Sashe 18
Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Shiru Daddyn Mansoor yayi yana kallonsa ya kasa magana,shi kuwa gogan durkusar da kansa yayi kasa tunda ya zauna bece masa komiba,momy ce ta shigo da sallamarta dauke da tray na flask da cup da kular abinci ta dire tana jifan mansoor da wani irin kallo,zata fita yace "dawo ki zauna muyi a gabanki kiji abinda danki yake fada"gaban momy ne ya fadi ta dawo da baya ta zauna tana fuskantarsa"Alhaji meya fada?meyace maka?kardai abinda nake zargi ke shirin faruwa"girgiza kai kawai daddy yayi yaja ajiyar zucuya yace "ya fada miki da bakinsa"yana nuna Mansoor yace "oya fada mata naga kamar sauri kakeyi ko?dan na fahimci dik maganar da mukeyi hankalinka baa nan yake ba"sai lokacin mansoor ya dago kai suka hada ido da momy data zura masa ido shi besan meye zai fada musu ba gabaki daya baya cikin hayyacinsa burinsa be wuce su gama magana ya tafi wajen Dina a asibiti ba ya barota ita kadai dikda yasan sameer na wajenta amma yasan shima akwai abinda zaiyi a wajen aiki,"kayi mata bayani ga mahaifiyarka na saurarenka"mansoor ya kara tamke fuskarsa hade da kauda idonsa gefe yace "momy nifa ban taba fada miki inason nabeeha ba,dan haka banida raayin yin aure yanzun kuma ko inada raayin yin aure bazan aureta ba dan ba ita bace zabina"wani zabura momy takeyi tace "karya kakeyi mansoor wallahi baka isa ba karyarka Tasha karya wallahi mu muka haifeka ko kai ka haifemu?yar Aminiyar tawa?tazo gidan nan wata da watanni zaman jiran lokacin aurenku?amma ka bude baki kace ita ba zabinka bace?sai uban waye zabin naka eyee?ko yarinyar da kaje kayiwa ubanta rashin kunya akanta zaka aura?yar kauye dangin kazzuwa zaka auro?",furzar da wata iska yayi daga bakinsa idanuwansa jajir ya kalli agogon hannunsa yace "Daddy bazan auri nabeeha inbar kasar nan da ita ba da sunan mata,idan maganar shaye shaye kukeyi nabar shaye shaye"cikin sauri daddy ya dago yana kallonsa cike da mamaki,ya jinjina kai yace "dagaske nakeyi na daina shaye shaye daddy kamar yadda kaji nafada inhar dan shaye shaye zaayimun aure na daina,nayi mata alkawarin haka"
"ita wa?"daddy ya tambayesa cike da mamaki ya cije lebe kawai bece komiba ya mike tsaye yana kokarin fita daddy ya daka mai tsawa "ina zakaje muna magana dakai?kanada wata wadda kakeso shine ka bari akayi muku baiko da nabeeha?"mansoor ya kada kai yace "Daddy ni bansa ayimun baiko da nabeeha ba dan haka bazan aureta intafi wata kasa da ita ba, idan dagaske ne maganar kasuwancinka ce kadai zata kaini zan tafi amma bada aureba idan kuma kuka matsamun akan sai na aureta na tafi da ita tabbas zakuga ba daidai ba dan bana raayinta"yana gama maganar ya fuzgi labule ya fice cikin sauri cike da bacin rai,
kuka momy ta fashe dashi cikin takaici tace "kana ganin abinda yaron nan yake fada ko?kanajin maganganun dayakeyi wallahi be isa ya watsamun kasa a ido ba be isa ya shiga tsakanina da Amincun mahaifiyar nabeeha ba idan an daura mai aure da ita yayi dik abinda zaiyi amma aurensa da nabeeha babu fashi idan kuma ya dage akan bazai aureta ba to tabbas zai gamu da fushina sanan dik yarinyar daya bullo da maganar aurenta ko yar gidan uban waye bazai aureta ba bada yawun mu ba"ta fice cike da takaici, tagumi daddy yayi yana mamakin wanan tashin hankali na hajiya saadatu....
******
yana isa asibitin ya shiga nemanta be sameta ba hankalin mansoor ne ya tashi ya ciro waya daga aljihunsa to ko ya kirata ne?tou idan kuma ya kirata tana tare da mahaifiyarta fa?idan sukasan tanada wayar salula a hannunta ansamu matsala wanan wayar ba karamin taimaka masa takeyi ba wajen magana da ita ta hanyar wanan wayar yake samun natsuwa,
tura kofar doctor yayi da sallama can kasa kasa,yana ganinsa ya ganesa ya fadada murmushinsa yace "barka da zuwa ranka ya dade"Mansoor ya jinjina masa kai ya nemi kujera ya zauna yace"nazo ne muje dakin gwaji cikin mintuna goma sha biyar nakeso ka cire k'odata guda daya ka dasawa waccen mara lafiyar batare da kowa yasan nine na bata ba,inason hakan ya zama sirri a tsakanina dakai likita"galala likita yayi yana kallon mansoor da yayi maganar babu wasa ko zolaya a cikin lamarinsa shiru yayi ya kasa magana Mansoor ne dan gidan Alhaji sulaiman Aliyu dan majalisar jiha yazo mikawa wadanan kucakan yan kauyen koda?"likita magana nakeyi maka inaso kayimun abun nan cikin sauri akwai abinda zani inyi ne"likita ya sauke ajiyar zuciya yace "Ranka ya dade sameer matawalle Amininnka yanzun yabar asibitin nan yaje don kawo million sittin din da zaayiwa baiwar Allahn nan aiki har mun tanadi kodar da zaasaka mata yanzun haka,kudi kawai ake jira"Mansour ya lumshe ido wata kaunar sameer yakeji a cikin zucuyarsa tabbas sameer Aminine na kwarai yasani ransa ne kawai sameer bazai iya sadaukar masa amma bayaso ya kashe kudinsa yanaso ya mallakawa mahaifiyar Dina koda ne tsakaninsa da Allah saboda girman kaunar da yakeyi mata,likita "muje ka cire kodar jikina banaso sameer ya kawo kudin nan ya bannatar da kudinsa"
"yallabai dagaske kakeyi kodarka zaka cire ka mallakawa wad'anan kauyawan?"wani kallo mansoor yayi masa wanda yasa ya tsuke bakinsa ya mike yace muje,kwankwasa kofar akayi likita ya bude zasu fita sukayi kicibis da Dina turus tayi ganin mansoor tsaye a bayan likita,kallonta yakeyi cike da tausayawa itama shi take kallo sosai kayan jikinsa suka burgeta sai yanzun ta fahimci kayan dake jikinsa ta lumshe ido likita ya wuceta mansoor yace"lafiya na ganki haka meyafaru"girgiza kai tayi idonta ya kawo ruwa tace "dama nazo fadawa likita innahta ta farka ne amma cikin nata ke ciwo,yanxun haka tanacan tana murkususu"hankalin mansoor ya kara tashi yace"yanzun zaa shiga da ita bari insamu likita"ya wuceta mamakinsa ne ya kamata tayaya zaayi mata aiki bayan baaga zuwa babanta da kudi ba?tasa hannu ta share hawayenta,taji mansoor ya kara shiga ranta bata taba sanin mutumin kirki bane sai da abubuwa ke faruwa dasu illarsa wanan shaye shayen ga mahaifinta ya tsanesa bataga aibunsa ba.....
bayan awa daya aka fito da innahr Dina daga dakin operation nurses suka gungurota suka kaita daki da sauri Dina ta tarbesu "innahta innah ki tashi ki farka insha Allahu kin samu lafiya kingama kinji?"tana maganar tana hawaye tana kuma shafa goshin innahrta cike da tausayawa,da sauri ta fito ta shiga dakin likita a tunaninta mansoor na ciki likita kadai ta gani a zaune yana rubuce rubuce tace "likita..... yanzun gashi anyi mata aikin baku jira tukunna an kawo kudin ba babana ya tafi kauye ne ya siyarda gidanmu ko kudin zaiyi"dariya taso bawa likita tayaya zai siyarda gida a kauye yakai million sittin kudin dashen koda?wajen zama ya nuna mata,a d'arare ts zauna "ansamu wani bawan Allah wanda yace kada a fadi sunansa ya bada kodarsa guda daya ansakawa mahaifiyarki"zumbur ta mike ta dafe kirjinta tace "wani bawan Allah?a ina? wayeshi da zai dauki kyautar koda Rabin rayuwarsa ya bamu? mai muka hada dashi?likita ka fadamun gaskiya wayene ya bawa innahta kyautar koda kafadamun ko wayeshi sujada ne kadai bazanyi masa ba likita dan nasan be halarta ba amma daya halarta shi din ma da nayi masa,waye ya sadaukar da rayuwarsa Dan ganin rayuwata ta inganta?"tana maganar hawaye na zuba a idanuwanta, tausayinta ne ya kama likita tabbas ya cancanci a fada mata Mansour ne ya bada kodarsa ga mahaifiyarta amma gudun sanin hali irin na mansoor yasa ya tsuke bakinsa,dakyar taja kafarta ta fito daga dakin likita tayi kicibis da sameer hannunsa dauke da basket na kayan abinci wasu kuloli ne na alfarma,
ganin tana kuka yasa yace "lafiya?kidaina kuka jikin nata ya matsa ko?nasamu baba a company ne yasa hannu a bani kudin nazo mu biya"
"ai anyi mata aikin"
"anyi mata?kudin ya rage kenan a biya?"ta girgiza kai tana share hawaye take fada masa abinda likita ya fada mata,
wata irin faduwar gaba ce ta ziyarci Sameer ya dire basket din dake hannunsa jikinsa na rawa cikin zucuyatsa cike da furgici yace kardai mansoor ne yasa aka cire masa koda aka dasawa mahaifiyar Dina?.....a kidime ya dubeta "ina Mansour?yazo asibitin nan?"ta gyada masa kai tace "ehh yazo amma bansan tafiyarsa ba nima inason ganinsa muyi magana amma ban gansa ba"ajiyar zucuya yayi cikin zucuyarsa yace tabdijan lallai mansoor cikin mamaki tace "yadai akwai wata matsala ne?"girgiza mata kai kawai yayi yana jifanta da wani kallo wanda yau ya fara yi mata hakan kuma tsarguwa takeyi,
"ya tafi bangansa ba Dan Allah ka kiramun shi ya dawo ina bukatarsa"ta marairaice murya yana kallon soyayyar mansoor karara da damuwa dashi a cikin kwayar idonta,gudun kada ta fahimci wani abu yasa ya fadada murmushinsa yace "Dina na fahimci kin kamu dayawa ko?"batasan lokacin data jinjina masa kai ba,sanan ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana dariya suka jera zuwa dakin da innahrta take....