Sashe 1
Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[07/11, 16:57] 😍Slim girl❤️: 💥 *MAZA BIYU....*💦
*NA:SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33
*marubuciyar:*
*K'ADANGARUWA*🦎
*RUD'ANI*💥
*DUHU.....*🌑
*1*
Hannunta dafe da kuncinta, batare da yabari ta dawo hayyacinta daga azabar data sauka a tsakiyar kwalwalwarta ba, cikin zafin nama ya ƙara sauke mata wasu tagwayen maruka, yana nuna ta hannu ya ce "How dare you talk to me like that eh? Sai na kashe ki a banza na kashe jakar ƙauye babu abinda uban wani ya isa ya yi, empty head" Sameer ya riƙe hannun abokin nasa yana dukan kafaɗar shi ya ce "Common my friend, akan wannan kake ɗaga jijiyoyin wuya?" A fusace Mansoor ya ɗaga hannu ya ce "Sam, barni irin jakan ƙauyen nan maganin su kaci uban su" Cike da tsiwa hawaye na zuba a kuncinta, amma bata karaya ba DINA ta ce "Kaci ubanka dai, nawa uban ba zai taɓa ciwo ba, daman daka ganinka maye ne kai wlh" Sam ya saki baki yana kallon Dina ganin bakinta yaƙi mutuwa, Mansoor wanda ake masa laƙabi da Man ya ce "What!" Sai kuma ya yi kanta, da gudu ta take ƙafafuwanta ta ruga a 136 tana cewa "Ohho dai kaji da warin wiwinka....."
cikin zafin nama samir ya rukosa wanda tuni dariya ta cika masa ciki ya cafko mansoor da jikinsa ke rawa kamar mazari yace"calm down man ya karamar yarinya kamar wanan zaka bita?idan ka bita me zakayi mata?bayan kaine zaka zama abin kallo a cikin garin nan dubeka fa?"samir na nunasa da yatsa ya cigaba da magana "karka zubar da class dinka akan DINA kaji abokina kaima narasa dalilin dayasa kake shiga sabgarta"wani kallo mansoor yayi masa batare da yace komi ba kawai ya jinjina kai saidai kallo daya zakayi masa kasan cewar yana cikin tsananin bacin rai yayi fushi,samir murmushi kawai yayi dan yasan man bazai taba magana ba yayi mamaki ma da har yayi musayar wadanan words din da Dina shida maganarsa ma in kana tare dashi zaka iya kirgawa kasantuwarsa miskili marason magana da izza,....wucesa yayi kawai magana kasa kasa kamar bayaso yace "kasameni a mota"be jira mai samir zaice ba yayi gaba abinsa yana bin yaran dake tsaitsaye suna kallonsu da wani irin kallo mai cike da kyama yana mamakin meye abun kallo a wajen su?bude motarsu yayi ya zauna a mazaunin mai zaman banza ransa a bace yake idanuwansa sun kada sunyi jajir kansa ya dau carji maganganun DINA ke yawo a kwakwalwarsa"kaci ubanka dai daga ganinka maye ne kai nawa uban bazai ciwo ba...mai warin wiwi"ransa ya kara baci ya runfe idonsa ita yake gani lokacin da take fada masa wadanan maganganun tunda yake wata mace bata taba masa kallon banza ba ballantana ta daga harshenta ta zagi ubansa......DINA....ya furta a zuciyarsa,yaja gauron numfashi ya sauke yayi murmushin gefen fuska kamar yadda ya saba kuma dabiarsa ce koda yana cikin bacin rai,
Sam kuwa shafa sajen fuskarsa yayi ya saki lallausan murmushi yace "DINA Akwai karfin hali amma burgeni kikayi inason mace mai courage"ya cije lebensa yana bin yaran wajen da kallo ya hangi wata yarinya tsaye ta tsaresa sa ido kamar zata cinyesa,murmushi yayi mata ya yafitota da hannunsa ta juya zata gudu ya karasa da sauri "dakata babu abinda zanyi miki kinji tambayarki zanyi ina ne gidansu DINA?"yace yana murnushi ganin dik yadda ta tsorata yasan halin yan kauye,
cikin hausarta ta kauyawa tace"can ne gidansu bari muje in nuna maka amma kada kace nice na nuna maka kaji?"jinjina mata kai kawai yayi yana murmushi burinsa kawai yasan gidansu dan tunda suke haduwa da ita bai taba sanin gidansu ba gashi yau sun kwashi kallo da mansoor beyi hira da itaba yana kewar hirarta da wawtarta, haka suka taka dik inda suka gifta su ake kallo,
Mansoor dake cikin mota na mamakin ina kuma sam zashi?yana kokarin kunna wiwi a hannunsa ya janyo wayarsa zai latso numbersa kiran da ya shigo wayarsa ne ya kara bata masa mood yayi jifa da wayar gefensa ya kwantar da kansa jikin kujerar motar yana sauke numfashi minti minti yana zukar wiwi.....
******
"Dina meyasa kikeso ki rinka saka kanki a matsala?yanzun gashi saade tace taga lokacin da kika zagi wadanan yan birnin guda biyu da suke zuwa gidan gonar nan dake bayan gidan mai gari?meyasa kika zageshi?har ya mareki?dubi yadda yatsunsa suka fito a gefen kumatunki?ko kin manta matsayinki ne?babanki ba kowa bane a garin nan face mai facin tayar mota ni karki daukomin masifa"innahrta cike da fada takeyi mata magana,
dina tadan tura baki tasa dumamen tuwo a gabanta ta gagara koda gutsurar loma daya tsananin takaici da bakin ciki yasa wasu sabbin hawaye masu zafi ke kara zubo mata daga kyawawan feraren idanuwanta masu daukar hankali,dikda haka bakin Dina be mutu ba "Innah ubana fa ya zaga harda cewa sai ya kasheni fa wai yaga wanda ya tsayamun harda zagina yayi da turanci ya fadi wasu maganganu"ta zumburi baki,innah ta tabe baki tace "koma meye yayi miki kece kikaja tunda kike shiga sabgarsu tunda ai ana ganinki da dayan aka fadamun dik garin nan labarinsu akeyi baa san daga ina suke ba kuma an tabbatarmun kina zuwa wajensu to ki shiga hankalinki tunda har maganar kisa ta shigo ciki"kwafa DINA tayi "innah ba abinda ya isa yayimun in turanci yake takama dashi nima ai baba yace zai kaini makaranta in zama likita"innah bata kara saurarenta ba ta dauko bokitin ruwan data ja a rijiya ta soma tatar kullun koko,
sallamar yarinya ce ta sa innah juyowa "ke yau bazamu siyi gyadar ba anata ciki wanan zamanin waye yake ta maganar siyen gyada?"girgixa kai yarinyar tayi tace "ba gyada na kawo ba wai DINA tazo inji wani balarabe"
"balarabe?kodai wanda ta tsokana ne ya biyota ya kasheta?"innah jikinta ya soma rawa,zumbur DINA ta mike taci dammara da dankwalin ta ta dauki tabarya "koni koshi a garin nan idan be kasheni ba ni zan kasheshi "DINA ta fice bata jira mai innah zatace ba hanlalin innah ba karamin tashi yayi ba tayi jifa da abun tatar koko ta soma salati tana kwalawa DINA kira,ko saurarenta batayi ba sai surutai da takeyi,
Sameer na tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa yana facing kofar gidansu tun daga jikin labulen buhu yake hangenta ya soma tuntsirewa da dariya yana hango abinda ke hannunta Yana kara kwashewa da dariya yace "DINA...ho"yana murmushi tana yaye labulen buhun tace "ina yake dan wiwin nina fishi..."kasa karasawa tayi ganin samir tsaye yana tuntsurewa da dariya,sakin tabaryar tayi tana murmushi tana kici kicin kwance dammarar da tayi "ah ah Dina kinyi shirin fada ne?"ta zumburi baki cike da shagwaba tace "ehh mana ba yace kasheni zaiyi ba?"tayi farr da ido ya kurawa fusharta ido yadda tayi jajir ga shacin hannun mansoor kwance a fuskarta cike da tausayawa yace "taho nan kawata DINA zo inji na biyoki ne nayi bikonki sam bazan juri zama nikadai batare da kawar hirata ba"
tad'an washe baki tace"Allah dagaske?"gira ya daga mata yana murmushi ta hararesa"kaima bazakayi magana bane irin na abokinka kurma?"tuntsurewa da dariya yayi yace "nasan sai kin magantu yanzun dai nazo bikonki kizo muje wajen hirarmu"
"Allah ya sauwake inje ya dukeni ya kasheni?bazanje ba banason ganinsa"bata fuska samir yayi ransa yadan sosu ganin haka yasa DINA tadan natsu "banason kina fadin haka akan abokina kinsam yadda nake tsananin kaunarsa kuwa?"ta ware ido. ta harde hannuwanta a kirjinta tace "saika fada ku Yan biyu ne?"girgiza mata kai yayi yace "ko daya mu abokai ne aminina ne inajin tsananin kaunarsa mudin abu daya ne da Ruhi mabanbanta abinda ya bambantamu kenan kowa nada gangan jiki da ban da ace gangan jiki daya ne da nafi farin ciki babu abinda zai rabamu"murmushi tayi ta fahimci akwai tsananin shakuwa da kauna a tsakaninsu saidai sunada banbanci wajen halaye,
"Yanzun dai ki gafarci abokina ki yafe masa marukan da yayi miki kinji?"ta tabe baki kamar zatayi kuka tace "da zafi fa?"cike da shagwaba tayi maganar,ya zuba mata manyan idanuwansa yana murmushi yace "nasani kiyi hakuri da wanine yayi miki marin nan da zan rama miki amma bazan iya rama miki marin nan ba sakamakon Man ne yayi mikisu?"tace "meyasa?"
"saboda idan na maresa tamkar kaina na mara"tayi yar dariya tace "shikenan muje"ya jinjina kai yaja wata sassanyar ajiyar zuciya,suka jera innah ta fito da sauri ta kwala mata kira "DINA ina zuwa?"murmushi Dina tayi mata tace "ba dadewa zanyi ba yanzun zan dawo"cike da ladabi sam ya gaida innahr DINA sanan suka jera tabi bayansu da kallo cike da fargaba da tsorom kada yaudararta sukeyi su aikata mata wani mugun abin tasan halin DINA sarai gabanta na faduwa ta juya ta Shiga gida....
******
daga cikin motar ya kure kida yana bi a hankali idonsa a lunshe hannunsa rike da wiwi yaji ana kwankwasa glass din windown motar dan tsaki yayi yasa hannu ya rage wakar sanan ya bude motar a fusace yaga waye,sam ya gani tsaye da Dina tana ta dariya sun shagala suna dariya ransa ya baci ya tsaya yana kallonsu saidai gabansa ne ya yanke ya fadi idonsa dayayi tozali da shacin hannunsa a kumatunta,ya lura hira sukeyi basusan ya bude ba hakan yasa yayi gyaran murya,take dukkansu suka tsaida dariyar da sukeyi sam ya nisa yace "ohh ashe ka bude nayi tunanin baka bude motar ba bakaji ba ai"DINA ta dan yatsina hanci warin ya dake hancinta tasa hannu ta rike hancinta tana mazurai,wani kallo mansoor keyi mata wanda taji kamar ta saki fitsari,da sauri ta cire hannunta daga hancinta taji kawai yayi kwafa yace "ashe kinada tsoro"ta murguda masa baki kawai,yayi dariyar gefen fuska ya juya yana fuskantar sam yace "yadai what do you want"girgiza masa kai kawai yayi "nadauka baka ciki ne ka Shiga gida ai shiyasa"ya jefa masa wani kallo "kadameni dayawa"mansoor yace yana satar kallon DINA samun kansa yayi da son kallon kwayar idanuwanta,juyowa tayi suka hada ido yana kallonta take ya kauda idonsa gefe daya yace"sai ka shigo bari na Shiga ciki yau zamu koma?"yana tambayar Samir ne cike da isa da gadara,
"yadda kace"samir na murmushi cike da zolaya yace "kardai wanan fad'an ya rikide ya koma soyayya",
wani kallo yayi masa,kawai bece komiba yayi gaba abinsa,