← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 36

Sashe 35

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

******
Mansoor mamaki ne ya kashesa gabansa sai faduwa yakeyi yana kallon tankamemen gate din dake kofar gidansu Dina,kofar gidan daya bari da falefale akayisa? gidan kasa da akayi masa yab'e da sumunti?murza idanuwansa yakeyi yana sake kallon bakin gate din yayinda wasu kauyawa ke zaune gefe akan benci sun zubo masa ido yana tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa tunani yakeyi kodai ba gidan bane?tou kodai sun tashi ne daga wanan gidan sun siyar?dakyar ya janyo kafarsa yana takawa jikinsa a sanyaye yace "Assalamu alaikum barkanku da war haka"yayiwa mutanen dake zaune a kofar gidan sallama,daya daga cikinsu ya ganesa yace "D'an birni yau kaine a gari mutumin Dina"wani farin ciki ne ya lullube mansoor jin sunan Dina wato har ansan shidin mutuminta ne?kenan Dina tana sonsa haka?gabansa be daina faduwa ba yayi murmushi,zaiyi magana yace "ya wajensu Dina?"yana maganar yana washe jajayen hakoransa mansoor yayi tsaye kamar an dasashi mamakin ya wajensu Dina kuma kafin ya tambayesa ya sake magana "ai mutumiyar taka nasan tanacan yanzu. ta canja ko?ai infada maka tou kodai bakada labarin Dina tayi aure ne?"yace yana murmushi ,mansoor take yaji wani abu mai kama da guduma ya daki tsakiyar kansa,nan da nan wata kibiya ta caki kirjinsa yayi baya da baya kamar zai fadi ya tsaya da kafafuwansa,jikinsa ne ya soma rawa kamar mazari yayinda zufa ke karyo masa ta ko wace gaba ta jikinsa kamar an kwara masa ruwa,cak yaji numfashinsa na kokarin tsayawa,ya rufe idonsa na seconds sanan ya bude tare da adduar Allah yasa mafarki yakeyi ba gaskiya ba,Allah yasa kunnensa beji masa daidai ba"yadai bawan Allah meyafaru?"suka hada baki suna tambayarsa ganin yadda jikinsa ke rawa yana tangal tangal,"ya ya ?kodai bakasan Dina tayi aure bane?ai Dina tayi aure sati uku zuwa hudu kenan"take mansoor ya durkushe a kasa idanuwansa yaji suna kokarin rufewa dakyar ya motsa labbansa ya bude idanuwansa dake rufewa suna budewa yace "tayi aure?tayi aurefa kace?kasan wace Dina nake magana?"murmushi sukayi suka hada baki "dik garin nan Dina guda daya ce kuma tayi aure wanan gidan da kake gani gidansu ne canjin rayuwa suka samu"

"Innahlillahi wainnahilaihi rajiun kawai mansoor ke maimaitawa can kasan makoshinsa domin maganarsa bata fita sosai besan lokacinda hawaye suka fara zubo masa ba,a karo na farko a rayuwarsa hawaye na zuba a idanuwansa?kuma akan mace?ya dafe kansa garin ke juya masa wata irin hajijiya ce ke kokarin kayar dashi,yasa hannunsa ya dafe kasa,kirjinsa keyi tamkat ana soka masa allura ,nan da nan ya soma ganin Duhu wanda idanuwansa ne suka rufe ya yanke jikinsa ya fadi a nan,da sauri suka karasa kansa "innahlillahi wainnahilaihi rajiun akawo ruwa"daya daga cikinsu ya Shiga bugun gate din gidansu Dina,mahaifiyarta ce ta bude yace "innahr Dina taimakemu da ruwa wancen ne ya suma"ta dan leka sanan ta koma cikin sauri ta dibo ruwa a dan jug na roba ta miko masa daidai an tallabo mansoor,tana tsaye tana lekensa idonta ne ya sauka akan mansoor wanda yasa ta waro ido tana kallonsa,tabbas ta ganesa wato wanan dan shaye shayen ne kenan?"ta tura kofar gida cike da furgici to meye ya kawosa kauye bayan abokinsa sameer ne ke auren Dina?har ya suma?tou kodai wani abu yasamu Dina ne?gabanta ya fadi jiki babu kwari ta zauna akan kujerar robar dake kofar dakinta ta jingina tana sauke nunfashi tana jiyo hayaniyar mutane,

cika sosai akayi kowa na leken dan birni wanda babu alamar rai a tattare dashi dikda wasu daga cikin jamaar sunce yana numfashi,daya daga cikinsu ne yace"mukaisa gidan gonarsu inaga zaifi tunda dama akwai masu kula da gidan gonar"suka daukesa suka nufi gidan gona dashi,

sameer ya fito ya shiga mota kenan ya zauna mansoor ya fado masa a rai tou kodai ya tafi kauyen ne?ya zaro wayarsa daga aljihunsa ya kamata ya kirasa yaji halin dayake ciki,jikinsa a sanyaye yasan tabbas akwai matsala,ya soma kiran layin wayarsa,har ta tsinke baa dauka ba gabansa ke tsananin faduwa ya soma kira a karo na biyu har ta kusa tsinkewa sanan sergent na gidan gona ya dauka "Hello sir"sameer hantar cikinsa ce ta kad'a a sarke muryarsa yace"ina man din?naji kamar sergent ka dauki wayarsa?"

"ehh sir muna hanyar shigowa gari dama dole zan kiraka domin gashi nan baisam inda kansa yakeba"sameer yace "what?meyafaru meyasames"

"tou ance wai yarinyar nan ce Dina tayi aure sir shi kuma yazo wajenta ne aka sanar masa shine ya fadi yanzun muna tahowa inaga ka kira gida ka sanar musu mu hadu a specialist hospital"sameer sandarewa yayi tausayin mansoor ne ya lullubesa tabbas yasan Amininsa ya kamu da tsananin son Dina yana kaunarta fiye da komi,shima kuma yanzun ya kamu da sonta Fiye da baya,sameer idanuwansa ne suka cicciko da hawaye yace "am sorry friend dik halin da kake ciki ka Shiga nine sila sakamakon aure Dina da nayi dan nima ina bukatarta a rayuwata ina sonta bazan ita sadaukar maka da itaba a halin yanzun,nasan ciwo da radadin da kake ciki nadan lokaci ne zaka mance da ita koda kaddara ta hadaku ka gano nine na aureta nasan zaka yafemun"yana maganar muryarsa na rawa hawaye na zuba a idanuwansa,yayiwa motar key sanan yaja yana kokarin kiran layin daddy ya sanar masa da halin da mansoor ke ciki ciki gaba daya a rude yake driving,

Daddy yana kokarin shiga parlor kiran sameer ya shigo yace "sameer mutanen kauye nasan kunje zance ko?"shiru daddy yayi jin yanayin sameer da abinda yake fada yasa yace "Innahlillahi wainnahilaihi rajiun yanzun ina Mansoor dun?"dukkansu dake parlorn mikewa sukayi tsaye a rude momy tace "yayi hatsari ko?meyasamesa ya fadi a mota ne?nasan yadda ya kosa yaga almurar yarinyar nan nasan sai wani abu ya samesa nashiga uku"ta rushe da kuka a rude take maganar rufaida kuwa kuka ta fashe dashi "daddy meye yasamu yaya man?"

"ku kwantar da hankalinku,yana asibiti ne bashida lafiya ashe batare da sameer sukaje ba shikadai ya tafi yanzun sameer ya kirani yake sheda masa akan ankirasa Mansoor babu lafiya ya yanke jiki ya fadi"sandarewa momy tayi a tsaye tace "meyasa zai fadi? meyasamesa ko iyayen yarinyar sun hanasa yarsu ne?yar gidan uban waye da bazasu bashiba babansa yana dan kasuwa dan majalisa"

"ki kwantar da hankalinki yanzun kuzo mutafi asibitin muga halin da yake ciki"a rude suka firfito sukayi motoci biyu dana excort suka nufi asibiti....

sameer na Shiga idonsa ya sauka akan mansoor wanda aka sakawa oxygen a hancinsa yana numfashi a hankali,kasa motsi yayi balle ya taka daga inda yake likitan dake duddubasa yace "kaine sameer?"gaban sameer ya yanke ya fadi ya jinjina masa kai yace "ehh"dakyar maganarsa ta fito ,doctor yace "bismillah ya ka tsaya daga nan ka karaso tunda aka kawosa yake kiran sunanka yaki magana"sameer jiki na rawa ya karaso ya zauna gefen gadon ya ruko hannun mansoir yana murzawa "mansoor calmdown ka kwantar da hankalinka zaka samu sauki kaji ka farka ka farfado i really need you friend please "yana maganar muryarsa na rawa,tawagar su momy ce ta iso suka shigo dukkansu sun kadu da ganin yanayin mansoor cikin kankanin lokaci ya fita hayyacinsa daddy yafi kowa shiga tashin hankali ganin babban dansa daya tilo cikin wanan halin yace "Doctor meye yasamu dana me akayi masa?idan na rasa Mansour zan dauki mataki akam kowa ciki harda kai meke damunsa?"Mansoor a hankali ya bude idanuwansa yana kallonsu yayinda hawaye ke cigaba da zuba a idanuwansa,kallon kowa yakeyi har idonsa ya sauka akan sameer,cikin ikon Allah dakyar ya bude bakinsa daya kafe ko miyau babu sai wani irin d'aci dake tasowa daga kirjinsa yace "sameer....sun aurar da Dina,narasa Dina wallahi mutuwa zanyi idan har ban samu Dina ba daddy"a rude Daddy yace "bazaka mutu ba mansoor zani in nemo maka Dina bazan taba bari na rasaka ba wacece Dina yar gidan uban waye a kauyen?ko waye mahaifinta zani garesa,zan zube masa kudi sanan zan ajiye mulkina da komi nawa na durkusa a gabansa ko wa aka aurawa ita a rabasu ta auri Dana bazai yuwuba mansoor bai taba neman abu ya rasa ba"sameer yaji wani yarrrrrr idan daddy yaje kauye tabbas yasan zaa sanar masa da shine ya aureta,wace hanya zaibi wajen ganin ya Hana daddy zuwa wajen mahaifin Dina dan kashe mata aure a aurawa mansoor ita?momy ce cikin kuka tace "Alhaji ka taimakeni yaron nan ya samu yarinyar nan bansan soyayyar da yakeyi mata tayi zurfi haka ba a nemo wanda ya aureta ya saketa mansoor ya aureta"gaban sameer ya yanke ya fadi cikin zucuyarsa yace bai shirya rabuwa da Dina ba dan shima yanzun ya fara sonta yanzun ya fara shaukin kaunarta shima rabuwa da ita tamkar zare masa rayuwa ne,dik yadda yakeson mansoor bayaji zai iya sadaukar masa da Dina bayan ya rigada ya aureta,

lumshe ido mansoor yayi rufaida tana jijjigasa "yaya man kayi magana kaji"tana jijjigasa dakyar ya bude rinannun idanuwansa yana kallonta saidai sam ya kasa magana dik yadda suke magana bakinsa yaki budewa,
Chapter 35 · 0% Book details