Sashe 4
Moon Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Girgiza masa kayi tayi ba tare data ƙara magana ba tayi lamo a jikinsa,turo da yatsan daya sa mata a baki tayi,kafun ta kallesa taga ya rufe idanunsa yana bacci,hannunta tasa ta shafi sajensa tace "laaaa Dad kaima kana da irin na Dad na" shuru yayi mata bawai dan baya jinta ba,lips ɗinsa ta taɓa ta ƙara faɗin "Dad kaima kana shan sweet ne" kafin ta ƙara faɗin wani abun aka fara bugun ƙofar ƙaramin ɗakin nasa,da sauri ya miƙe tsaye tare da ɗaukan Moon ya sanyata a bayan ƙofa, buɗe ƙofar yayi ganin Alhaji tsaye yasa yayi shuru yana kallonsa kafin yace "mrng Alhaji" Alhaji yace "mrng too ba zaka fito ai jana'izar da kai bane?" Ƙasa yayi da kansa sbd kallon da yaga Alhajin nayi masa gaba ɗaya ya manta cewa gashin kansa a kunce yake,cikin basarwa yace "eh,ban jin daɗi ne" jinjina kai Alhaji yayi alamar gamsuwa kafin ya juya ya nufi cikin motarsa yayi waje,yana zuwa ya fito daga motar ya karasa wajan jami'in jana'izar da za'ai,gaba aka shimfiɗesu su uku har yanzu jini bai bar zuba daga cikin ko wannan su ba, addu'ar da ake yi a cikin sallar jana'iza Liman ɗin ya fara.
"اللهم Ø§ØºÙØ± لله وارØÙ…ه،وعاع٠عنه،وأكرم نزاله،ووسع مدخله،واغسله بالماء والثج والبرد،ونقه من الطايا كما نقيت الصوب الأبيض من الدنس،وأبدله دآرآ خير من داره،وأهلا خيرآ من زوجه وأدخله الجنة،وأعذه من عذاب القبر وعذاب النار."
_(Ya Allah ka yi masa gafara,ka jiƙansa,ka amintar da shi daga bala'i ka yi masa rangwame,kuma ka girmama liyafarsa,ka yalwata mashigarsa (kabarinsa), kuma ka wanke laifukansa kamar yadda ka ke tsaftace farar tura daga dauɗa, kuma ka musanya masa gidan da ya fi gidansa alheri,da mutanen gida da suka fi mutanen gidansa alheri,da mata matar da ta fi matarsa alheri (da mijin daya fi mijinta alheri) kuma ga shigar da shi /ita aljanna,ka tserar ta da shi /ita daga azabar kabari da azabar wuta)_
Ana kammala jana'izar aka miƙa su zuwa gidansu na gsy,bayan an dawo Alhaji yana zaune a saman danning yana breakfast gefensa Farouk da Yasmin sai matarsa Hajja khadu suna kiranta da Ummi ta kallesa tace "wannan lamarin yana bani mamaki,ace an kashe kowa na gidan amma a rasa inda ƙaramar yarinya take,wannan wacce irin rayuwace yanzu wa yasan halin da yarinyar take ciki, Allah yana gani da za'a ga rinyar nan nice zan riƙe ta,Alhaji anya ba wanda suka aikata wannan abin bane suka ɗauke ta ba?" Ta faɗa tana ɗaukan tea tare da kaiwa bakinta Farouk yace "Ummi ko ajiya naga yarinyar ta tsallako titi hannunta riƙe da ice cream,sosai nai mmki sbd ban taɓa tunanin aƙwai wata ƙaramar yarinya ba a cikin gidan" Ummi tace "Nima sau ɗaya na taɓa ganinta,kamar dai basa barinta fita tunda ko compound na gidan da wahala ka ganta ciki" sai lokacin Yasmin tace "to Ummi ko dai ɓoyeta suke?" Kai Alhaji ya ɗaga ya kalli autar tasa kafin ya miƙe yace "Auta me zai sanya a ɓoye ƴar ne? Kawai da bata da cikakkiyar lafiya shiyasa ko da wanne lokaci a kuma ko ina ciwonta na iya tashi"yana faɗin hakan yay shuru da bakinsa ya nufi part ɗinsa, cikin ƙasa da murya Farouk yace "Ummi meke damunta?" Miƙewa Ummi tayi tace "Ni tayaya zan sanan wannan lamari Allah dai ya bai yana ta,ko kuma ya kaita hannu na gari, Allah sarki ƙyakkyawar yarinya da ita"