Sashe 20
Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mansoor kallon sameer yakeyi gabaki daya yanayinsa ya canja daga shekaran jiya zuwa yau ya rasa menene matsalarsa kamar akwai abinda yake boye masa,sameer ajiyar zuciya ya sauke yace "am gonna miss you friend "mansoor ya jinjina kai "nasani kaima kasan zanyi kewarka sosai na zabi tafiyar nan ne a wanan lokacin yadda dana dawo zan san matakin da zan dauka wajen ganin na ingata rayuwar Dina"sameer ya dafa kafadarsa "haka kayi nisa akan soyayyar Dina?lallai kayi zurfi man a tsananin kaunarta tunda ka dauki Rabin rayuwarka ka mika musu dikda irin tsanar da mahaifinta yayi maka"mansoor murmushi yayi yace "well i dont care da tsanar da yayimun tunda nasan na kafa soyayyata da kulawata a cikim zucuyarta ai shikenan,babban farin cikina be wuce yadda wancen dan kauyen ya janye daga maganar aurenta ba komi zaizo mun da sauki nayi mata alkawura kala kala a daren jiya muna waya da ita wanda dana dawo zam cika mata shi kota wani hali"sameer tsura masa ido yayi kawai yana gyad'a kai yace "good luck inaso naje nasamu daddy a company yana jirana sanan akwai maganar da nakeso muyi dashi mai muhimmanci"rungume juna sukayi mansoor na bubbuga bayan sameer cikin sigar lallashi ya rada masa a kunne "i can see you are already missing me"sukayi sallama sameer ya juya ya shiga motarsa mansoor na daga masa hannu har ya bar cikin Airport din,
a reception mansoor ya zauna kusa da wata budurwa wadda tun shigowarsa ta ganesa shi be ganeta ba hakan ya bata damar kawar da kanta gefe guda bugun zucuyatta ne ya tsananta ta lumshe ido cikin zucuyarta tace "tarko na ya d'anu a daidai tare zamu tagi cyprus dakai mamsoor bazaka taba barina kasha a banza ba sainasan yadda nayi nashiga rayuwarka ka koma shaye shaye wanda inada labarin sanadin daina shaye shayenka wata yar kauye ce,kafin ka dawo ka mance da ita"wayarsa ya ciro daga aljihunsa ya shiga hoton Dina ya fito dashi wanda yayi mata da kayan fulani bakin nan yasha jan baki jajir kamar zai d'igo yayi murmushi ya shafa fuskarta a screen din wayar yace"bansan yadda zanyiba da rashinki peace of mind banso wanan tafiyat tazo a wanan lokacin da nake tsaka da bukatarki ba"tunanin kiranta yakeyi a wanan lokacin yasan likita ya sanat masa da an sallamesu tunda safe to ko suna gida?tambayar da yayiwa kansa kenan ya kwantar da kansa a jikin kujerar da yake zaune ya lumshe idonsa,
"Dina lafiyanki?tun dawowar mu daga Asibitin nan nake ganinki kamar bakida lafiya"cikin taushin murya innahrta ke tambayarta tana daga kwance,
tsaki kakarta baba kulu tayi tace "lafiyanta kalau mana akwai abinda ke damunta banda ya wuce tunanin yan birnin can?nifa nafara zargin wani abu akan wanan yarinyar dan hatsabibiya ce ban yarda cewar wani bane ya baku kyautar kodat da aka sa muku kila wadanan yan birnin ne sun samu abinda sukeso suka biya muku kudin aikin"innah cikin rashin fahimta tace "kamar yaya sun samu abinda sukeso?"
"ya wuce sun gama lalata da ita?"innah ta dafe kai taji takaicin wanan kalmar data fito daga bakin baba kulu da badan mahaifiyarta bace da babu abinda zai rabasu yau sai Allah, innah ranta ya bacu ta juya ta kalli Dina wadda ta rafka tagumi batasan ma me sukeyi ba hankalinta baya kansu,hamdala tayi da Dina batajiba tasan zataui bakin ciki kuma bazata kyale baba kulu ba,
vibration wayar Dina ta somayi ta zabura da sauri innah tace "ke lafiya?"wani miyau ta hadiya jikinta na rawa tace "kamar cinnaka ne ya cijeni innah Bari in duba ta fada dakinta ra bugo kofa da sauri jikinta na rawa ta ciro wayarta,
"yaya man...."tace a sanyaye cikin siririyar murya data daki zucuyatsa yaci wani sanyi a cikin ransa yacev"ashe zan sameki nadauka kina tare dasu innah inata tunani gashi inaso naji muryarki kafin na shiga cikin jirgi"
"jirgi?"tace tana dafe kirji cike da mamaki ya jinjina kai yana dariya kamar tana ganinsa yace"ehh wanda kike gani a sama din nan?"ta kwashe da dariya tace "haba kai zanso in ganni cikin jirgi zani Makka"dariya sosai ya hauyi maganarta cike da wawta yace "ke ba dik wanda zai aureki zaisha fama da wawtarki da dramer"ta lumshe ido ta turo baki tace "ba kai zaka aureni ba"wata faduwar gaba yaji be taba tunanin Dina zata fada masa wanan maganar ba ,shiru yayi batare da yayi magana ba tace "yi hakuri tunda ka fasa auren nawa"tayi maganar muryarta na rawa kamar zatayi kuka,jin haka yasashi sarkewa yace "sorry Dina zan aureki nina isa ince bazan aurekiba?"ta share hawayenta tace "ya man bazan iya auren wani ba idan ba kaiba,kaga idan mukayi aure sai mu cigaba da abotarmu babu mai rabamu ko?"murmushi yayi fararen hakoransa suka fito ya fahimci maganarta bataso tayi aure su rabu su daina abota hakan yasa ta yanke hukuncin aurensa badan tasan meye aure ke nufi ba,
sanarwa aka somayiwa matafiya masu shiga cikin jirgi,ya cije lebensa yacev"Zan shiga cikin jirgi Dina ki zama kusa da wayarki koda yaushe yin waya dake shine zai samun kwarin gwiwar yin dik abinda zanyi har nadawo gareki sanan karki Bari kowa yasan kinada waya kinji?idan banjiki ba komi zai iya faruwa dani"ya kashe wayar ,ya mike yaja akwatinsa,
bin wayar tayi da kallo haka kawai jikinta yayi sanyi ta kasa koda kwakkwaran motsi ta lumshe idonta tace "ina sonka yaya man....."mari taji an sauke mata,da sauri ta bude idonta suka hada ido da mahaifinta dake tsaye akanta Yana kallon wayarta,gabaki daya sandarewa Dina tayi tai mutuwar zaune cikin tsananin tashin hankali da rudewa ta cillar da wayar gefe ta tarwatse a wajen baba yace "sannu Dina.....lallai wuyanki yayi kwari Dina kuma yaron nan ya cuceni ya cuci rayuwata wato har wayar salula ya siya miki?"ta girgiza kai bakinta na rawa a kidime tace "bashi bane ba yaya man bane "ya kara sauke mata mari yace "idan har kika Kara cemun bashi bane saina fasa miki baki "innah ce ta mike ta lallabo ta shiga dakin ta samesu,
"lafiya malam? yaushe ka shigo?"
"nashigo tun dazun nazi da cefane ta bayan gida na biyo kawai nakejin magana ta cikin dakin Dina gabaki daya na tsorata yasa na dauke kafata dan insan meke faruwa a dakin nata ko barayi ne kwatsam ina shigowa na bude kofar batasaniba tayi nisa wajen yin wayar salula"
"wayar salula?"innah ta dafe kirji tace "waye yabaki wayar salula Dina?"
baba ya karbe "wancen Dan iskan yaron mashayi mana?har tana fada masa shi zata aura dan su cigaba da Abotarsu?dan tasan idan ta auri wani bazasuyi abota ba?tou ko zaki mutu bazaki auresa ba bari kiji koda tasiu ya fasa aurenki ina muawiyya wanda yake sonki da aure gobe goben nan idan an sauko masallacin jumaa zaa daura aurenki dashi"ya duka ya dauki wayar ya hada ya zura a aljihunsa ya fita cike da takaici sabuwar tsanar mansoor ce ta kara darsuwa a cikin zucuyarsa,
"Dina baki kyautawa kanki ba ga abinda kika jawowa kanki nan ai"ta juya ta barta nan durkushe dafe da kumatunta hawaye na zuba a idanuwanta ta dora hannunta akai tace "shikenan nashiga uku dik wani mafarkina da nakeyi na ganin yaya man ya zama nawa ya kare kenan?shikenan bazanyi karatu ba haka zan kare rayuwata?"ta fad'a kan katifarta hawaye masu zafi ne suka soma zubowa daga idanuwanta nan da nan idanuwanta suka rufe wani irin zazzabi ne mai zafi ya lullubeta ta soma rawar sanyi tunsnin yadda zaayi tayi magana da mansoor takeyi gashi bata haddace number wayarsa ba,tayaya zatayi taga sameer ta sanar masa da halin da take ciki?bazata taba iya zama cikin kauyen nan batare da yaya man ba,ya zatayi da kaunarsa data daskare a cikin zucuyatta tayi Mata riga da wando da mayafi?jikinta ne ya soma karkarwa,aure?ita da wani a cikin kauyen nan bazata bari ta auri kowa ba idan haka ne gara ta gudu ta mutu data auri wani ba Mansoor ba idan tayi aure bayanan taci Amanarsa.....
******
suna zaune da daddy da sameer a dining bayan sun dawo daga company suna cim abinci daddy ya dubi sameer yace"kace akwai maganar da kakeso kayi dani naga akwai magana a bakinka amma ka kasa fadamun kanada wani wanda ya fini ne sameer?"ajiye cokali sameer yayi gabansa na tsananin faduwa dikda yasam dik abinda yakeso a duniya Shi mahaifinsa yakeyi da mahaifiyarsa kasantuwar shine dansu daya tilo yasa kome yakeso sukeyi masa,shiru yayi ya kasa magana,
momynsa ce ta fito sanye da wani jan material mai flowers golden an mata dinkin doguwar riga ya karbi jikinta sosai yasha ason stones sai walkiya takeyi tace "yadai naganku haka Sameer? lafiya kanada damuwa ne?"shiru yayi ya kasa magana momy tace "kodai kaida khairatu ne kuka samu matsala?yanzun nan suka bar gidan nan da ummahnku hajara ai kagansu lokacin da zaka fita ko?meyafaru?akwa damuwa ne?"
gyada kai yayi daddy ya ruko hannunsa cikin sigar lallashi yace "nasan damuwarka bata wuce Amininka daya bar kasar ba ko?nasan da kasan da tafiyar nan tare zakuyi visa kutafi amma idan kaga bazaka iya zamaba ka shirya zan kira waya yanzun insa ayi maka visa ka bishi"sameer yaja ajiyar zucuya ya girgiza kai yace "daddy kayi hakuri aure nakeso nayi gobe goben nan"momy tace "aure?gobe goben nan kuma? shine dik ka Shiga damuwa wanan ai Mai sauki ne saina kira ummahn khairatu na sanar mata da su shirya komi gobe in ankai sadaki sai a daura kawai"girgiza kai yayi yace "momy ba khairatu zan aura ba akwai wadda zucuyata keson na aura bansamu damar hakan ba sai yanzun"zaro ido tayi cike da mamaki take kallonsa daddynsa ma kallonsa yakeyi "ehh daddy dama nasamu wanda idan har baku taimakamun na mallaketa ba zaku rasani"da sauri momy ta rukosa yana kokarin tashi daga kujerar dayake zaune "mu rasaka kuma?meyayi zafi da zamu rasaka sameer?ai zaka iya hadasu duka ka aura tunda Allah ya hore mana dukiyat yin hakan kuma hakan bazai taba zumuncin mu ba "girgixa kai yayi yace "aurenta nakeso nayi badan soyayyarta tayi karfi a zuciyata ba saidai kawai in mallaketa inkawota gidana,ku taimakamun inyi hakan idan har bansameta ba tou tabbas zan rasata"Ajiyar zucuya daddy ya sauke yace "yat wacece a garin nan a ina suke?waye mahaifinta?"