← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 36

Sashe 29

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ina zakaje?ko ganina ne bakaso?idan nice bakason gani dole zakaso ka shaki numfashin abinda ke cikina Daya kasance mallakinka sameer?ko kanaso kace baka sona yanzun waccen bagidajiyar daka kulle a cikin daki itace muradin zuciyarka sameer?karya kakeyi kayi karya kaso wata bayan ni ina sonka soyayyarka ce tasa na zabi haihuwar shege a gidan kakansa"maganganunta suna tafarfasa masa zucuya cikin tsananin fushi ya kalleta ga mamakinsa hawaye yagani suna zuba a idanuwanta hakan yasa jikin sameer yayi sanyi ya tsareta da manyan idanuwansa wanda kallo daya zakayi masa ka hango tsananin furgici da rudani,kallonta yakeyi cike da mamakin karfin hali irin na khairatu tana tunanin zuwa gidansu da cikin shege zaisa ya aureta?yayi murmushi yasa hannu ya share mata hawaye yace "ya isa haka kinsan banason kukanki ko a da ballantana yanzun da kike dauke da gudan jinina"cike da dabara da lallashi yayi maganar ta fada kirjinsa yayi saurin tallabota tana sauke ajiyar zuciya yana bubbuga bayanta yana waigawa gefe da gefensu bugun zucuyarsa ne ya tsananta daga idanuwansa yayi saman bene ta bangaren dakin Dina yaga window dinta a bude ya tsare window dun da idanuwa gabansa na tsananin faduwa yake hangen tamkar inuwarta a tsaye jikinsa na rawa ya janye jikinsa daga nata tayi saurin kallonsa ya sunkuyo da kansa daidai kunnenta yace"come on so kikeyi a fahimci wani abu?kinsan momy fa tana gidan nan kuma naga alamar kamar motar daddy"yana maganar yana waigen sama cikin dabara khairatu ta kalli inda yake kallo windown Dina ne a wajen yake facing garden din tayi ajiyar zucuya tace "ko kuma kana gudun matarka tasan halin da muke ciki ko?kana jin tsoronta ne?"girgiza kai yayi ya shafa gemunsa cikin sauri yadan ja da baya ganin momy daga nesa tana magana da masu yankan flowers,tasha wani tsadadden lace red mai flowers baki fa gyalenta da takalmi da jakarta duk bakake,kamar ance ta waigo ta gansu,nan da nan momy ta sauya fuska ta watsawa Sameer harara yayinda ta karaso idanuwanta dauke da tambayoyi gabansa ne ya shiga masa lugude "mai kukeyi ku biyu a nan?"tace a kausashe ya sosa keyarsa yace "naga khairatu ita kadai a nan tana kuka ne"ya kalli khairatu ya kashe mata ido ta sunkuyar da kai momy tace "kukan mai kikeyi khairatu?ba nace kidaina koke koken nan naki ba?ko ba nayi miki fada akan abinda ya sameki kaddara bace?kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki har Allah ya saukeki lafiya kigani dik wanda yayi miki cikin nan sai mun karbar miki yancinki sanan sai ya dandana kud'arsa"khairatu ta saci kallon sameer wanda ya basar tamkar babu wata damuwa a tattare dashi tace "wuce ciki kije ki kwanta zan dan fita ne yanzun zan dawo"khairatu ta jinjina kai tana waigen sameer ta baya tabi,kasa tafiya tayi samun kanta tayi da son sauraren mai momy zata fadawa sameer,taga alamar taji haushin ganinsu tare,hmmm matar nan batasan cikin dake jikinta na danta bane ko? har take wani zare musu ido ganinsu tare?sai ta wayi gari ta gansu kwance a gado daya a daki daya sanan zucuyarta zata buga ita sameer zai yaudara yayi aure?ta kasa kunnenta ta bayan flowers,

"sameer kada in sake ganinka da khairatu kun kebe ku biyu kaji nafada maka ko?idan nasake ganinku kaida ita tabbas saina bata maka rai, kasani ciki take dauke dashi wanda baasan na waye ba Allah ne yasa ma bazaka aureta da cikin wani ba dayake Allah yaga zuciyarmu ashe tagama zubar da mutuncinta a waje"sameer ya jinjina kai gumi ya karyo masa khairatu shine ya fara saninta a waje kuma shi kadai ke taba jikinta,shiru yayi ya kasa cewa komi momy tace "yadai naga dik yanayinka ya sauya?"ya girgiza kai yace "bakomi bari nashiga ciki nasamu Dina"momy ta jinjina kai tayi murmushi tace "abinda boyonta kakeyi yarinyar nan ko hira baka bari ta fito muyi"suna maganar suna tafiya a tare,ya sosa kewayarsa cikin zucuyarsa yace "tayaya zanbari Dina ta fito momy?Dina bazata taba fitowa ba banason kaddarar da zata hadata da mansoor domin yanzun nine mallakinta"a zahiri yace"batason yawan magana ne kawai inacewa ta sauko bataso"momy ta bude mota tace "yauwa wai kaji mansoor jirgin rana zai biyo da yamma zai sauka ko?naji dazun suna magana da daddynku yace bayaso a fada maka ne surprise zaiyi maka saidai ya kiraka yace ka daukoshi a Airport kawai nafada maka ne dan ka shirya gashi nasan nan zaici abinci ya kenan?kaga dai Dina bata iya irin abincinmu na birni ba"tana maganar ne amma gabaki daya gumi ya jika sameer tashin hankali wani irin damuwa yakeji a ransa gashi yana tsananin bukatar mansoor Amininsa a tare dashi gashi ya auri Dina ya kenan?tayaya zai kaucewa haduwar Dina da mansoor?"tsaki momy tayi "kai kasani kag driver ja muje ina magana yana can yana wani tunani na daban"karar rufe kofar motar ne ya dawo dashi daga tunani yace "momy...."ta watsa mai harara driver yajata ya soma horn gefe ya koma ya lumshe idanuwansa Amininsa zai dawo gari yasan yana dawowa zai bukaci Dina,lumshe idonsa yayi ya hasko fuskarta dazun sosai take burgesa yadda take magana,kunnuwansa ne suka tuno masa da sautin kukanta da barota da yayi a daki tana kuka,cikin sauri ya nufi hanyar da zata sadashi da cikin gidan dole ya lallabata ta bashi tausayi yasan yadda take tsananin son mansoor dole dik yadda zaiyi ya mantar da ita mansoor kota wani hali....

*******
"Ah Ah su Anty nabeeha Kenan anata shiri kinji yadda dakin nan ya kaure da kamshi kamar a maiduguri?kamar wata amarya"cikin sigar tsokana rufaida tayi maganar ta zauna gefen gadon da nabeeha ke shiryawa "kin manta ni Amarya ce?ko kin manta yaya Mansoor nadawowa zamuyi aure?na tabbatar yanzun ya mance da wanan yar kauyen "rufaida ta jinjina kai ta sauke gauron numfashi tace "Allah yasa kam"nabeeha tayi farrr da ido "kinga nasa su Asama'u su fara shirya abinci kafin na fito nashiga kitchen din na tayasu Dan dani zaayi abincin da yaya man zaici"rufaida tace "dakyau Amaryar yaya man aimu yan biki ne Allah dai ya dawo dashi lafiya,kenan ke yaya sameer zaizo ya dauka yaje daukoshi?ya kamata ace yayi tozali da wanan kwalliyar daya sauko daga jirgi"nabeeha tace "kinsan bazai yuwu ba yaya sameer nasan shi kadai zaije kila da matarsa zasuje taryar yaya mansoor"rufaida ta yatsina fuska"Allah yasa da ita din tinda bata fitowa fa koda mukaje gidan da momy jiya yin Allah ya sanya Alheri bamu ganta ba "nabeeha tace "boyonta yakeyi yafiso abokinsa ya soma ganinta"rufaida batace komiba ta mike tsam tausayin nabeeha takeyi dan koda sukayi waya da yaya mansoor ya tabbatar mata yana isowa kauye zaitafi wajen Dina tasani su momy sunyi haka ne dan su mantar dashi auren yar kauye basusan yar kauye soyaytarta tayi dashe da jijiyoyi da rassa a zucuyar yaya man ba,

nabeeha na ganin fitar rufaida cikin sauri ta bude wardrobe dinta ta fito da kwalin da ummah ta karbo mata wajen boka ta tsaya a gaban madubi tasa shi da kyau ta fito da turare ta dangwalo ta zana a koshinta kamar cros ta lumshe ido tace "idona idonka yaya man ka tashi aiki babukai babu wata yar kauye nice zan mallakeka nikadai na dace dakai"ta fada kan gado cikin farin ciki,momy ta kwala mata kira cikin sauri ta mike ta fice sukai karo tanata faraa tace"ah ah nabeeha dik wanan murnan ganin mansoor ne?"nabeeha ta sunkuyar da kai cike da kunya,momy tace cikin zuciyarta Allah yasa dai ya mance da waccen kucakar bakauyiyar"a zahiri tace "tou muje ku shirya masa dining nasan yanzun sun kusa sauka"tace "Toh momy"tayi gaba momy na bin ta da kallo cike da tausayawa,momy ta lumshe ido tace "ai nayi shiri akamsa ke nakeso ya aura da zarar yaci abincin can nasan zucuyarsa zata cire masa son wata tsinanniya nan"tabi bayan nabeeha cike da sake sake....

*******
sameer na rungume da Dina a kirjinsa ta kwantar da kanta ta gefen idonta hawayene ke zubowa wanda batasan dalili ba tarasa dalilin dayasa zucuyarta ta kasa mantawa da mansoor dikda ya yaudareta ya cusa mata soyayyarsa daga karshe yayi tafiyarsa amma ta gagara mance amon sautin muryarsa a kunnenta,ta gagara mance kyakkyawar fuskarsa da shanyayyun idanuwansa dama karya yayi mata da yace ya daina shaye shaye?....wayar sameer ce take ruri idanuwansa a rufe ya janyo wayar dayan hannunsa na cikin gashin kan Dina yana yawo da hamnunsa ciki wata irin natsuwa yakeji ta musamman yau kasancewarsa tare da Dina "Ranka ya dade aiki nata tafiya yanzun haka an kusa kammalawa sirikin naka baban Dina yace ayi maka godiya"abinda Dina taji kenan ta dago kai ta tsaresa da ido,wani abu yaji ya tsarga masa ganin irin kallom da takeyi masa ya hura mata iska a ido ya kashe a raunane tace "aikin me akeyi wanda baba yakeyi maka godiya?"yayi murmushi besan sanda ya sunkuya ya mata light kiss a bakinta ba tayi saurin janyewa yace "gidanku nasa ayi renovating"tayi shiru tana kallonsa bata gane ba yace "sorry na mance nasa a rushe gidanku ne a sake muku sabon gini irin na birni na zamani ya kirani yana shedamun an kammala karashene zuwa da safe zasu gama"farin ciki taji ya lullubeta ta soma dariya fararen hakoranta suka bayyana tana kallonsa lokaci daya taji ya samu wani girma a idonta mahaifanta?ya kyautatawa?ya dage mata gira yace "kinji dadi?"ta daga masa kai ya janyota jikinsa sosai hannunsa na kokarin shiga breast dinta ta ture hannun ta zumburo baki "nifa banayin iskanci"dariya sosai ta bashi ya kyalkyale da dariya ya rinka dariya,khairatu na labe a jikin kofar tanajin dariyarsa wani kishi ne ya taso mata ya rufe mata idanuwa ko gani batayi ta soma bubbuga kofar iya karfinta, Sameer da Dina suna can ciki basu saniba ganin bazaa bude ba yasa a haukace ta nufi daki neman wayarta dole yau ya kwanta da ita ko yaki koyaso dan tana kewarsa,
Chapter 29 · 0% Book details