← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 36

Sashe 2

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"a gayas"DINA tace tana binsa da harara,murmushi man yayi kawai ya juyo idonsa da nata suka hadu wani yarrrrr Dina taji tayi saurin dauke idonta cikin zucuyarta tace Allah yasa beji ba......
********
"momy tun safe nake kiran ya mansoor baya daukar wayata bansan meyasa ba"cike da shagwaba matashiyar budurwar ke magana tana kallon momy idonta yayi rau rau,
"tou ke ya nabeeha inda sabo ai kin saba da miskilancin ya mansoor meyasa kikeso kidamu kanki kinsan yanayin abu lokacin da yakeso kuma ya gadama ne ni narasa gane kan wanan abun naku"

"bazaki gane ba rufaida ni bansan meyake zuwayi wanan kauyen ba ma nafara suspecting dun wani abu"tayi maganar a kufule cike da kishi sai lokacin momy ta yi magana "nabeeha kinfi kowa sanin mansoor ai karma ki tunanin akan mace yake zuwa wanan wajen raayinsa ne nima banida yadda zanyi kuma shi yasan bazai dauko mun wata yar kauye ya kawo ba"..

rufaida tadan ja tsaki tace "a birni ma beso mata ba sai a kauye?dama kincire wanan a ranki kawai kiyi kokarin samun soyayyarsa kawai in kinada saa"rufaida na maganar ne tana kokarin saka kayan bacci tana daure da towel momy ta yunkura tace "da nasan abinda kika kirani kicemun kenan da banzo ba wallahi keda mansoor bazan iya da fitinarku ba"momy na maganar tana kokarin fita cike da tausayn nabeeha,

kara dialling wayarsa tayi a karo na ba adadi,

yana kwance ya kishingida yana kallon kiran nabeeha na shigowa ko motsi beyi ba balle asa ran zai dauka sam dake gefensa yace "baka ganin kiran nabeeha ne?ka dauka mana kaji me zatace"

mamsoor ya kallesa ta gefeb ido yace "amma kasan DINA dazun tabani mamaki?"samir yayi murmushi yace "mamakin me ta baka abokina?"shiru yayi bece komiba ya lumshe idonsa kawai kwayar idonta yake gani masu zara zaran gashi da yalwar gashin gira,sanan amon sautin muryarta tana zaginsa keyi masa yawo samir ya cigaba da danna laptop dinsa har ya manta da suna magana yaci mansoor yace "tanada courage sosai....babu macen data taba kallon tsabar idona ta fadamun magana sai ita"murmushi samir yayi yace "toh fa to kayi mata magana mana?nima inaso ku sasanta ko saboda....."sai kuma yayi shiru be karasa ba ya cije lebensa yana cigaba da danna laptop dinsa,

"dawa zamu sasanta?ni?hmmm lets see"kawai yace ya dauko wayarsa dake cigaba da ruri ransa a bace yace "owoooo nabeeha why?you are disturbing my peace"ya dau wayar a fusace yace "i dont want to talk"
ta sauke ajiyar zucuya tace "why?"zucuyarta na cigaba da azalzalar ta da tsananin kaunarsa yace "later"kawai ta kashe wayat gaba daya yayi jifa da wayar ya janyo bargo ya lullube kansa ya lumshe ido DINA yake gani kawai dariyarta da fararen hakoranta,idonsa a lunshe yake murmushi,...
******
DINA na zaune a gaban mahaifinta bayan innah ta gama labarta masa komi daya faru yau ta dora da "kaja ma yarinyar nan kunne kada ta daukar mana abun kunya a garin nan dan dik garin nan maganarta akeyi ni banason alakartq da yan birni"

mahaifin dina yayi murmushi yana kallon dina yace"kinji abinda innahrki tace ko?nima ina wajen gyaran facin taya aka fadamun abinda ya faru anga lokacin daya zabga miki maruka ya biki aguje DINA ki rufamun asiri idan daukar magana zaki aurar dake zanyi"da sauri ta zabura tace "haba baba ka manta kace zaka kaini birni inyi karatu?ka manta likita nakeson zama?"mahaifinta ya daura fuska yace "tou indai kinason zama likita kada na sake ganinki da wadanan yaran yan birni kinji na fada miki ko?idan nasake ganinki dasu aure zanyi miki kuma bazaki karatun likitancin ba"sosai Dina ta tsorata ta gyadawa mahaifinta kai "bazan sake zuwa wajensu ba"

"dakyau tashi kije ki kwanta dare yayi"mahaifinta ya bata umarni,ta mike ta kwashe kwanukan da sukaci abinci sanan ta Shiga dan dakin dage gefen na innahrta ta rufo kofar,
ta jingina da jikin kofar tace "yanzun ya zanyi da abokina samir mai kirki?gashi baba ya hanani muamala dasu"zuciyarta babu dadi tayi rau rau da ido tad'anyi tsaki tace"gashi inada kudirin ramuwar gayya akan wancen dan wiwin yanzun ya zanyi?bazai mareni yaci bulus ba"ta shiga safa da marwa a cikin dakin tana tunani yadda zaayi ta dauki fansa akan mansoor....murmushin mugunta tayi take tace "yauwa nasamo mafita bazan taba barinka haka ba"tayi tsalle ta fada yar katifarta tana dariyar mugunta......

*SLIMZY*✍🏻
[08/11, 12:04] 😍Slim girl❤️: 💥 *MAZA BIYU....*💦

*NA:SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33

*Marubuciyar:*

*K'ADANGARUWA*🦎

*RUD'ANI*💥

*DUHU...*🌑

*2*
washe gari,
Innah na zaune akan tabarma ta kunna radiyo baban Dina na zaune a gefenta yana gyara jakarsa zai fita yace "ina Dina?ko har yanzun bata tashi ba tana kwance tana sakarci?"innah ta girgixa kai tace "natasheta sallahr asuba dai amma banida tabbacin ta tashi tayi sallahr yanzun nake shirin daukar bulala na shiga na tasota"bata rufe baki ba Dina ta fito tana Mika hade da salati wani kallo baba yayi mata yasa ta katse hammarta ta durkusa a gabansa "ina kwana baba katashi lafiya?ina kwana innah?"kusan hada baki sukayi "kinyi sallah ne?"ta jinjina kai "ehh nayi sallah"tace gabanta na faduwa alhalin batayiba fashin sallah takeyi kunyar ta fadawa innah takeyi,"dakyau dama ke nake jira na gargadeki kafin na fita kar inji kinje wajen yan birnin nan kin nemesu fada kinji na fada miki ko su sakaki a mota su gudu dake bamu saniba"murmushi Dina tayi tace cikin ranta "ai saidai su koma a kafarsu dan badai da wanan motar tasu ba badai akanta dan jiji da kan nan ke hura hanci ba kamar wani basarake"baba ya daka mata tsawa ganin tayi shiru tana murmushi yace "ke murmushin me kikeyi?"ta girgiza kai a tsorace "wani abun dariya na tuna,Allah ya tsare ya bada saa"tacewa mahaifinta ganin yana kokayim zura takalminsa tun sassafe yake fita daga kauyen yaje bakin hanya gyaran tayar mota,bayan fitarsa ta zauna a gefen innah ta soma zuba mata hirarta mara kan gado cikin hirar harda labarin sameer take ba innahrta wadda gaba daya batasan ina ta dosa ba,

minti kadan kamar an tsikareta ta mike "innah zani gidan su lubabatu na dubota kinga idan Rana tayi bazan iya zuwa ba"shiru innah tayi tana karantar DINA ganin ta zuba mata manyan idanuwanta yasa ta gyada mata kai "kiyi sauri kada kidade kuma karki biya wajen wadanan mutanen"ta jinjina mata kai tana murmushi,

mansoor kasa sukuni yayi haka kawai yakeson ya fita zaga gari ko zaiga mara kunyar daya dauki dammarar koya mata hankali dan haka Sameer na bacci ya dauki wayarsa yasa ear pice kunne daya,yana sanye da wasu kayan sanyi masu ruwan toka kansa babu hula yabi cikin garin yana tafiya yana haduwa da almajirai yana basu sadakar kudi dik wanda ya gaishesa saidai ya daga musu hannu yayi musu murmushi,DINA ya hango ta bullo ta wani lungu tana tafe tana rera waka da zazzakar muryarta tsaki yayi yace "shashasha tana tafe tana waka kamar ba mace ba"yad'anyi tsaki ya makale a jikin bango tazo ta wuce,wani iri. faduwar gaba taji da sauri ta juya babu kowa sai wani irin kamshin turare takeji wanda ta rasa a ina ta taba jinsa,jim kadan tayi a cikin lungun tana waige waige yana kallonta da narkakkun idonsa gashin kansa yasha gyara sai walkiya yakeyi tayi tsaki "sauri nakeyi kafin su tashi subar garin nan in rama abinda nayi niyya yau saidai mutum ya koma birni a kafa"tayi maganar tana kwafa,ransa yadan sosu yasan dashi take ya danne zucuyarsa kada ta gansa yabi bayanta tana tafe yana biye da ita wayarsa ya fito da ita ya danna recording da video tana wakar sarmadan ya masoyi sarmadan sarmadan....tsaki yayi yace "village girl baki sai rashin kunya"ya girgiza kai har suka isa kofar katafaren gidan gonar mahaifinsa ya makale a jikin gate,tana waige waige babu kowa a wajen sai kukan tsuntsaye dake bishiyoyin dake cikin gidan ta daga kanta tana kallon bishiyoyin cike da tsiwa tace "ni tsorom wanan bishiyoyin nake da wadanan tsuntsayen masu kukan tsiya"da sauri ta cire abun iskar tayar motarsu duka hudun tana cikin cire na karshe ta gagara cirewa tayi gumi kawai taga mutum tsugunne a gefenta,damm gabanta ya yanke ya fadi ta dago ido nan da nan jikinta ya soma kyarma tana kokarin mikewa ya cafki hannunta "Dan Allah kayi hakuri kaji karka fadawa innah ta kada ka kasheni kaji zan gyara muku tayarmu na iya wallahi"sosai tabashi dariya yadda jikinta ke rawa yasan tsananin tsoro take ciki da furgici,cije lebensa yayi hade da sakin murmushin gefen fuska yace "let me help you and removed it"kallonsa take bata gane meyace ba sai gumi dake karyo mata,

"kace?"ya girgiza kai yace "wawuya batajin turanci"tadan tura baki tace "niba wawuya bace"a ciki yace "me kikace"girgiza masa kai ta shigayi tana kokarin kwace hannunta daga rukon da yayi mata ko motsa hannunsa ta gagarayi,

sameer ne zaune gefen gado ya shirya tsaf yana kiran wayar mansoor bata shiga tsaki yayi "ina kuma man ya shiga?inaso na fita na nemi DINA kafin mubar garin nan amma ya kama ya fita ina kiransa baya Shiga"

ya sake kiran wayar cikin saa ta shiga yana rike da hannunta ya kafeta da ido waya ta shigo wayarsa yace "yauwa ina tunanin hukuncin da zanyi miki ne ga abokinki ya kira"fuskarsa a daure yayi maganar take hantar cikinta ta kad'a cikin seconds hawaye suka shiga zubowa daga idonta yasa hannu ya dangwalo hawayen yayi murmushi sanan ya danna recieve yace "yes i can hear you"

"kana ina ne haka?natashi tun dazun na shirya inaso na shiga cikin gari sanan mu wuce ban ganka ba ya kamata mubar garin nan da wuri ana jirana ne nasa hannu a wata takadda a kamfani"harshensa ne ya sarke ganin yadda ta jike da gumi har zai fadawa Sameer yana tare da DINA sai kuma ya fasa still idonsa na kanta bayaso sameer yayi wani tunani,bayajin zai iya fada masa cewar ita ya fita nema bawai dan yanajin wani abu akanta ba "kadan jirani ganinan zuwa"be jira mezaice ba ya katse wayar,

tsaki samir yaja ya kalli agogo ya dafe kansa "bazan tafi ban hadu dake ba kawata kodan in kara baki hakuri akan abinda man yayi miki"cikin takaici yace....."ko ina yayi oho mtswww"yaja tsaki,
Chapter 2 · 0% Book details