikinsa ga wani numfashi da yake fitarwa,cikin ɗaga Murya Ohinoyi yace "what happened?what happened to you ALIYOU? Idanunsa yana ɗan lumshe ya kama hannun Ohinoyi ya ɗura bisa saitin zcyarsa wacce take bugawa da ƙarfin gaske kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito, taune lips yay jikinsa yana ɗan rawa sbd daman ba lafiya garesa ba, jijjigasa Ohinoyi ya fara ganin yana shirin sume masa,da ƙarfi kuma yace "meke damunka? Please dan Allah ALIYOU ka gayamin me ke damunka? me kakeso?" Bakin Deen na rawa idanunsa na zubar da hawaye kamar ba Deen da muka sani ba, lumshe ido yay kana ya danne saitin zcyarsa da ƙarfi kafin a hankali bakinsa ya shiga furta "i want be on her side Abba, ina son auranta Abba,ina son......,"maganar ce ta maƙale sabida numfashinsa daya ɗauke ya faɗa jikin Ohinoyi a sume...