← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 36

Sashe 13

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"sai kace wata gidan rediyo?"tace hade da murmuda baki, murmushi yayi samun kansa yayi da nishadi nan da nan ya mance bacin rai da damuwar dayake ciki,kiran wayar nabeeha ne ya shigo wayarsa call waitin ya duba yayi tsaki da sauri tace "waye kakewa tsaki badai Abokina sameer ba"ya juya ya kalli sameer daya dage kafarsa yana waya hankalinsa kwance yace "yayi bacci"tace "toh"nan suka cigaba da hira da Dina wadda hakan yasa mansoor yaji wata kaunarta na kara shigarsa cikin minti talatin wata shakuwa tashiga tsakaninsu dikda hirar da sukeyi surkullenta da kauyanci take baza mai,

"yauwa ya man nace karkayiwa su tasiu komi kaji"cije lebensa yayi tunowa yayi da yasa an dauresu yace "bazanyi ba tunda bakiso"murmushi ne ya subce mata,

innahr Dina zama tayi ta kara fitilar dakin ta taba babanta dake kwance wanda shima ba baccin yayi ba "tashi kaji"da sauri ya tashi yana kallonta "lafiya kika tasheni cikin wanan daren?"

"nifa ina tsoron mutanen nan kudin nan da aka baka da sunan zakka kar azo siyar musu da Dina kayi"ajiyar zuciya ya sauke "ko daya,yaron daya bani yanada hankali sameer sunansa, ba irin shashashan abokinsa bane mashayi,ki kwantar da hankalinki bazan taba siyarda dina ba"

"idan sukazo da maganar soyayya fa?"innahr Dina tayi maganar cike da damuwa,nan da nan fuskarsa ta sauya yace "babu soyayya tsakanin su domin wanda ke son nata ko mutuwa zaiyi bazan bashi yata Dina ba"shiru dukkansu sukayi ji sukai kamar ana magana cikin gidan hakan yasa hantar cikin innah ta kada "kaji ko kamar muryar Dina nakeji kardai yaron nan cikin dare ya biyo tunda ka yanke alaka a tsakaninsu"

saukowa yayi daga gadon cikin fushi yace "idan shine kuwa saina sheme masa kai inyaso uban nasa yazo garin ya kaini kiri kiri"mikewa tayi Yana kokarin bude kofar fale fale,

kara Dina taji alamun bude kofa idonta a lumshe suna magana tayi saurin budewa ta zabura ta zauna tace "ya man naji motsin bude kofa kamar su baba ne saida safe"tana gama maganar ta katse ta daga katifa ta tura waya,mahaifinta daidai nan ya turo kofar dakin ta rufe ido cikin zuciyarta tana adduar Allah yasa beji ta ba......

*SLIMZY*😍
[11/11, 08:16] 😍Slim girl❤️: 💥 *MAZA BIYU....*💦

*NA:SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33

*Marubuciyar:*

*K'ADANGARUWA*🦎
*RUD'ANI*💥
*DUHU...*

JAMA'A, INA GABATAR MAKU DA ROYAL EXQUISUTE, GIDAN GYARAN AURE, GIDAN AMINCI, GIDAN GIGITA MA'AURATA, JAMAA INA AMARE? UWAYEN GIDA? ZAWARAWA? DA KUMA MASU JEGO, INA MATA? MATAN DA SU KA AMSA SUNAN SU MATA? MATAN DA SUKE SON ZAMA DARAM DAM A ZUKATAN MAZAJEN SU? MATA ƳAN ƘWALISA? TO WALLAHI ROYAL EXQUISUTE NA KU NE, SUKE DA INGANTATTUN KAYAN MATA NA GYARA BA WAI TAWULWULBA, BA WAI SHA KA TAFI BA, KAYAN MATA DAKE ƘARA DARAJA DA ƘIMA WAJEN OGA, GA SAUƘI GA ARHA, GA KUMA AIKI..ROYAL EXQUISUTE ZATA GYARE KU
KI TUNTUBI WANNAN NUMBER 08030644073
Location kano,nationwide delivery

*8*

kallon kallo innah da baba sukeyi tsaki yaja "gashi kim fito damu a daren nan kedai kawai kin tsorata kina tunanin zasuzo su sace miki yarinya babu mai sace Dina a cikin garin nan sanan kisa a ranki bazan taba bawa wanan yaron yarinyar nan ba ko shi kadai ne namiji a duniya bazan bawa mashayi yata mara kunya ba"yana gama maganar ya fice,innah ta girgixa kai ta janyo kofar tabi bayansa,a hankali Dina ta bude idonta maganganun mahaifinta keyi mata yawo akai,meyasa babanta zaiyi wanan furucin akan mansoor saboda ya damu da ita?bayan shaye shayen ya daina a dalilinta wanda itace ta zama silar shiriyarsa?sam bataji dadin furucin mahaifinta ba,kawai be fahimci mansoor bane,ajiyar zuciya ta sauke ta ciro wayar daga kasan pillow tana kallo,murmushi tayi tana jujjuya wayar "ban gaji da magana da yaya man ba gashi yanzun na katse wayar kuma ban iya kiransa ba dana kirasa mun karasa maganar mu,naji kamar yanaso yamun magana akan makaranta,ta gyara kwanciyarta tana rike da wayar cikin zuciyarta tana adduar Allah yasa ya kira tana son jin muryarsa ashe yana hira haka?

mansoor tagumi yayi minti minti yaja tsaki,ya kalli sameer wanda tuni yayi bacci,ya daga ido ya kalli agogo karfe biyu da minti arbain da biyar na dare,yayi tsaki meyasa mutumin nan zaiyi musu haka? mahaifin Dina ya cika tsauri,meye yajeyi cikin dakinta a wanan daren idan ba fiti na ba?dan shi ya haifeta aiba Shi ya halicceta ba da zai takurawa rayuwarta,tsaki yaja ya koma ya kwanta ya lumshe idonsa, muryarta ce ta daki dodon kunnensa "yaya man...."wani zabura yayi ya zauna "no no bazan iya bacci ba sai naji muryarki Dina sai naji halin da kike ciki,i will call you just once in kin dauka shikenan idan bako dauka ba nasan mugun mahaifinki yana tare dake yana azabtar mun dake,ya cije lebensa ya dauki wayarsa ya sake kiranta,wayar na shigowa ta zabura ta dauka ta kara a kunnenta,wata ajiyar zuciya ya sauke yace "are you ok?"shiru tayi bataji abinda yace ba ya sake fada,still batayi magana ba ya ciro wayar a kunnensa yaga tana tafiya ya sake karawa a kunnensa yace "Dina....."cikim siririyar muryarta tace "naam yaya man....."ya lumshe idonsa wani nishadi ne da farin ciki ya lullubesa yace "halan bakiji ina magana ba kika share bakice komi ba"

"tou aidai kasan banajin yaren nan naka na yan birni"tayi maganar kamar tana rad'a can kasa da muryarta tayi wanda hakan ya haifarwa da mansoor wata irin kasala,wani irin yanayi yakeji wanda be taba jinsa ba a rayuwarsa "kasan me?"ta katse masa tunani Yana lumshe ido yace "sai kin fada"tayi shiru kamar bazata fada masa ba,tana gudun kada ransa ya baci yace "umhmm ina jinki yi magana"tace "babane daya shigo"

"ya dakeki ko?"yace a kausashe da sauri tace "ah ah,cewa yayi bazai taba baka ni ba idan ma siyansa kukesonyi da sameer ya bashi kudi,ko kai kadai ne namiji a duniya"wani irin bacin rai ne ya ziyarci mansoor nan da nan jijiyoyin kansa suka firfito zucuyarsa nayi masa wani irin zafi da tukuki,tana magana ya kashe wayar,take taji hankalinta ya tashi ta zabura ta zauna tace "nashiga uku ya kashe wayar meyasa nafada masa?"ta jingina da jikin bango take wasu hawaye da batasan dalilinsu ba suka soma zubowa,

shi kuwa kamar mahaukaci haka ya mike ,"an fada masa ni zanzo neman aure wajensa ne?koko an fada masa zanso yarsa da aurene?be kai matsayin da zanzo in durkusa dan ya bani yarsa ba,babu wanda ya tabamun wulakanci da kaskanci irin wanda mutumin nan yayi mun,wato sameer ya kai masa kudi ne dan ya amince damu mu rinka kula yarsa ko mene?"cikin daga murya yake maganar,sameer cikin bacci yakejin maganar mansoor sama sama idonsa a rufe yaji mansoor na bubbuga sa da sauri ya mike ya zauna "lafiya?meyafaru?ko an daura aurenka da nabeeha ne?"ransa ya kara baci kiran sunan nabeeha da sameer yayi,

"meyasa kayimun haka sam?meyasa ka siyarmun da mutunci?sam tayaya zaka dau kudi kaba mahaifin Dina?ka zubar mun da mutunci?yayi tunanin nayi hakan dan in siyeshi ne! yaushe kabashi kudi?"jikin mansoor har rawa yakeyi yayi fushi sosai,sameer ya nisa ya dafe kansa sam bayason irin maganganun da mansoor yakeyi akan mahaifin Dina bayan yana tare da yarsa kuma sonta yakeyi dikda ya kasa yarda da hakan?katse masa tunani yayi "magana nakeyi kayi shiru"sameer yace "yanzun meya faru?"nan mansoor ya kwashe yadda sukayi da Dina a waya ya fadawa Sameer,

"calm down ni abun arziki nayi,dan ban fada maka bane kawai ya zama laifi,nazo da kudi sosai dayawa da zan rabawa mutanen garin nan saboda zakka muka fidda hakan yasa na dauka nabawa mahaifinta amma bada nufin wai in siye bakinsa ba,akan me zan siye bakinsa bayan kaidin kace ba soyayya kukeyi ba"shiru mansoor yayi be sake cewa komi ba, Sameer ransa ya baci ya koma ya kwanta kawai badan yanajin bacci ba saidan zafin abinda mansoor yayi masa,yaja tsaki ya gyara kwanciya yaja bargonsa,

kasa bacci mansoor yayi zuciyarsa keyi masa wani irin kuna,gashi ya kashe mata waya batare da sunyi sallama ba me zata dauka?ko ya kirata ne?wata zucuyar tace kada ya kirata meyasa zai tsanesa haka kawai dan kawai yana shaye shaye?yaja tsaki ya dubi agogo hudu da rabi ya mike kawai ya shige toilet ya dauro alwala ya fito ya shimfida dadduma ya tada sallah,.

lamo tayi akan katifarta tana kallon wayar batajin bacci lokaci kankani bacci ya kaurace mata dole zata sanarwa da mahaifinta waye mansoor dan bataji dadin furucinsa akansa ba,to idan ta fada masa hakan zai tabbatarda bataji maganarsa ba suna nan tare,dakyar bacci barawo ya saceta gab da asuba,befi baccin minti arbain tayiba taji innahrta na buga mata kofa.....
*****
"rufaida kin fito?dama yanzun nakeso in tasoku kizo kiga wadanan kayan hajiya basira ce da sassafen nan tasa driver dinta ya kawosu na dauka zaasa a akwatin nabeeha"rufaida ta zauna tana kallon tsubin kayan dake gaban momy fuskarta babu walwala Momy tacev"yadai naganki haka ina nabeeha?bata tashi ba tana nan tana baccin nata"girgixa kai tayi "ko daya matar da batayi bacciba ta kwana tana kuka"momy ta fiddo ido waje "meyafaru meya hanata bacci?"rufaida ta nisa "momy wanan auren da kuke shirin yiwa yaya man da nabeeha bafa ya sonta fa?ina zargin akwai wadda yakeso wallahi saboda jiya dik Kiran da takeyi masa baya dauka call waiting daga karshe yayi diverting calls dinta wanda hakan ne yasa hankalinta ya tashi take tunanin dawa yake waya kuma kinsam fa dama basu daidaita kansu ba"tana maganar tana kokarin daukar passport din data gani zube a centre table "wanan fa?"ta bude taga passport din mansoor ne dana nabeeha wanda aka kai har visa ta fito zasu tafi nan da sati uku,tabdijan "momy dagaske kukeyi dai zaku daura auren ya man da nabeeha su tafi Cyprus "Momy tayi tsaki tace "da karya kike ganin inayi?eye? to dagaske nakeyi koma dawa yakeyin waya shi yasani shi ta shafa amma tabbas sai ya auri nabeeha ya tafi da ita,zamu rabashi da garin nan ne saboda wanan mugun shaye shayen da yakeyi"rufaida ta bata rai tace "dan shaye shaye?idan kuma yasamu me hanasa fa?"
Chapter 13 · 0% Book details