← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 36

Sashe 8

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"barka dai man...ka shiga daddynka nason ganinka"gabansa ne yadan fadi"lafiya?"ya tambayi momy,ta girgiza kai tana murmushi "ka shiga zakaji koma menene"tace ta maida hankalinta kan tv tana cin apple din dake hannunta tsaye yayi ya kasa motsi haka kawai ya tsinci kansa da faduwar gaba.....

*SLIMZY*✍🏻
[09/11, 15:00] 😍Slim girl❤️: 💥 *MAZA BIYU....*💦

*NA:SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33

*Marubuciyar:*

*K'ADANGARUWA*🦎

*RUD'ANI*💥

*DUHU....*🌑

*5*
"yanzun ke innahr Dina Ashe abinda ke faruwa Kenan baki fada mana ba?dama ance akwai wasu baki yan birni da sukazo daga cikin birni kamar turawa tare ake ganinsu da Dina koda yaushe na karyata sai gashi labari ya isar mun cewar ai salisu ya gansa a kofar gidan nan yana shaye shaye kuma yace wajen Dina yazo"shiru innah tayi tana sauraren mahaifiyarta dake zaune gefenta tasi'u ne dan gidan goggo lubabatu kanwar innahr dina,"ina magana kinyi shiru bakice komiba bayan magana taje har wajen mai gari to labarinku akeyi kaf a garin nan yanzun akan Wandan Yan birnin sun gama lalata Dina"da sauri innah ta kalli mahaifiyarta dake magana cike da masifa tace "baba kulu anya maganar da ake fada gaskiya ne Dina bazata tabayin lalata da wani ba a cikin garin nan balle wajen garin nan kuma wanan yaron da ake magana"Dina ce ta fito daga daki ta tsaya tsaye tana binsu da wani irin kallo musamman da taga tasiu tare da kakarta tasan daga wajensu munafuncun ya bullo tsaki taja ta tsirtar da miyau ganin wani kallo da tasiu keyi mata da jajayen idanuwansa ya washe baki hakoransa jajir kamar ruwan goro "wanan maganar karya ce makirci aka shirya dan aga bayanmu an bata mana suna babu wani Dan shaye shaye kuma ai gara Mansoor shaye shaye yakeyi ba mazinaci bane"tayi maganar tana watsawa tasiu wata irin harara,

"ke waye mazinacin?dawa kike?"tasiu yayi maganar yana mazurai ta rike kwankwasonta tace "Kai idan kana ganin tsoro nakeji na fada maka mazinaci ne kai banajin tsoronka ban kama ka da asabe a lungun gidan mai gari ba ta dauko talla ka sauke kana tattaba ta?idan karya nake Allah ya tsinen"salati baba kuluwa ta rafka "au kema neman abinda zaki kare kanki kikeyi?zaki kulla masa sharri tou kisani idan ma soyayya kukeyi da wanan balaraben baxaki taba aurensa ba dan bamusan kosu waye ba sun gina gidan gona a kauye suna zuwa bamu san irin kudinsu kona shan jini bane yauwa ko kinki ko kinso baki isa ki bata mana suna ba"innahr dina ranta a bace ta share hawayenta zayayi Magana dina ta amshe "oho dai niba soyayya mukeyi ba yauwa abokantaka yakeso muyi kuma yace indai na Amince zai daina shaye shaye kuma malamarmu tace yanada kyau ka zama silar shiriyar wani dan haka zan gwada tawa saar indai yazo garin nan "wani gigitaccen mari Dina taji ta bayanta da sauri ta juya taga babane ya shigo da buhunsa a hannu yace "ke dina da kunnena nakejin zaki abokantaka da dan shaye shaye akwai abokantaka tsakanin namiji da mace ne?inba lalatattun yan birni ba?ke dina anya kudin da nace zan samu in kaiki makaranta ma zai yuwu ba aure zanyi miki ba?"ta dafe gefen kumatunta ranta a bace zucuyarta nayi mata zafi da zarar aka Kira mansoor da dan shaye shaye ita kadai take kiransa da hakan itama tanayi ne badan zucuyarta naso ba sai Dan tanajin matukar zafi idan ta gansa Yana bushe bushen nan kasancewarsa kyakkyawa ajin farko uwa uba ga turanci alamu sun nuna yanada ilimi sosai,

baba kulu ta mike ta kakkabe zaninta tana nuna dina "kai tasiu tashi mutafi ka gayawa luba idan kaje ta fara shiri ko taki ko taso sai ta aureka inaga salisu abinda zamuyi kawai shine muyi auren yaran nan shine zai raba Dina da wadanan yan birnin kuma tasiu kasa ido sosai akan dina dik inda kaga tayi ka bibiyeta kaga da su waye take tare ka fadawa mahaifinta gashi"ta nuna baban dina dake tsaye ransa a bace , Baba kulu surukarsa ce an basa auren mahaifiyar dina ne kasantuwar ansan wasu kakanninsa amma shi kansa bashida kowa a garin bayaso Dina ta auri tasiu da wani zai fito daban bashi dinba a gaggauce zai aura masa ita,innahr dina kuwa zaune tayi kamar an dasata dole tasa salisu mahaifin dina ya aurar da dina ga tasiu ko bayaso kodan kada ta raba mata zumunci,
bayan fitarsu zama yayi yaba fuskantarta zaiyi magana ya dago ido ya kalli Dina "ke tashi a nan kafin in kakkaryaki dik wanan masifar kece kika janyota ai gashi nan yanzun abinda baba kulu tace bani waje"ta tura baki gaba tana kunkunai ta shige daki tana bubbuga kafa cike da takaici tace "ko yau yazo garin nan zan kulasa saboda ina kwadayin samun lada ko zaa kasheni ai shima da ne kamar kowa"ta zauna a kasa ta rafka tagumi,

"kinaji innahr Dina kiyi hakuri kidaina wanan kukan,sam banason tasiu ya auri dina saboda kinga basu dace ba ki duba kiga irin dabiun tasiu kwanaki ina wajen mai gari aka kawosa akan ya saci kaji uku an gansa dasu zai saidawa wasu baxanso yata ta hada iri da barawo ba"wani kallo innah tayi masa "sai da dan shaye shaye ko?"cije lebe yayi yace "da wani zai fito daban basu ba da zan bashi da rayuwar dina ta lalace ko fahimceni"innah ta mike ta kakkabe zaninta tace "ni baxakajamun masifar baba kulu a garim nan ba koba komi mahaifiyata ce"tana gama maganar tayi daki,ransa nayi masa zafi da kuna ba wanda ya jawo fitinar nan sai Dina data shigewa wadanan yan birnin dole ma zan rabata dasu ya mike yabi innahr dina daki,...
********
"ya naganka dik kana wani mazurai mansoor daga ina kake ko kauyen ka tafi?"gabansa ya fadi ya girgiza kai "tunda son zaman kauyen kakeyi nasamo maka mafita"a kufule daddy yayi maganar, Mansoor yadan ware ido cike da faduwar gaba yana jiran me daddy keson fada masa "kai nasamu wani distributor daga U.K zaa turo mana dabbobi daga can irin nasu da naso na turaka can din ne"gaban mansoor ya yanke ya fadi wasu zufa ke tsattsafowa daga goshinsa ya kallli daddy yana jiran me zaice daddy ya tsare sa da ido yana karantar yanayinsa,cikim zucuyar mansoor kuwa fadi yakeyi "no no am not going any where daddy i don't want to go i want to change that Village girl no matter what idan natafi ya zanyi?waye zai rinka baxamun wanan haukar tata?"daddy yace "kai tunanin me kakeyi haka?"da sauri yadan lumshe ido hade da murmushi "ba tunani nakeyi ba ina jiran naji me zakace ne"daddy ya girgiza kai yace "you are hiding something to me mansoor"shima girgiza masa kai kawai yayi ba yanzun yakeso asan yanada wata dangantaka da Dina ba,"tou dama so nakeyi kuje garin can kaida sameer kusamu sati daya idan sun iso zuwa jibi ni kuma zansa a motoci a kawo muku can da maaikatan can asa komi yadda ya kamata a cigaba da kula dasu"cakkk Mansoor yayi yana kallon daddynsa ji yakeyi kamar a mafarki daddy ke maganar yace "you mean daddy zamuje kauye muyi sati daya?"daddy ya jinjina masa kai "yes ko kanada wani abinda kakeyi a nan ne daya wuce yawon club da shaye shaye mansoor? gara katafi kauyen ka zauna a can da maganar daka daukomin ranan fisabilillahi yar aminina ka mara?haba mansoor ka kira sameer ko kuma ni zan kira daddynsa akai dan nasan shima bazai zauna a nan baka nan ba kaima bazaka zauna kai kadai Acan batare dashi ba"wani farin ciki ne ya lullube Mansoor yayi wani murmushi da ya karawa fuskarsa kyau yace "Toh shikenan daddy zamuyi shiri"yana gama maganar ya mike cikin farin ciki zai fita daddy ya tsayar dashi look,cakk Mansoor ya tsaya hade da juyowa "momynka tayimun bayanin tsakaninka da nabeeha idan ka dawo zaayi zancen aurenku ko hakan zai zama silar dena Shaye shayenka,wani faduwar gaba yaji cakk ya tsaya ya kasa motsi jikinsa ya soma rawa,dakyar ya seta natsuwarsa ransa a bace yake ya kasa cewa daddy komi wato nabeeha ce musu tayi shi zata aura?bazaice komiba yanzun dan kar ya bata shirinsa na zuwa kauye daddy ya fasa amma yasan me zaiyi,fitowa yayi daga sashenn daddy yana fitowa yaji hayaniya cike fa gidan ransa a dan bace,

momy na zaune a parlor. ya sauko ya hada girar sama data kasa,ganin wacce ke zaune gefen momy ya soma dariya yace "welcome my favourite",dariya itama tayi masa wata matashiyar macece da momy Zata dan girmeta saidai daka kalleta kasan yar uwarta ce dan suna tsananin kama "my son kwana biyu ina ka boye?"da sauri nabeeha ta amshe "baya zama yanzun kauye yake tafiya"tace "really kauye?doing what?"zura hannunsa yayi aljihunsa ya watsawa nabeeha harara yace da wani irin kallo mai cike da tsana,tayi saurin kasa da kai yace "and yanzun din ma can zan tafi so sai ki cigaba dasamun ido"momy ta amshe "ka tattara ka koma can ma koma me kake kullowa watarana zai fashene kuma nagama yanke hukuncina"tana hararsa take maganar,....ya zauna gefen Aunty zaleeha yace "Anty inataso nazo nasameki akwai muhiimiyar maganar da nakeso muyi,kinsan ke kadai nake fadawa abuna"yayi maganar fuskarsa a daure as usual dariya tayi tace "nasani ko nasamu suruka ne?"da sauri ya girgiza kai yaga dukkansu shi suke kallo ya harari rufaida "munafuka lafiya?"gimtse dariyarta tayi ta mike "babu ruwanmu kaida Antu zallyn ka ne mu yan kallo ne ya nabeeha muje daki kiji wata magana"gaba daya hankalinta yana kansa ta tsura masa ido tanajin wani irin kishi akansa tana tsananin son ya mansoor gashi har yau hankalinsa baya kanta dikda momy ta fada mata ta fadawa daddy soyayya suke,rufaida ta zungureta "mai kike kallo ne haka"Anty zali tayi dariya tace "ya man take kalla"shi kuwa cewa yay"ai mayya ce, let's me call Sameer akwai albishir dim da zanyi masa ma,karku batamun mood, Anty zali now zan kiraki kawai ko kuma gobe kafim nabar garim nam zan shigo gidan naki"tace "okay sir"tana murmushi shima murmushin yayi mata ya mike ya shafa kan yaronta Adnan dake zaune gefenta ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya fice,
Chapter 8 · 0% Book details