← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 36

Sashe 16

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ina magana mansoor kayimun magana nace wacece kake kokarin gurbata musu tarbiyyarta?"still beyi magana ba nabeeha idonta ya kawo ruwa wato dama akan wata yar kauye yake wulakantata?daddy yace "tou ka bude kunnenka da kyau ka saurareni Mansoor,idan nina haifeka na rabaka da wanan yarinyar harabada,sanan kaje kabawa mahaifinta hakuri"mansoor ya Shiga girgixa kai da sauri sameer ya zunguresa cikin rad'a yace "kace Toh"mansoor ya girgiza kai yace "Daddy i cant,i want to help her nifa ba"dakatar dashi daddy yayi "iyyeee nace kayi abu kace bazakayi ba ko? tou dik abinda kakeyi jibi jibin nan ka tattaro ka baro kauyen nan ka dawo gida idan baka dawoba dik hukuncin dana yanke akanka kaika siya"

"naji"mansoor yace be jira me daddy zaice ba kawai ya datse wayarsa,

"kingani?kashe wayarsa yayi bejira me zance ba dan ubansa ya dawo in tara mutane im daura musu aure da nabeeha subar kasar nan kafin ya daukomin maganar kauyawa"momy tayi kwafa tace "ninasan baa banza suke dokin zuwa kauyen nan ba shida sameer ashe da abinda suke shukawa to dukkansu aure zasuyi mu huta shima momynsa dazun take cemun anyi maganar aurensa,ran daddy a bace yabar parlon,

cike da masifa Sameer yace "meyasa kayiwa daddy musu?ba haka naso kayi ba gashi ka bata komi yanzun ai"murmushin takaici mansoor yayi yace "haka kake gani?ban bata ba ina sane da abinda nakeyi koda nake shaye shaye,ba mahaukaci bane ni inada hankalina bazan taba masa karya akan abinda nasan bazan iya ba,bazan taba rabuwa da Dina ba,kuma bazan taba bawa mahaifinta hakuri ba bayan shine ya mareni wanda inda kotu zan kaisa sai ya Biyani diyyar marin da yayi mun,abinda nasani shine zanyi masa biyayyar komawa jibi kamar yadda yace amma kafin inbar garin nan i will fix everything daya shafi Dina da cikar burinta"

"ciki harda karatunta?da hana aurenta da tasiu bayan shine kudirin iyayenta?"Sameer yayi maganar yana kallons yace "yess ciki harda daina Shaye shaye da zanyi na gaske bana karya ba'tsura masa ido sameer yayi yana mamakin yadda mansoor ya sauya,

Dina tana shiga bayan gida ta ciro wayarta daga wandonta jikinta na rawa ta rufe kofar ta leka ta jikin ramin katangar ban dakin taga innahrta na alwala zata shiga daki hakan ya bata damar Ciro wayarta tana adduar Allah yasa ta iya kiransa,cikin saa ta danno ta kara dannowa taji kara din din......tayi saurin sawa a kunnenta tana adduar Allah yasa kiran ne,

yana kishingide yaga wayarsa na haske ya kalli wayar "peace of mind"yayi mata saving ya mike ya zauna yana murmushi sameer yace "yadai?"

"peace of mind ke kirana"cikin rashin fahimta Sameer yace "waye haka?"

"Dina....."ya bashi amsa a takaice,galala sameer yayi yana kallom ikon Allah......

*SLIMZY*😍
07042277401
[12/11, 09:31] 😍Slim girl❤️: 💥 *MAZA BIYU....*💦

*NA:SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33

*Marubuciyar:*

*K'ADANGARUWA*🦎
*RUD'ANI*💥
*DUHU...*

JAMA'A, INA GABATAR MAKU DA ROYAL EXQUISUTE, GIDAN GYARAN AURE, GIDAN AMINCI, GIDAN GIGITA MA'AURATA, JAMAA INA AMARE? UWAYEN GIDA? ZAWARAWA? DA KUMA MASU JEGO, INA MATA? MATAN DA SU KA AMSA SUNAN SU MATA? MATAN DA SUKE SON ZAMA DARAM DAM A ZUKATAN MAZAJEN SU? MATA ƳAN ƘWALISA? TO WALLAHI ROYAL EXQUISUTE NA KU NE, SUKE DA INGANTATTUN KAYAN MATA NA GYARA BA WAI TAWULWULBA, BA WAI SHA KA TAFI BA, KAYAN MATA DAKE ƘARA DARAJA DA ƘIMA WAJEN OGA, GA SAUƘI GA ARHA, GA KUMA AIKI..ROYAL EXQUISUTE ZATA GYARE KU
KI TUNTUBI WANNAN NUMBER 08030644073
Location kano,nationwide delivery

*10*

"Hello.....Dina"yace a sanyaye yana lumshe idonsa,bugun zucuyarsa ne ya sauya jin yadda tayi shiru ta kasa magana,batasan lokacin da hawaye ya soma zuba daga idanuwanta ba tana sauraren yadda yake sauke numfashi minti minti,"Dina....ashe kin iya kiran waya"yace cikin zolaya dikda yadda gabansa ke tsananin faduwa bukatarsa kawai tayi magana,share hawayenta tayi taja majina yace "what kuka kikeyi?meyasaki kuka?"ya tambayeta cike da kosawa,
"Dole zanyi kuka nasan baa kyauta maka ba ya man...inata tunaninka nasan kayi fushi dani bansan hanyar da zanbi inzo gareka ba baba yasamun dokoki masu tsauri akanka ni kuma bazan iya jure hakan ba nasaba dakai dayawa"shiru yayi yana sauraren siririyar muryarta mai zaki,dikda kuka takeyi amma sautin muryarta kadai ya haifar masa da sukuni da kwanciyar hankali ya lumshe ido ya sake budewa yace"is ok ya isa kibar kukan banyi fushi dake ba bazan kuma tabayin fushi dake ba kinji?haka bazan taba iya rabuwa dake ba sai na cika miki burinki,inaso na sauyaki na sauya rayuwarki Dina,hakan yasa nake tunanin yadda zaayi ki fara karatu dikda nasan mahaifinki ya tsaneni matuka,bansan hanyar da zanbi ba wajen ganin na inganta rayuwarki kafin na mallakeki"shiru tayi tana saurarensa,hawaye na cigaba da zuba a idanuwanta ta nisa"na cire rai da samun inganci a rayuwata ya man....domin yanzun haka shirye shiryen aurar dani akeyi ga tasiu wanda kuka samu matsala,sanan kasani banajin zaka taba mallakata domin bamu dace da juna ba hasalima ba soyayya mukeyi ba abota ce"..ajiyar zucuya ya sauke yace "mahaifinki ya fada ne kawai yana barazana amma banajin zai iya mikaki ga wancen mahaukacin yaron jahili wanda besan abinda yakeyi ba,saboda haka ki kwantar da hankalinki kinji?"ta jinjina kai kamar yana ganinta tace "naji shikenan yanzun ma boyewa nayi dan in kiraka kar innah ta tanemeni kaji?an hanani zaman daki gudun kada na tafi wajenka"murmushi yayi yace "karki damu ni zanzo gareki koda zasu tsireni kinji?kinason ganina?"damm gabanta ya yanke ya fadi tayi shiru ta kasa magana idan tace batason ganinsa tayi masa karya,kuma idan tace tanason ganinsa yazo kofar gidansu batasan meye zai faru ba hakan yasa batace komi ba yace "shikenan ba komi zamuyi magana Anjima kinji zansan yadda zanyi na ganki nima jibi zanbar garin nan"wata irin faduwar gaba ce ta ziyarceta wadda batasan dalili ba nan da nan taji wani jiri na neman yadda ita, har ya kashe wayar ma bata sani ba dafe kirji tayi tai shiru ta kasa ko motsin kirki dakyar ta tashi daga kan dutsen datake zaune cikin ban daki ta dauko buta a sanyaye ta fito,

jigum jigum ta sammu innahrta zaune da uwaliya makociyarsu wadda gidansu ke hade tabi Dina da kallo itama kallonsu takeyi cike da tsoro ta dire butar ta karaso ganin hawaye nabin fuskar innahrta,

"Innah karkicemun nice silar wadanan hawayen dake zuba a idanuwanki Innah meyafaru?mutuwa akayi?"ta juya ta kalli matar dake zaune gefenta ta rafka tagumi tace "baba uwale lafiya?mutuwa akayi meyafaru naga innah ta tana kuka"ta zauna dirshan a gaban innahrta tana tambayarta,

dakyar innah ta bude baki tace "burinki ya cika Dina.....burinki ya cika yanzun babarku lubabatu ta aikomin da sakon cewa tasiu bazai aureki ba dan ana zargin ciwo gareki wadanan yan birnin sun gama dake"wani abu taji ya caki tsakiyar kanta kamar mashi,gabanta ne ya yanke ya fadi nan da nan ta soma ganin duhu a gabanta wanda yasata saurin rufe idanuwanta,

"kedai Dina baki kyautawa kanki ba ga abinda kika jawowa kanki nan bacin suna ga iyayenki gareki ke kanki kaf kauyen nan babu wanda ya kaiki kyau kaf yan matan garin nan samari rububi sukeyi akanki sosai musamman idan anje dandali yan matan nan babu wadda ta kaiki kasuwa gashinan dik inda ka bulla cikin garin nan maganarki akeyi hakan ya zama sanadiyyar rabuwar zumuncin innahrki da yar uwarta"Dina kasa magana tayi tsananin bacin rai da bakin ciki dikda ta gefe daya wata rahma taji ta saukar mata dan babu yadda zaayi tayi rayuwa da tasiu a matsayin mijin aurenta data aureshi gara ta auri malam salihu mai kasa kanwa a bakin kasuwa dikda ko wanke baki bayayi amma shi ba dan iska bane,dakyar ta mike batare da tace komiba ta nufi dakinta da niyyar shiga "ke Dina"sai lokacin innahrta tayi magana a kausashe ta tsaya "ina zakije?zaki shiga ne ki fita ta jikin bango yadda kika saba?"girgiza kai tayi a raunane tana hawaye tace "innah babu inda zani kaina ne yakemun ciwo sosai shine nakeso nad'an kwanta ko zai daina"kwafa innah tayi kawai ta kauda kanta Dina ta shige dakinta ta fada kan yar katifarta tana sauke numfashi wani sabon kuka ne ya kufce mata wanda batasan dalilinsa ba....
*******
"nabeeha na fada miki ki kwantar da hankalinki idan kinga baayi aurenku da Mansoor ba to numfashi ne banidashi a doron kasa kuma bazan taba barinsa ya kwaso wata yar kauye ya kawota cikin dangin mu ba,nina fara zargi ma Allah yasa ba asiri kauyawa sukayi masa ba ganinsa dan birni da mota babu abinda bazasu iya ba"nabeeha ta share hawayenta tace "momy tunfa daya tafi idan nakirasa bana samunsa tundai ranan da nakirasa har wajen asuba call waiting kina ganin anya yar kauyen nan ce kuwa suke soyayya da ita?"momy ta dubi Anty zalli dake ta faman danna waya batace komi ba tace "ke kinki yin magana kodan saboda mansoor din Dan gidanki ne?tunda kikazo gidan nan ganin kaya bakice komiba kuma kinji abinda ya aikata"ajiyar zucuya kawai ta sauke tace "me zance?bayan mansoor din be dawoba tukunna?ai kubari muga isowarsa garin badai gobe bane akace zai dawo?ko jibi?idan ya dawo dik wacce zaayi sai ayi amma ke nabeeha wanan koke koken da kikeyi ba abinda zai haifar miki sai bacin rai,meyasa ma zaki kuka bayan dubi nan?"ta nuna gefenta set din akwatuna ne a gefe seto biyu na auren mansoor da nabeeha,ajiyar zuciya ta sauke ta kwantar da kanta a pillow ta lumshe ido cike da farin ciki can kasan zucuyarta tana kissima tafiyarsu Cyprus da Mansoor mahaifiyarta ta tabbatar mata da auren mansoor babu makawa dan akan hakan ta tafi garinsu tunda safe,hangosu takeyi a cikin jirgi ita dashi tasani baya sonta amma da zarar hakart ta cimma ruwa sai ya manta da wata ya mace a duniya saita maidashi bawanta,sai ya haukace akan kaunarta ballantana wata yar kauyen banza da zarar ta mallaki man.....ta gama samun duniyarta.....
Chapter 16 · 0% Book details