Sashe 17
Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*******
yana makale da waya daddare suna magana da Dina "kinsan me na gama shirya komi akan sakaki a makaranta batare da mahaifinki yasan daga wurina bane kingane ko?"ta lumshe idonta tanajin wata sabuwar kaunarsa na kara shiga cikin jikinta cikin wani irin yanayi tace "idan ka tafi yaushe zaka dawo?"cije lebensa yayi yace "da inada damar dawowa kauyen nan da zama dana dawo gabaki daya kodan saboda ke abokiyata Dina"murmushi tayi tace "nidin?har matsayina yakai hakan?"bece komi ba yayi shiru hakan yasa ta gane yaji haushi tayi yar gyaran murya tace "Afwan nasan kayi fushi amma kasan mene?nasamu kaina cikin kunci yau din nan, saboda ganin innahta tana kuka da hawayenta saboda fasa aurena da akayi da tasiu,amma ta wani fannin kuma ina farin ciki da hakan koba komi bazamu rabu ba zamu cigaba da abotarmu,kasan mene?wallahi da babu wayar nan inaga idan ina kewarla sato hanya zanyi intafi birni"dariya ya kwashe dashi wadda bemasan ta kwace masa ba ya mike ya zauna "zaki sato hanya kitaho birni idan kikazo kice wajen waye kikazo?"yayi maganar yana dariya yasa wayar a speaker ganin sameer ya tsaya da buga karta da yakeyi dukkansu sukasa kunne suji me zatace salati sukaji ta hauyi "meyafaru?lafiya Dina?meke faruwa?"tace "ina zuwa sautin kukan innah nakeji dama tunda rana nake ganinta kamar batada lafiya taki fadamun saboda fushi takeyi dani"
"karki kashe wayar ajiye kawai zan ajiye idan kinzo kawai kiyi magana ki fadamun meke faruwa Dan Allah"yace cike da damuwa,ta dire wayar akan katifarta yana jin karar bude kofarta ta fice,
ya dubi Sameer da yanayinsa ya sauya wanda gaba daya Mansoor ya kasa gane menene damuwarsa ya tambayesa yaki fada masa saidai yana ganin damuwa a kwayar idonsa "lafiya wai sameer?kanata mun boye boye kaki fadamun ainihin damuwar ka gabaki daya ka sauya tun dazun ga abincin da muka tura akayi order nan kakici"sameer ya dauki cup din shayin daya hada kawai ya soma sha mansoor ya tsura masa ido yana saurarensa bece komiba,
"yaya man....."da sauri ya dauki wayar ya kara a kunnensa ya cireta a speaker"yadai meyafaru"kuka yaji ta rushe dani , gabansa ne ya shiga faduwa "lafiya?"yace yana saurarenta cikin kuka tace "innah ta ce batada lafiya ciwom ciki ne yake damunta har suma takeyi na sameta tare da baba dik tayi Amai nashiga uku banaso na rasa mahaifiyata"a tsorace yace "ganinan zuwa bari nazo mukaita asibiti"
"kada Kazo idan kazo babana zai gane wani abu zansan akwai hanyar da muke magana nida kai,yanzun zan fita cikin darem nan nemo motar da zata dauki innah mu fita mutafi asibiti"ajiyar zucuya ya sauke yace "okay nasan mafita "Yana gama magana ya kashe wayar ya diro daga shi sai singlet ya dauki rigarsa ya zura "ina zakaje a daren nan?"
"waccen golf 3 din motar can nakeso nasa daya daga cikin yaran nan da ke cikin gidan nan suje wucewa ta inda gidansu Dina yake yadda zaakai mahaifiyarta asibiti"sameer ya mike yace "bazan barka ka fita ba"tare suka fito cikin saa aka tada motar suka tsaya a wajen gate din gidan har ya karya kwanar hanyar gidansu Dina,
Dina ba tsunnne a kofar gida tana rizgar kuka mahaifinta na tsaye yana kallon hanya gabas da yamma kudu da arewa babu kowa sai kukan tsuntsaye,gashi garin yayi bakinkirin da hadari karfe biyu na dare suka hango hasken mota "Alhamdulillah ga mota nan kila malam dauda ne ya dawo tukin dare"ya Shiga saka masa hannu,kamar yadda mansoor ya shirya haka ya tsaya mahaifin Dina ya tsaresa da ido kamar ya ganesa saidai besan a ina bane "baba meyafaru na ganku a nan cikin darem nan?na kawo tumaki ne gidan mai gari zan dau hanyar birni"ajiyar zucuya baba ya sauke "mara lafiya garemu ka taimakeni mu tafi tare dakai dan dik garin nan asibiti daya ne kuma kasan yanzun an rufeshi sati guda kenan har suma takeyi"ya jinjina masa kai ya kashe motar ya fito tare suka Shiga suka fito da innahrt Dina baba ya dauko kudin dayake shirin maidawa Sameer yasa a aljihu suka dau hanya......
******
washe gari,
"Dina yanzun ya kike gani?wanan kudin dake hannuna bazasuyi ayiwa mahaifiyarki aiki kamar yadda likita ya fada ba kodarta ce tasamu matsala aiki zaayi mata ai mata dashen koda,sun gwadani akan yadda zaayi a dauki tawa daya asa mata nima ance bazai yuwu ba gashi bamuda kudin da zamu siyi koda"cikin kuka tace "baba ni su cire tawa duka indai innahta zata Rayu banida wani buri a wanan duniyat daya wuce ganinku cikin koshin lafiya,nasani nice silar shigarta cikin wanan halin a ta dalilin bakin cikina ne"baba yasa hannu yana sharewa Dina hawaye idonsa jajir yace "kaddara ce kawai Dina bake bace fatana tasamu lafiya idan burinta ki auri tasiu din ne ni zan basu hakuri suxo ayi maganar aure ki aureshi din dikda banason gurbata rayuwarki hakan yasa na tsani wancen dan shaye shayen,wanan kudin ma so nayi na mayar musu saiga wanan iftila'in,yanzyn abinda zanyi kawai kauye zan tafi ga wanan ki siyi abinci ku karya insa gidanmu a kasuwa inyaso sai ayi mata aikin"wasu sababbin hawaye taji suna zubowa daga idanuwanta masu dumi ta zura masa ido ta kasa magana,
mansoor ne ke jan motar tare da sameer da driver daya kawosu daddare yayi musu jagora har asibitin daya kawosu yayi parking a harabar asibitin ya dubi sameer yace "bazamu fito ba banaso ya ganmu bazan lamunci yayi mana tozarci cikin jamaa ba dikda taimaka musu zamuyi amma kasan mutumin kauye da kafiya"Sameer ya nisa yace "haka ne tabbas amma kamar gashi nan fita zaiyi"ta jikin glass din mota yabi mahaifin Dina da kallo har ya fita sanan suka firfito,ta mike tsaye tana tunanin yanzun ta ina zata fara?yau gata a birni amma a sanadin rashin lafiya?"ganinsa tayi tsaye a gabanta ya harde hannuwansa a kirjinsa ya zuba mata ido fuskarta ta kumbura sosai tayi jajir alamar tasha kuka,
"ya sameer kune?"tayi maganar a sanyaye tana satar kallon mansoor yace "mune"cikin mamaki take kallonsa yadda akayi yasan asibitin da aka kaisu,ta juya tana hada ido da driver ta gane dama mansoor ne ya turoshi?a hankali ta sauke ajiyar zucuya a sanyaye ta dubesa tace"nagode"bece komi ba sameer ne yace "yanzun me ake ciki?"wani miyau mai kauri ta hadiye sanan ta fashe da kuka ta soma yi musu bayani,
dukkansu shiru sukayi cike da tunani,daga bisani Mansoor yace "inaga zanga likitan kawai zan shiga a gwadani idan k'odata zatayi kawai a cire daya asa mata"zaro ido waje Dina tayi tana kallonsa tana girgiza kai cikin fargaba da tashin hankali tace "kodarka?zaa cire asawa innah ta?"ya gyada mata kai,
Sameer ya kauda kansa gefe yana wani tunani yace "noo bazaayi haka ba man tayaya zaa cire kodarka asa ma innahta?bayan ni inada kudin da zan iya Siya mata koda daga naira daya zuwa million dari?"kallonsu kawai takeyi dan bata fahimci wanam lissafin ba,
daddy ne ya kira layin Mansour ya dauka da sauri "Hello Daddy barka dai"yace yana gyara tsayuwarsa "ance anga motarku ta shigo gari ina kaje?"ya kalli cikin asibitin sanan yace "ehh nashigo ina dan wani abu ne zan karaso"
"kazo yanzun yanzun nan"daddy ya katse wayar yace "sameer daddy na kirana i have to go kasan akan rigimar da muke nasam an fada masa ne so zan barka a nan kayi handling komi"sameer ya gyada masa kai suka wuce tare da driver,
Dina shiru tayi ta kasa magana,wani irin matsayi mansoir garesa haka da isowarsa keda wuya dik girman birni ace har anganeshi mahaifinsa yasani?sanan wace irin matsala yake ciki. haka!?shi kuwa sameer tsaye yayi akanta ta rafka tagumi ya tsura mata ido wanda besan yanayi ba kallonta kawai yakeyi ko kifta ido bayayi ji tayi a jikinta ana kallonta a hankali ta dago kai taga yadda ya tsareta da ido gabanta ya fadi ta kalli kanta sanan tace "lafiya?"ajiyar zucuya ya sauke yace "bakomi"ta sunkuyar da kai barinta yayi a wurin kawai ya shige cikin asibiti wajen likita.......
Page Daya zaku samu yau🫣
*SLIMZY*😍[13/11, 09:35] 😍Slim girl❤️: 💥 *MAZA BIYU....*💦
*NA:SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33
*Marubuciyar:*
*K'ADANGARUWA*🦎
*RUD'ANI*💥
*DUHU...*
*11*
*Assalamu alaikum* ina maiso taga tayi K'IBA jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga NONO yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakkiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku zumar kiba, zumar kiba zumace wadda zata saka kiba cikin kwana 7 dayardar Allah zumar kiba zumace mai inganci wadda aka hadata da magun gunan gargajiya,Bugu da qari har nafdac ta amince da lafiyar zumarmu ta bamu BACH NO hjy indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kasha zuma saika chanza Maza kinemi mmn khairat domin samun ingantacciyar zumar qiba Mai cike da lafiya with zero side effect🤗 08167453086