← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 36

Sashe 22

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sameer na jingine jikin mota sanye da farar shadda kansa babu hula hannunsa rike da waya a kunnensa Mansoor ne,cikin damuwa mansoor yace"sameer narasa meyasa zuciyata take rawa,tunanina yake tsayawa cak ba,hankalina ya gaza kwanciya tun daren jiya,dana kwanta bacci sai mafarke mafarken Dina nakeyi, please me kake boyemun kacemun da sassafe zakaje kauyen nan ka dubomin ita kaga wani hali take ciki amma na kiraka sau biyu a na uku ka dauki wayata,karka boyemun komi wani hali Dina take ciki?"Yana maganar ne muryar mansoor tana rawa gabaki daya sautin muryarsa yasa jikin Sameer yin sanyi kalamansa sun karyar masa da zuciya saidai bayajin zai fasa kudirinsa na auren Dina,dikda irin son da yakeyiwa Aminin nasa yasan yadda mansoor ya damu da Dina sosai amma yasan Dina bata dace da mansoor ba dashi ta dace dikda kasancewarsa amininsa,lumshe idonsa yayi ya bude ya nisa yace "calm down man ina kauyen yanzun haka maganar da mukeyi dakai nasa a bincikomin Dina din ne kasan mahaifinta bayason muamalarku da ita so banaso kowa yasan nazo balle a fada masa anganmu da ita"ajiyar zucuya Mansoor ya sauke a sanyaye yace "it's okay don't hide anything for me idan kun hadu da ita kaji?na nemi wayarta tun jiya shiru nasan mahaifinta zai iya kwance wayarta saboda ni idan har ya kamata dashi please ka kirani ka hadani da ita idan babu waya a hannunta kuma ka siya mata wata Dan Allah baxan iya abinda najeyi ba sam idan har banji muryar Dina ba kasani she's my peace of mind"sameer ya lumshe idonsa bugun zucuyarsa ne ya tsananta ganin mahaifin Dina a kusa yasa ya katse wayar ba tare da yace komiba,yaja gauron numfashi ya sauke cikin zuciyarsa yace "sorry friend.....Dina ta koma tawa"ya durkusa ya gaida baban Dina sanan ya mike suna fuskantar juna,baba yace "Sameer inajin tsoro kada kuyimun angulu da kan zabo"

"Baba ban fahimceka ba kafadamun mai maganarka take nufi "yayi maganar yana sosa keya,shiru mahaifin Dina yayi sanan yace "tou ina tunanin kar Mansoor ya turo ka ka aurar masa Dina tunda yasan nace bazan bashi ita ba"sameer yayi murmushi ya girgiza kai yace "ko daya baba nine kawai nakeda muradin hakan,inaso na cika maka burinka na cika burin Dina wajen inganta rayuwarta da karatu kamar yadda kakeso"baban Dina farin ciki ne ya lullubesa ya gyada kai yace "na baka Dina"ya juya kawai wajen mahaifin sameer sukai magana suka kama hanyar masallacin garin dan gudanar da sallahr jumaa da daura auren Dina da sameer.....

Dina tagumi ta rafka cikin tashin hankaki tace "kace kanata kiran wayarsa yana shiga amma yana waya ko?"ya jinjina mata kai yace "ehh waya yaketayi be dauka ba daga baya ma yanzun wayar bata shiga Dina,amma kibar layin a wurina idan ya kira zan sanar masa da kece kikeson magana dahi inyaso sai kizo ko anjima daddarene kuyi Magana "Dina tayi shiru cikin faduwar gaba ta kasa magana, tayaya zatazo bayan yau mahaifinta yayi alkawarin aurar da ita ga mai kayan miya idan ya kira lokacin kuma lokaci ya kure fa?ta juyo ta marairaice murya tace "idan ya kira kasamu yaro kawai yazo gidan mu ya fadamun zan fito kota wani hali muyi magana"ya jinjina mata kai yace "Dina kenan yar innah"yana dariya ta wuce zucuyarta cunkushe da tsananin takaici,

mansoor ya tasa takadda a gabansa gefensa wasu turawa ne da suke tattaunawa gabaki daya hankakinsa baya jikinsa dik maganar da sukeyi masa ya dafe kansa,meyasa Sameer ya sauya masa?ya kasa fada masa gaskiyar meke faruwa?tou kodai beje kauyen bane yayi masa karya?girgiza kai yayi yace "kai sameer bazai mun karya ba"ya dauki wayarsa ya dubi daya daga cikinsu yace "excuse"furkarsa ya daure idanuwansa jajir ya koma can gefe ya tsaya ya bude wayarsa misscalls goma ya gani,nan da nan bugun zucuyarsa ya sauya yana danna wayar dan ganin waye jikinsa na rawa yana gani jikinsa ya soma rawa kamar mazari yace "Dina....why meyasa sai yanzun kike kirana?kin wahalarmun da zucuyata? Insta tunanin halin da kike ciki"ya gyada kai yayi murmushi yace "nasan kila sun hadu da Sameer ne"yana murmushi yaja ajiyar zucuya yayi dialing,bugu daya aka dauka gabansa ne ya yanke ya fadi jin muryar namiji yayi shiru ya kasa magana wani jiri ne yake neman daukarsa,ya dake yayi gyaran murya yace. cike da isa da izza yace "ba mai wayar wayarta"shafiu yace "ai mai layin dai nine mai wayar Dina ce"bakinsa har rawa yakeyi yace "ina take?ina wayar tata?kace mai layin?"shafiu yace "ehh layi ta kawomin tace nasa mata kuyi magana munata kiranka kuma baka dauka ba shine ta tafi gida"ji yayi kamar ya caka masa wuka a kahon zucuya,nan da nan idanuwansa ke neman rufewa da duhu ,a sanyaye yace "ya zaayi inyi magana da ita?ka taimakeni zan baka dubu dari ka hadani da ita Dan Allah"

"tayaya zaka ganni kabani dubu dari malam banason karya ban taba rike dubu goma bama ballantana dubu dari" Mansoor yace "look zan baka wallahi zansa har inda kake a kawo maka matukar zaka hadani da Dina muyi magana"shafiu ya washe baki yace "Angama zan aika yanzun a kirata"ya kashe wayat wata ajiyar zucuya mansoor yayi sai lokacin ya samu sassaucin yadda yakejin faduwar gaba wanda besan dalilin hakan ba....

********
khairatu na kwance ta kifa cikinta wasu hawaye masu d'umi kebi ta gefen idanuwanta yayinda kanta ke wani irin sara mata wanda ya haddasawa idanuwanta yin nauyi ta kasa budesu saidai hannunta daya na rike da wayarta wadda taketa trying number sameer tun safe bata samu,turo kofar dakin akayi da karfi wanda ya haddasa mata tsananin tashin hankali da furgicin da take ciki mai tsanani ta bude idonta tana kallon ummahnta wadda ta harde hannuwanta a kirjinta tana kallonta cike da damuwa da tashin hankaki,ganin yanayin ummah yasa khairatu saurin mikewa ta zauna tana kokarin saita natsuwarta cike da tsoron kar ummah taga lokacin da mai gadi ya kawo mata abun awon ciki,

"Khairatu kardai abinda aka sanar mun a waya ne kema kikaji ya haddasa miki wanan tashim hankalin?"damm gaban khairatu ya yanke ya fadi cikin zucuyarta tace dik girman tashin hankalin da kike ciki be kai wanda zakiji daga gareniba ummah idan har kikasan ina dauke da cikin sameer matawalle wanda ake gab da yi mana baiko dashi,

"kinyimun shiru bakice komi ba khairatu,ko bazakice wani abuba nasam wata damuwar tana haddasawa harshe kasa motsi ballantana ya furta abinda ke cikin zucuya,nasan kinada labarin wai sameer sunje an daura masa aure yanzun nan da wata?"damm gaban khairatu ya yanke ya fadi wanan kalmar ce ta haddasa mata wani irin mummunan hankali wanda yasa zucuyarta ta tsaya cak yayinda numfashinta yake kai komo daga kirjinta zuwa cikinta wanda hakan ya haddasa mata wani irin gumi da ya soma karyo mata,

bakinta na rawa ta soma magana "ummah dagaske sameer aure yayi?ya auri wata ne ya dawo ya aureni ko kuma ya aureta ne ni ya watsar da tawa soyayyar"hawaye ya soma zubowa daga cikin idanuwanta kamar am bude famfo,

"yanzun nakira hajiya zinariyar matawalle(mahaifiyar Sameer)nake tambayarta akan maganar zuwan nasu dikda abun dik na gida ne amma ya kamata na sanarwa da kannen mahaifinki shine take sanar mun akam muyi hakuri dama zatazo akan wata magana,na nemi ta sanar mun abinda yake faruwa shine take fadamun yanzun haka sun tafi nema masa auren wata yarinya daga can aka daura auren zasu taho da ita ma"dafe kirji khairatu tayi ta koma da baya ta fadi jagwab akam gado cikin mummunan tashin hankali tayaya zata fuskanci iyayenta da nasa ta sanar musu da cewar tana dauke da juna biyu na sameer?wanda shine ya bukacu ta boye soyayyarsu kada su sani sai ya nemi aurenta? tayaya zasu yarda da hakan?"

zama ummah tayi gefen gado ta dafa kafadarta cike da takaici tace "nasan ciwon abinda kikeji khairatu akan sameer,nadade da sanin kina sonsa dan nasan hakan a kwayar idonki dik zuwan da yakeyi gidan nan kika boyemun dikda be furta yana sonki ba amma ke kina sonsa,dan haka ki kwantar da hankalinki dik wata hanya da zanbi sainabi wajen ganin kin shiga gidan daular matawalle kota wani hali kuwa"khairatu ta kalli mahaifiyarta da jajayen idonta ta gyada mata kai kawai ita kadai tasan masifar da take ciki,ummah ta mike tace "yanzun zan shirya zan nufi gidan su kafin nan gidan Antynku zan fara zuwa sanan muje gidan wajen tarbar amarya Inga wace kalar amarya ce wadda tafi tawa yar? Asali kyau koko dangantaka?"kuka kawai khairatu takeyi cikin tashim hankali ta koma ta kwanta wani zazzabi ne mai zafi ya lullubeta idanuwanta sukai mata nauyi......

********
Gidansu Dina cike yake da jamaa ganin komi takeyi kamar a mafarki yadda gari ya dauka Dina tayi aure a birni tana jingine da bangon dakin mahaifiyarta ta lunshe idanuwanta,ko mansoor ya kira shafiu mai shago oho?cikin tsananin mamaki ta kara duban mahaifiyarta tacev"innah nakasa yadda akan cewa aure zanyi kuma a birni dikda kunki sanar mun da wanda zan aura mai hakan yake nufi?"dafa kafadarta innahrta tayi tana murmushi "zakiso wanda zaki aura Dina nasani tunda dama kuna son junanku"lumshe ido Dina tayi ta bude tace "innah munason juna kuma?waye haka wanda muke som juna yazo da maganar aurena lokaci daya?"tana kallon innahrta cike da rudani zucuyarta na wani irin bugawa tou kodai Mansoor dinta ne ya turo a aura masa ita kafin ya dawo daga kasar waje?tou idan mansoor ne mahaifinta zai amince da auransa bayan yana ikirarin cewar mashayi ne?irin tsanar da mahaifinta yayiwa mansoor batajin zai Amince da aurensa lokaci daya,

shiru Dina tayi gabanta na tsananin faduwa innah ta dubi kanwarta baba lubabatu da baba kulu tace "muje daga waje mu tattauna wadanda zasu raka Dina din tunda sunce tarw da ita zasu tafi basa bukatar komi"

baba kulu ta tabe baki tace "kundai siyar da yarku kawai a birni hankalinku ya kwanta shiyasa kuka kulla abinda taki auren tasiu niban yarda cewa yau ne akazo da batun auren Dina ba wallahi koma menene zai kare muku keda mijin naki"innah murmushi kawai tayi ta fita,
Chapter 22 · 0% Book details