← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 36

Sashe 12

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hankalin mansoor ba karamin tashi yayi ba yace "what?aura miki wanan gajan?"ta jinjina kai idonta ya kawo ruwa tace "bazan auresa ba saboda mahaifina bayason hadin,innah ta ce keso saboda shidin yaron yayarta ne"Mansoor ya cije lebe ransa ba karamin baci yayi ba ta kalli window din sanan ta dubesu ta kasa fada masa me takeso,kafeta da ido yayi yace "inada feelings akan akwai abinda kikeson fadamun"ta sunkuyar da kai cike da kunya tace cikin zuciyatta taya zan fara fada masa ya dorani ta window din nan in dura?,katseta yayi "mu zagaya naga shigarki cikin gida"da sauri ta girgiza kai "kinajin tsoron a ganni tare dake a fadawa mahaifinki anga mashayi a kofar gidansa?"girgiza kai tayi tace "ko daya kawai dai da zan fito ba ta kofar gidanmu na biyo ba na taho wajenku"cike da mamaki mansoor da sameer sukace "ta ina kika biyo?"tana murmushi ta nuna musu window din dukkansu dariya sukayi mansoor mamaki ne da al'ajabi yasa ya kara bin window din da kallo,

"kina nufin durowa kikayi kikazo wajen man?"sameer yayi maganar cike da tsokana,tura baki tayi zatayi kuka da sauri mansoor yace "ya isheka Sameer"gimtse dariyarsa yayi sameer ya juya kiran khairatu ya shigo wayarsa,

"yanzun in daukeki in doraki kenan."ta gyada masa kai,murmushi yayi ya matsa daf da ita yana kallonta itama shi take kallo cikin wani irin yanayi kallom da yakeyi mata yasa ta runtse idonta cike da kunya,hakan ya bashi damas sa hannu daya ya dagota ya tallabota ta kasa da dayan hannunsa ya dorata saman window din dai dai nan sameer ya juyo,sakin baki yayi yana kallon yadda mansoor ke rike da dina tana kokarin direwa,da sauri ya kashe wayarsa ya soma musu video tana kyalkyala dariya shima dariyar yakeyi yace "sai nauyin tsiya me kikaci haka kikai nauyi?"tayi murmushi tace "awara"tana fadan haka ta rike wayarta da kyau ta Dira cikin dakin yana juyowa yaga sameer na dariya ya hade rai yace "muje"suka soma tafiya.....

murmushi Dina kawai takeyi tana sauke ajiyar zuciya bayan dirarta cikin daki,bugun kofar dakin yasa gabanta ya yanke ya fadi ta sauke ajiyar zucuya tace "nagodewa Allah yasa nadawo da badan hakan ba da asirina ya tonu"tace a fili da sauri ta bude akwatin garwarta ta tura wayarta ciki sanan ta cire hijab dinta ta cire dankwalinta ta bude kofar dakin tana murtsika ido,saida gabanta ya fadi ganin baba kulu da su tasiu tare da innahrsa "na fada muku ba Dina kuka gani ba Dina tana cikin daki kaga ma bacci ta tashi kungani"wani kallo baba kulu keyiwa Dina sanan ta dubi tasiu da idonsa daya ya kumbura yayi baki kamar wani abu ya cijesa tace "kace kaga Dina da wanan yaran yan iska na birni"kallon Dina tasiu yayi cike da mamaki yace "wallahi naganta a gabanta ya mareni har sau biyu saboda ita har ya kumburamun fuska sanan da bakinta tace ko zan mutu bazata aureniba data aureni gara ta mutu batayi aureba"Innahr Dina ta dubeta tace "wai haka Dina tsakaninki da Allah nasan bakya karya koda kuwa laifi kikayimun"Dina gabanta ya fadi tabbas batayiwa mahaifiyarta karya amma yau ce rana ta farko da zatayi dan ta kare kanta "innah nifa ban fahimci abinda suke fada ba wadanan dan ni yanzun na bude kofa bacci nakeyi tundazun da baba yazo ya fita ta ina suka ganni?tayaya har nayi musu magana kurwata ce tazo?"ta karasa maganar tana harararsu duka,innahr tasiu tace "kinga in zakuba yaron nan yarinyar nan kubashi idan bazaku bashiba ku fada mana kawai mu cire rai da aurenta,inma bashi dinba mezaiyi da Dina yar dake yawo da yan iskan birni yan shaye shaye,waye yasan ma me sukayi da ita ragowarsu zai aura"Dina ta harzuka tace ko kuma ni in auri ragowar yan talla ba,wanda kuke zargin dan iska ne shi ba dan iska bane kuma yabar shaye shayen a dalilina"innahrta ta kai mata duka a baki take taji wani zafi ya ziyarceta ta rike bakinta tana baka musu harara tasiu kuwa kwafa yayi yace "zasuga abinda zanyi musu"ya juya da tawagarsa sukayi gaba sukabar baba kulu da mahaifiyarsa da innahr Dina suna magana,Dina furucin mansoor ne ya dawo mata kada su tasiu suje wajensu sukai kansu dan tabbas bata yarda da furucin mansoor ba ta juya ta koma daki....
*******
mansoor na rike da waya yana sauraren rufaida cike da rudani yace "ohhh really shirin aure da nabeeha akeyimun?tou wallahi bazan aureta in tafi kasar waje da ita ba babu inda zani "yana maganar ransa a bace rufaida ta nisa "na fada maka ne dan ka shirya domin nasan baka sani ba amma ya man Dan Allah kada momy tasan nina fada maka"ta marairaice jinjina mata kai kawai yayi "ok"ya katse wayar sameer dake sauraren komi yana gefensa ganin yadda mansoor ya Shiga damuwa yasa shima ya Shiga "common kai fa namiji ne meyasa zaka Shiga damuwa?babuwanda ya isa yayi maka auren dole beside idan bakason nabeeha ga Dina mana"da sauri mansoor ya kallesa "yess ga Dina ko zakacemun ba sonta kakeyi bane?man kanason Dina tunda har ka iya kasa sukuni saboda ita mansoor ka fadamun abinda ke cikin ranka akam Dina"ajiyar zuciya mansoor ya sauke ya zauna akan sofa ya dafe kansa sameer na tsaye yana kallonsa,ya mike da sauri ya bude jakar daya zuba kayan shaye shayensa ya shiga cirowa da sauri sameer ya rikesa "lafiyanka?maganar aura maka nabeeha ce tasa zakayi shaye shaye bayan ka tabbatarwa da Dina ka daina hakan yasa ta amince da kai a matsayin aboki bayan nasan ba abokantaka bace soyayya ce?"girgiza kai yayi "bazan taba iya daina shaye shaye ba na fada mata ne kawai dan ta Amince dani domin ina tsananin bukatarta a kusa dani halayenta da dabiunta suna sakani nishadi, kasancewa da ita na samu natsuwa da kwanciyar hankalin,infact Dina is my peace of mind"murmushi sameer yayi mansoor ya bude kwalba daya ya shiga sha yana lumshe ido sameer na tsaye ya harde hannunsa a kirjinsa kalaman mansoor keyi masa yawo akai,yana fadin itace peace of mind dinsa amma yace ba soyayya sukeyi ba?yana nan tsaye har mansoor ya shanye kwalbar ya janyo tabar wiwi ya kunna ya soma zuka yana busar da hayakin idanuwansa jajir ya kalli sameer "da kake maganar in auri Dina tayaya?ka manta da kiyayyar da mahaifinta keyi mun?ko ka manta ne in tuna maka?baxan taba zuwa in durkusa in rokesa akan yarsa ba beside Dina ba aji na bace yarinyar data taso a kauye ta girma a kauye batasam komi ba"

"idan haka ne saika hakura ka auri zabin iyayenka nabeeha tunda tana sonka kuma kun dace"tsaki mansoor yayi "zabin momy ce ita bana daddy ba kuma bazan aureta ba bazan taba auren nabeeha ba dik su gama shirinsu akai zuwa lokacin da zan koma zan rusa musu plan"murmushi Sameer yayi "amma kasan momy bazata amince da yar talaka bakauya ba?"

"wai kai waye yace maka inason Dina?how many times zan fada maka canjata nakeso nayi?look babu soyayyarta a tare dani banajin hakan babu alamun kaunarta a zuciyata"shiru sameer yayi tabbas mansoor ya bashi tausayi sosai yana tsaka mai wuya ya kasa amincewa da yanason Dina amma tabbas soyayyarta ke dawainiya dashi,hayaki ne cike da dakin lokacin da sukaji motsi ta ta cikin gidan,kallon juna sukai sameer yajiyo muryoyinsu take ya gane su tasiu ne ya karasa yaja labulen window din ya gansu ya juyo yace "man mutuminka ne suka biyomu su dau fansa"yayi mgnr yana dariya mansoor ya mike yace "good ya kawo kansa kira su captain dake baya suna ba dabbobin can abinci da masu tsaro su kamasu su dauremun su"sameer ya jin jina kai cikin seconds ya kira captain ya shaida masa,

tasiu na kokarin ciro wuka ta baya yaji an cafkeshi yana juyawa yaga sojoji cikin kaki sun zagayesu sameer ya kalli mansoor sukai murmushi suka saki labulen.....
*******
misalin karfe goma na dare Dina na kwance a daki tayi shiru tunanin kudin da mahaifinta yazo dashi yace sameer ne ya bashi takeyi me hakan ke nufi?sunba mahaifinta kudi ne dan wata manufa? Mansoor take tunani tayi murmushi shine ma zaiba Sameer dan yaba mahaifinta,meyasa zaiyi haka?matsalar sa shaye shaye kuma ya daina tasan babanta zai amince da abotarsu matukar ya bari,

mansoor wayarsa ya ciro a jikin carji ya kalli sameer ya tabe baki yana waya da khairatu "malam da mun koma ayi maganar aurenku kawai ba sai ka jirani ba wanan soyayyar da kukeyi tsaf zaka haikewa yar mutane"ya daura fuska mamakin maganar mansoor sameer yakeyi be tanka masa ba yana murmushi ya kwanta ya ciro wayarsa,

"wanan village girl din ko tayi bacci oho"yayi dialing numberta daya sa mata a wayar,

wata zabura Dina tayi jin wani vibration a cikin a kwatinta ta dafe kirji gumi ne ya shiga karyowa a goshonta "maciji nashiga uku a cikin a kwatina"wani fitsari taji yana naiman kufce mata ta Shiga sintiti cikin dakin,can taji shiru wayar ta katse,

tsaki yayi ya sake dialing a karo na biyu "common ki dauka Dina ki dauki wayar nan i cant sleep without talking to you common"Sameer ya kallesa ya girgiza kai,

a hankali ta taka gabanta na faduwa ta leka akwatin wayar tagani tana haske,dafe kirji tayi ta runtse ido ta sauke ajiyar zucuya ta waiga jikin window kar innarta basuyi bacciba taga ba kowa sai hasken farin wata ta dauki wayar ta kara a kunne "ko kinyi bacci ne in barki"yace cike da isa,

girgiza kai tayi kamar yana ganinta "banyi bacci ba ya man....."yadda ta kira sunansa yasa ya mike zumbur ya zauna ya murtsuke idonsa "mai kikace?maimaita abinda kika fada kinji ya man...."ji yayi tamkat tafi kowa Iya kiran sunansa shiru tayi tace "nifa kabani tsoro na dauka maciji ne ya Shiga akwatina ashe waya ce dan gab nake da fita in taso baba da innah a shigo a fitar mun dashi"wata dariya ya kwashe da ita yace "really?"shiru tayi dan bata fahimci me yake fada ba,

"da kin kwabsa da mahaifinki ya gani da ya kwace da kinjamun wata sabuwar tsanar"shiru tayi jin abinda yace dukkansu basu sake magana ba gajiya yayi yace "meye labari Dina "
Chapter 12 · 0% Book details