← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 36

Sashe 31

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"mansoor meyasameka haka naga ka rame?"daddy ya tambayesa yana rukosa suna kokarin shiga yace "nadanyi rashin lafiya ne kwana biyu"tare suka Shiga duka kowa ya zauna a parlor, Sameer ya dubi nabeeha wadda keta zuba murmushi yace "ke baki hugging din nasa ba"ta sunkuyar da kai momy tace"to rasa kunya a gabanmu zata rungumesa"sukayi dariya sai lokacin mansoor ya dago suka hada ido da nabeeha,wata faduwar gaba yadanji cikin zucuyarsa yace "hasbunallahu wa niimal wakeel"ita kuwa farin ciki ne ya lullubeta dan sun hada ido tabbas kwallin da ummah ta bata ta tabbatar mata sunan kwallin idona idonka da zarar sun hada ido zai makance da kaunarta zai manta da wata yar kauye,"Barka da zuwa yaya man"tace cikin siririyar muryata ,yayi shiru tamkar baiji ta ba momy tace "mansoor bakaji nabeeha tana maka sannu da zuwa bane?"ya juyo suka kara hada ido ya wurga mata wani kallo wanda yasa ta saurin sunkuyar da kai yace "Barka"yayi mata kyau sosai ya kara kwarjini ramar da yayi tayi masa kyau daddy kare ma mansoor kallo yayi cike da mamaki yace "sameer bakaga abokinka ya canja ba?yayi kamala ya zama kamili tamkar bashi ba injidai an ajiye shaye shaye an dawo da shirin aure?"mansoor yayi murmushi masu aiki keta jera kuloli akan katuwar daddumar da aka shimfida,mansoor ya nisa yace "daddy sauyi kam kaga sauyi canji kuma na canja ciki harda gudunmawar Dina"momy tace "Dina kuma?waye wanan sabon aboki kayi"mansoor ya girgixa kai yace "ko daya Dina....matar da zan aura kenan wadda itace silar sauyin danku,itace silar daina shaye shayena,tabbas daddy na dawo da shirin aure kamar yadda kace ina fatan zaka bani goyon baya yadda na kammala maka wanan aikin nadawo"nabeeha sandarewa tayi a zaune jikinta ya soma tsuma nan da nam taji wani abu ya sara mata a kai kamar gatari duhu ya soma gani a wurin,yanzun dik kwallin da tasaka da turaren data murza a goshinta yadda ummahnta tace hankalinsa da tunaninsa suna wajen wata yar kauye wai ita Dina?Dina?ta maimaita a cikin zuciyarta nan da nam idanuwanta suka cicciko da kwalla ta d'ago kanta suka hada ido da mommy wadda tausayin nabeeha ya kamata tace "nabeeha yi serving din yayyin naki abincin da kikayi musamman dansu?"girgiza kai nabeeha tayi "momy kaina ke ciwo zanje in kwanta"tanayi tana satar kallom mansoor wanda ko kallonta beyi ba idonsa nakan wayarsa hoton Dina ne a fuskar wayar ta wuce jikinta har rawa yakeyi a fusace momy tace "yanzun mansoor ka kyauta abinda kayi kenan?daga dawowarka ka dawo dasaka yarinyar nan kuka?a gabanta kake fadin kanada wadda kakeso?"Mansoor ya dago kai babu ko tsoro yace "au momy kunyarta zanji?wai dama Zaman jirana takeyi indawo ta aureni? she's not serious dama ta tattara tsummokaranta tabar gidan nan Dan wallahi babu mai hanani auren Dina"daddy yayi gyaran murya yace "ya isa haka sauka ga abinci nan Kaci,sameer ga abinci kuci"mansoor ya mike yace "bazanci ba tunda ance itace ta hada abincin zamuje gidansu sameer muci idan bamu samuba zamu eatery"yana gama magana ya wuce abunsa sameer ya girgiza kai yaja gauron numfashi yace "kuyi hakuri momy zai canja tunda ansamu sauyi sosai akansa bari nasameshi, rufaida dafo mana indomie nasan zaici bazai yuwu isowarsa kenan ya zauna beci wani abuba"yabi bayan mansoor,

daddy ya nisa yace "meyasa kikayi magana?aida kin kyaleshi keda kike lallabimsa akan ya aureta?ai a hankali zakibishi matukar kinaso yayi abinda kikeso"momy rai a bace tace "yanzun yayi cim fuska sai inkasa masa magana?ita Dina din yar gidan uban waye?jakar kauye zai kwaso mana?"daddy yace "look hajiya bana bayanki a wanan fadam gaskiya,bazai yuwu ayiwa namiji auren dole ba idan kin matsa ya aureta you will end up jin kunya ni yanzun ganinsa da samun sauyi yasa naji inaso ya auri yarinyar wallahi ki duba kiga yadda ya zama mutumin kirki idan har besamu yarinyar nan ba zai koma shaye shayensa da yawon club da bin mata kinason haka?babu abinda mansoor ya taba nema a rayuwarsa ya rasa banaso a karo na farko a rayuwarsa ya rasa abinda yakeso"shiru momy tayo cike da tashin hankali yanzun da wani ido zata kalli ummahn nabeeha?babbar damuwarta kenan dakyar takai cokali daya na abinci ta mike ta nufi daki wajen nabeeha.....

********
zama mansoor yayi ya dafe kansa kirjinsa nayi masa zafi da radadi sameer ne ya turo kofar ya shigo dakin "Daga dawowarka? kafara batawa da iyayenka akan Dina?wanan shine yakin da kace zakayi ka mallaketa?duba ko abinci fa bakaciba Ranka ya soma baci daga isowarka haba Man ka kwantar da hankalinka mana koka manta kana tare da Amininka ne?"cikim sigar lallashi sameer ke maganar ya zauna gefen masoor ya dago kansa da hannunsa yace "kasani tun muna yara banason ganinka cikin damuwa kamar yadda kaima bakason ganin bacin raina ko damuwata man,meyasa ni zan ganka cikin damuwa nabarka"ajiyar zuciya mansoor ya sauke "I know na fahimci kun kasa fahimtar irin soyayyar da nakeyiwa yarinyar nan ko kasan saboda ita nabaro Cyprus nadawo?"sameer ya jinjina kai idanuwansa suka sauya ya shiga damuwa ganin soyayyar Dina karara a kwayar idon Amininsa tabbas yanason Dina so mai tsanani ya zaiji idan yasan Dina tayi aure?kuma shi ta aura?bazai iya barwa mansoor Dina ba dikda irin kaunar da yakeyiwa Amininsa zai iya sadaukar da komi na rayuwarsa ga mansoor amma banda Dina yau kadai daya kasance da ita ya fahimci irin nishadin da mansoor yasamu lokacin da suke communicating,yana tare da mansoor ne amma hankalihsa gaba daya Yana wajen Dina da badan mansoor zai fito dauka bama da be fito ba yaji dadin kasamcewa da ita sosai"sameer ya naga kamar kanada damuwa ko kai bazaka tayani yakin da zan mallaki Dina ba"sameer ya tsaresa da ido cikin zuciyarsa yace "sorry friend narabaka da Dina domin nima tawa zucuyar in mallaka mata abinda takeso"a fili yace "yeah inada wanda ya Fika ne?kaima bakada wanda ya fini man dan haka ina tare dakai dari bisa dari"suka rungume juna mansoor ya sauke ajiyar zuciya yace "am hungry amma bazanci abincin da waccen jahilar yarinyar tayi ba"be karasa magana ba rufaida ta turo kofar bakinta dauke da sallama da tray da plate da cokula akan kamshi ne ya gauraye dakin cikin sigar tsokana sameer yace "anya bazan daukeki aikin zuwa ki koyawa amaryata girki da kwalliya ba"rufaida ta tabe baki tace "abinda munje gidan da momy"gaban sameer ya fadi bakinsa na rawa yace "kunje kun ganta?"mamaki ya kashe rufaida ganin yadda sameer ya firirice tace "ehh munje amma tana kulle a daki har muka fito bamu samu ganinta ba rowar ganinta kakeyi mana yaya sameer"ajiyar zuciya ya sauke da basu ga Dina ba dan yasan da rufaida ta ganta Tabbas zata tambayeta sunanta zataga kamanninta zata fadawa mansoor,bayason rushewar abokantakarsu yana tsananin son mansoor bayaso akan mace su sami matsala,rufaida taja kofar ta rufe mansoor yace "wai tunanin mai kakeyi haka ne?ka sauko mana muci abincin dakasa ayi"sameer ya sauko ya dauko cokali yana danna waya ya bude datarsa sakon khairatu ya gani take ta fado masa da bukatar ta nason kwana dashi ya dubi mansoor cike da damuwa yace "man....kasan cewa ban auri khairatu ba"da sauri mansoor ya hadiye abinci jin Yana neman sarke masa yace "meyasa?meyafaru?"sameer ya cije lebe dan dole ya sanar masa idan be fada masa be auri khairatu ba zasuje gidan kuma zai ganta a gidan zata iya baro masa aiki yace "ehh saida mukazo aure akayi test akaga tanada ciki"mansoor ya ajiye spooon yace "what?ciki?cikinka kardai kacemun wanan soyayyar da kukesha kasanta q waje sameer karka fadamun kayi zina da khairatu"jikinsa na rawa yake maganar yana kallon kwayar idon Sameer,sameer ya nisa ya seta natsuwarsa yace"ba cikina bane ita dai tasam wanda yayi mata tana nan a gidanmu momy tana rukonta harta haihu a gano wanda yayi mata cikin,kuma kasan har yanzun maitar sona takeyi?"tsaki mansoor yayi yace "har naji na tsaneta dama dik koke koken da takeyi maka akan soyayyarka kuyi aure karyane mazinaciya ce?tou waye ka aura?"gaban sameer ya yanke ya fadi tambayar da mansoor yayi masa ta gigitasa waye ya aura?idan yace masa Dina fa?ya cije lebe idanuwansa jajir yana kallon mansoor ya kasa magana mansoor yace "umhmmm talk waye ka aura?a iya sanina baka da budurwa sai khairatu kamar yadda a iya saninka kasan babu wadda zucuyata keso sai Dina"shiru sameer yayi ji yayi idonsa sun cicciko da hawaye tabbas yayiwa abokinsa laifi na aure masa Dina da yayi amma yaya shi zaiyi da son nata da yakeyi?
Chapter 31 · 0% Book details