← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 36

Sashe 34

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dina tayi wanka tana zaune kan dadduma ya shigo yadda tayi da fuska yasa yadan tsorata kardai ta farka daddare bata gansa ba? ya shigo ya zauna gefenta yayi tagumi yana kallonta ta turo baki gaba ya tsura mata ido burgesa tayi sosai "yadai nayi laifi nasani ko?"ta jinjina masa kai yace "tou ayi hakuri wanan shine auren ai ko?kin gasa jikinki da ruwan zafi?"kawai yaga ta fashe da kuka ta fada jikinsa,"ni ka daina tambayata nidai banida lafiya ka zauna tare dani"a rude yace "yau tare zamu wuni kinji?ba jnda zani inason shagwabar nan"ta fada jikinsa yana bubbugata,gabansa ne ya fadi tunowa da mansoor fa zai nemeshi suje neman Dina kauye bayan gashi tare da ita gashi yau din nan jinsa yake sabon ango dan haka ya ciro wayarsa a aljihu yaga karfe shida da minti arbain,

ya tura masa message *Hey Man good morning sorry please zuwa kauyen nan i cant make it madam ba lafiya zamuje asibiti idan ka dawo zamu hadu kawai inji ya kukayi idan kaje ka gaida Dina* ya tura masa sanan ya kara rungumeta ya dagota sosai ya haye gado da ita,

jim kadan Mansoor ya shirya tsaf yaga message din sameer yace "ooohhhh bakomi ciwo nagaba da komi"yayi masa reply

*idan nadawo zamu hadu mu tattauna*

Sameer na gani farin ciki ya lullubesa dan yasan babu yadda zaayi yaje kauye tare da mansoor wajen neman Dina bayan yan kauye kowa yasan shine ya aureta....

Mansoor tunda ya dauki hanyar kauyen gabansa ya tsananta faduwa wanda ya rasa dalilin hakan,ya rasa meke masa dadi ya rasa dalilin dayasa yakejin wani sauyi a bugun zuciyarsa kodan zai hadu da Dina ne?......

kunada labarin gobe free pages zasu kare?mai kike jira ki hanzarta ki tura 400 memakon 500 garabasa zuwa gobe normal group vip 600 memakon 700 two pages a rana

2255398726
zenith bank
Amina jibril

shaidar biya ta 07042277401 ko 08036953516

*SLIMZY*😍
[21/11, 09:43] 😍Slim girl❤️: 💥 *MAZA BIYU....*💦

*NA:SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33

*Marubuciyar:*

*K'ADANGARUWA*🦎
*RUD'ANI*💥
*DUHU...*

*INA MASOYA LITTAFIN MAZA BIYU?MAI KIKE JIRA A WANAN TAFIYAR?KINADA LABARIN WANAN SHINE LAST FREE PAGE? HANZARTA KI BIYA 400 NAIRA PROMO A MAIMAKON 500 DA MARUBUCIYAR TAYIWA DIK WANI MASOYIN LITTAFIN MAZA BIYU MASUSON VIP 600 MEMAKON 700 INA MASOYA?*

*2255398727*
*ZENITH BANK*
*AMINA JIBRIL*

*SHAIDAR BIYA TA 07042277401 KO 08036953516*

*20*

Hameeda mamakin khairatu takeyi tana jujjuya wayar da videon da sukayi na dik abinda ya wakana daren jiya itada sameer tace"zan tura masa wanan videon amma sai yayi yunkurin bijirewa bukatuna na dik abinda nace masa inaso ko kuma yayi yunkurin aiwatar da wani abu akaina zan nuna masa shi karamin dan cin Amana ne,dan waccen kucakar da yake makale da ita a d'aki ita zan fara nunawa wanan videon dan tasan abinda ta aura dan inada tabbacin kwadayi ne yasa ta aureshi"hamida ta jinjina kai tace"ki tura videos din ban dik inda kikasan zaa ajiye mikishi ki turawa surayya kawarki"khairatu tace "yess correct nasan idan natura mata tarkon da nayiwa sameer matawalle sai tafi kowa farin ciki domin a halin yanzun babu abinda takeda bukata irin nayi ramuwar gayya akan cin amanar da yayimun"hamida tace "kamar na Allah sai gashi yanata numfarfashi kamar wanda aka dorawa kaya"suka kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya suka tafa,momy ce ta kwankwasa kofar yasa sukayi tsit ta tura kofar tana tsaye tana binsu da kallon tuhuma tace"nikam wai dararrakun mai kukeyi haka ne?kundaisan daddy na cikin gidan nan hai fita ba kuma yayanku yana sama shima nasan bai fita ba in zakuyi ku rage murya banson iskanci"momy na cikin magana sameer ya sauko hannunsa rike dana Dina a karo na farko da Dina ta sauko daga sama tun zuwanta gidan shima shagwaba tasa masa akan lallai saita sakko ta gaida momy,momy na ganinsu ta fad'a d'a murmushinta"ah ah idonki kenan tunda kikazo gidan nan ko saukowa bakyayi?"hamida da khairatu karo sukayi wajen lekowa suga Dina dan rabon da Hamida ta ganta tun ranan da aka kawota,Dina ta durkusa har kasa tana sanye da wata bakar abaya mai stones golden a jiki sai walkiya yakeyi ta yane kanta da gyale yadda sameer ya nuna mata kallo daya zakayi mata ka dauka balarabiya ce yadda tayi wani mugun fari ta kara kyau fararen idanuwanta ta zizara musu kwalli sun kara fitowa da ita sai walkiya takeyi momy kanta cewa tayi "Tabarakallah y'ata kinyi kyau sosai"wani irin kishi ne ya tasowa khairatu irin yadda taga Dina tayi matukar kyau dik irin kyau nata da haske sai taga kanta baka kirin akanta,mamaki ne ya cikata ganin yadda ta sauya bayan hoton da aka turo mata yar kauyece tantagarya,momy ra ruko Dina ta dagota ta rike hannunta"muje yau tare zamu karya"gaban sameer ne ya fadi bayaso Dina ta dauki wasu mintoci a kasa tsoronsa kada mansoor yazo gidan idan har bai tafi kauye neman Dina ba ya ganta,bakinsa na rawa yace"sama zamu hau momy can zamuyi breakfast kisa akai mana"khairatu na tsaye tana kallonsu tamkar ta sokawa Dina wuka tsananin takaici, cikin zuciyarta tace"zaki zama yar kallo kamar yadda kikazo daga kauye haka zaki koma ki auri bakauye ki koma saka badani jaka jar hodar nan mai kama da jar kasa ita ta dace dake da zarar na nuna miki videon mijinki yana kwanciya dani hade da sambatu"tayi guntun tsaki wanda ya fito fili yasa momy juyowa da sauri ta kalleta itada Hamida wadda tuni ta sandare a tsaye tace"au kuna ganin yayanku da matarsa bazaku gaisat dasu ba"kallon da khairatu tayiwa sameer yasashi Hadiyar wani miyau mai kauri yace"sun gaishemu bakiji bane momy Bari mu karasa sama Dina batajin dadi yanzun ma ta matsa ne mu sauko ta gaisheki"yana maganar yana kokarin ruko hannun Dina a gaggauce babban tsoronsa da tashin hankalinsa shine kada mansoor yazo gidan dan su tafi kauye dikda ya fada masa bazaijeba,"meyake damunta kuje asibiti mana ka kira...."kafin momy ta karasa ya tarbi numfashinta yasan mansoor takeso tace sam bayaso a ambaci sunan mansoor kada Dina taji a fama mata ciwon dake cikin zuciyarta yasan cewar bawai ta hakura da son Aminin nasa bane"momy taji sauki jiya kin kwanta lokacin danasa aka duba ta"Dina ta kallesa jin yayi karya yasan tsaf zata karyatasa yasan wawtarta yasa ya hada rai yana kallon irin kallon da takeyi masa a gaggauce yaja hannunta sukayi sama,momy ta bisa da kallo tana murmushi a fili momy tace"kila an samu karuwa ne"tana yar dariya khairatu ta ce cikin ranta "kina gab da maraba da jikoki da dan sunnah da dan shege"momy ta wuce parlor khairatu cike da kishi ta kasa sukuni ta soma sunturi a cikin dakinsu hamida tace "wai kinga yadda yar kauye tayi clean wallahi nadauka balarabiya ce"khairatu ta toshe kunnuwanta cikin daga murya tace "ya isa Hamida"Hamida ta kama bakinta ita ta kosa taje gida ta shafawa momy Ruma badakalar da akeyi a gidan matawalle......

*******
Anty zali kanwar momy na zaune suna fuskantar juna da momyn Mansoor tace"niko inaga wanan dabarar da kikayi akan mansoor kin amince da aurensa da Dina yar kauye tamkar yaudara ce kinsan halin mansoor sarai idan har baku amince da aurensa da muradin ransa ba to wallahi koda kun aura masa nabeeha zai iya sakinta dan ya kunsa muku takaici,inaga gara ku lallabasa ya auri Dinar daga baya saiya auri nabeeha kinga bazaiyi musu ba tunda yasan cewar kunyi masa abinda yakeso sanan ina mai tabbatar muku idan har kuka hanasa Dina to tabbas wanan shaye shayen daya bari zai koma kuma babu wanda ya isa ya hanasa"shiru momy tayi tana sauraren kanwar tata jiki a sanyaye tace "zaliha kin kawo shawara dan tabbas mansoor zai iya bijiremun ya rabu da yarinyar nan kina ganin farin cikin da takeyi yau tunda ta wayo gari da labarin ya Amince da aurenta"Anty zali ta gyada kai tace"idan ya dawo kauyen zan kirasa zamuyi magana zan lallabesa yadaina wulakanta nabeeha kema kuma karki nuna masa kiyayyar da kikeyiwa abinda yakeso gudun kasa ya bijirewa bukatarki tunda idonsa ya rufe akan wanan yarinyar"momy tace"haka ne,yanzun zan fara shiri amma wallahi niba wani d'okin auren sa da yar kauyen nan nakeyi ba"Anty zali tayi murmushi tace "koma menene dai ayiwa yarona abinda yakeso,yanzun zan biya kasuwa zan duba wasu abubuwan afara siyayyar ita waccen ko?"momy ta tabe baki tace"me zaa siya mata banda dangwali yab'a da bad'ani jaka hodarsu ta kauye ai komi daidai da ita zaayi tunda already nabeeha an rigada anyi siyayyar aurensu tun kafin tafiyarsa cyprus"dariya kawao Anty zali tayi ta dibi makullin motarta tace "koma dai menene komi kauyancinta surukarmu ce haka zamu karbeta"ran momy ya baci ji takeyi tamkar ta kashe tsinanniyar yarinyar nan idan mansoir ya aurota yadda taki jinin talaka?talakar ma ta kauye?batasan wace kalar yarinya bace mansoor ys susuce akanta a kauye,tayi tsaki suka jera suka fito daga sashenta suna tafe suna kara tattaunawa....
Chapter 34 · 0% Book details