← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 36

Sashe 5

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

komawa nabeeha tayi ta zauna jagwab akan kujara ta dafe kai tace "village girl?"ta maimaita kanta na sara mata "waye village girl?"tambayar da tayiwa kanta kenan cike da tsananin kishi ta yunkura ta mike tana wasa da yatsunta "kardai yayi budurwa a kauye"wani abu taji ya caketa kamar mashi take kishi ya rufe mata ido kenan wajen budurwa yake zuwa?kamar mansoor ya rasa waye zaiso sai a kauye?da sauri ta bawa kanta amsa "no no its wont happen,nikadai zaiso saboda shikadai nakeso bazai taba son wata yar kauye ba,momy bazata barsa ba dan babu abinda momy ta tsana take kyama sama da talakawa,balle ace yar kauye ce?dole zata sa masa ido ta gano who's that village girl he's talking about wadda ta fita iya shagwaba.....
*******
tare suka shirya suka fito suka gaida momy sanan sukai mata sallama kamar yadda suka saba shirin office da fita tare sukeyi dikda kowa yana aiki a kanfanin babansa ne Sameer matawalle matashi ne kuma da daya wajen mahaifinsa wanda yake tsananin so yakeji dashi dik abinda Sameer keso shi akeyi masa,a kofar kamfanin matawalle Mansoor yayi parking "thank you driver idan an tashi zakazo ka daukeni ko insa driver ya kawoni office dinku?"mansoor ya jinjina kai yace "yadda ka gani,lets see dai idan ban tafi kauye naga wani sakarci waccen yarinyar keyi ba"fuskarsa a daure yayi maganar,samerr mamaki ne ya cikasa kafin ya dakatar dashi yaja motar ya barsa nan tsaye,ransa yadan sosu ya tsaya yaji me zaice be tsaya ba,me zaijeyi kauye wajen Dina?koda yake bazata sauraresa ba dama zama yayi ya nemi yardarsa ya kama kafa ta wajensa,ya kada kai kiransa zanyi karyaje ya lalata komi nafiso na lallaba masa ita,yayi tsaki ya nufi hanyar da zata sadashi da ofishin mahaifinsa,ko wace hanya yabi gaisuwa akeyi masa cike da girmanawa sameer kenan matashi maiji da kudi da naira wadda dik abinda yasa agaba yakeso cikin kankanin lokaci sai ya samu,

tura office din mahaifinsa yayi ya shiga cike da girmamawa ya gaishesa ya nemi kujera ya zauna "yadai Sameer ina abokin naka?bezo ya gaisheniba ya wuce ko?"sameer yayi murmushi "nasan meyake gudu"

dariya abban sameer yayi yace ",gudun in tambayi yaushe zaayi aure akeyi ko?nagaji da ganinku haka gaskiya musamman kai Sameer gara mansoor yanada yan uwa amma kai bakada kowa kai kadai gareni ina bukatar kayi aure dan insamu jikoki"shafa keya sameer yayi yace "soon Abbah ina gab da gabatar maka da matar da zan aura cikin kankanin lokaci,"farin ciki ne ya lullube Abbansa yace "dakyau da nayi Maka gagarumar kyauta"sameer dariya yayi ya janyo takaddun da abbansa ke jira yazo yasa hannu ya soma sama musu hannu daya bayan daya yanayi amma zucuyarsa na wajen mansoor Amininsa kiran khairat ke shigowa wayarsa ya saci kallon mahaifinsa ya cigaba da sa hannuna takaddun....

********
Tunda ya hango mahaifinsa da wasu maaikata guda biyu gabansa ya fadi irin kallon da sukeyi masa da irin hararar da daddy ke watsa masa yasa yadanji tsoro amma dayake namijin duniya ne hakan be nuna a fuskarsa ba saima kara daure fuskarsa da yayi tamau tamkar be taba dariya ba haka ya karasa inda suke cikin ladabi ya gaida mahaifinsa ba yabo ba fallasa daddy ya amsa sanan yace "shiga office ka jirani"ya kalli daddyn zaiyi magana yace "nace ka shiga office ka jirani ko?"ransa ya dan baci taya agaban wadanan maaikatan daddy zai masa tsawa?,bece komiba yasa kai ya wuce ko waigensu beyi ba ya bude office din ya Shiga yana bin ko ina da kallo yayi tsaye ya zura hannunsa a aljihunsa,ya kalli agogon dake manne a jikin bango kusa da tankamemen hotonsa dana daddynsa gefe hoton daddy ne da governan garin,ya danyi tsaki "nifa banzo office din nan da niyyar zama ba fita zanyi"be rufe baki ba daddy ya shigo dauke da sallama yana bin mansoor da wani irin kallo shekeke ganin haka yasa mansoor zama a daya daga cikin kujeru bakaken dake zagaye da table din daddy "ai na dauka a tsaye zaka tsaya kana jirana ka nunamin ka kai karshe a rashin kunya"wata ajiyar zuciya mansoor kawai yaja ya sauke ya durkusar da kansa batare da yace komiba saidai cikin zucuyarsa na azalzalar sa to meye yayiwa daddy haka?maganar daddy ce ta katse sa "mansoor nagaji da halayenka na wulalanci da tozarci abun har ya kai kan yar gidan danmalilki?"sai lokacin mansoor ya dago kai ya kalli daddy,,"kalleni da kyau jiya kacemun kana gidansu sameer abokinka yau kuma Alhaji ibrahim dan maliki ya kirani akan yarsa fatima Da ka mara a mashaya jiya inda kasaba zuwa ko?"

"Daddy....tafada abinda tayimun"

"babu ruwana da abinda tayi maka dan nasan halin isarka da izzarka ina jiye maka ranan da zakayi danasanin wanan halin naka,na gida baka barmu ba na waje ma haka,nayi nayi ka kawo matar aure kaki to bari kaji wanan yarinyar daka mara itace sadakin aurenka dan ita zan aura maka tunda bakada mutunci"....cikin ko in kula mansoor yace "bana sonta bazan aureta ba....inada...."sai kuma yayi shiru daddy ya tsura masa ido yana karantarsa akwai abinda yakeso ya fada saboda miskilanci da zurfin ciki irin nasa ya kasa karasawa "kanada wa?kanada wadda kakeso?"girgiza kai kawai yayi ya mike "ina kuma zakaje?munada aiki dayawa yau a office dun nan koma ka zauna"

"Daddy sameer zanyiwa rakiya yana jirana"shiru daddy yayi yana kallonsa yanaso ya gano wani abu a fuskarsa tamkar akwai yar damuwa amma ya kasa gane hakab,"bazan hanaka ba tunda sameer ne amma dik inda azahar tayi maka kazo kasameni ina jiranka"murmushin nasara mansoor yayi ya dibi makullan motarsa daya dire a table din daddy da wayoyinsa ya fice daddy ya girhiza kai yace"Allah ya shiryamun kai mansoor amma tabbas aure zanyi maka dan shi ya dace dakai'daddy ya janyo wasu files da aka ajiye masa ya soma duddubawa....

*******
cike da mamaki Dina ke lallon mansoor wanda ke zaune a saman mota a kofar gidansu yara sun dajiye motar sunata kallonsa, tsayawa tayi daga gefe yace "yadai ki karaso mana ko ance miki cinyeki zanyi?ko wani abu zanyi miki?"ya tsura mata ido tadan kauda kai ta murguda masa baki sanan ta matso taku daya,
shiru yayi mata bece komiba ya cigaba da danna waya kusan minti goma sha biyar tana tsaye tana kunkuni,dakyar cikin fushi tace "malam ni zan koma gida dan inada abinyi innah taje cin kasuwa tana gab da dawowa tasani inyi mata tatar kunun tsamiya da tatar awara babu wanda nayi kana batamun lokaci na tambayeka ina abokina samir bakacw komiba"ta zumbura baki,

"nace ki matso kinki matsowa ni kuma bazan rinka magana ina daga murya ba ba dabiata bace yanzun ma kin karyamun doka banayiwa mutum magana sau biyu akan abu dayax"shekeke ta kallesa sanan tace "saikace wani sarki ko basarake ni kafadamun meye ya kawo ka ko kazone yau din ma ka tabamun hannuna,yauwa Allah ya isa yabamun hannu da kayi ranan"dariya ce ta kamasa ya soma yar dariya fararen hakoransa suka bayyana wadanda suka kara masa kyau da kwarjini dimple din gefe da gefen fuskarsa suka lotsa,Dina sakin baki tayi tana kallonsa yayi matukar mata kyau tamkar balarabe da take gani a TV gidandu innahrta lubabatu kanwar mahaifiyarta,ganin yadda ta tsura masa ido yasa yace "lafiya?"dariya ta kwashe dashi "ashe kana dariya na dauka mugunta rka bazata barka yin dariya ba"shi dai bece mata komi ba,ganin yayi shiru yasa ta matsi daf dashi tace "gani nan to meya kawoka kayi abinda ya kawoka ka kama yan matan kafafuwanka kabar gidan nan kafin innah ta tadawo kajamun bala'i"dirowa yayi daga saman motar saura kiris ta kwasa aguje ta dauka dukanta zaiyi taga ya tsaya dab da ita tana jin saukar numfashinsa,yanajin nata kamshin turarensa take shaka cikin wani irin yanayi tace "kamshin nan akwai dadi"

"thank you,yauwa Dina ko?"yace yana daga gira, cikin kosawa tace "ehh ina jinka nifa dik na kosa katafi dan kar shaye shayenka ya motsa kayi mana a kofar gida idan baba ya dawo aka bashi labari yankani zaiyi,kasan babana beda wasa"sai surutu takeyi dik ta cikasa da magana babu full stop ransa yadan baci cikin daga murya yace "shout up haba you like talking to much dina baki lura banason yawan magana ba?"shiru tayi tana kallonsa cike da mamaki "yauwa nazo ne nima na kulla abota dake dan inason na canjaki Dina"yace cikin wani irin yanayi,cike da mamaki da al'ajabi take kallonsa shima ita yake kallo tayi masa kyau sosai dikda kayan jikin nata kayan Fulani ne yau amma tayi masa kyau fiye da ko yaushe Hatta kitson kanta na fulani ne gashin nan sun xubo gaban kirjinta da bayanta ga wani sihirtaccen kyau dake futa a fuskarta tasha jan janbaki,"umhmm talk kiyi magana zaki abota Dani?"cikin marairaicewa yayi maganar besan yayi ba,yana kallonta ya daga wayarsa ya kashe mata hoto tayi matukar kyau daidai ta dago manyan idanuwanta,

daure fuskarta tayi tamau tace "abota dani dakai?Allah ya kiyaye inyi abota dakai ni Dina dama abinda ya kawoka kenan?to ka tattara yan matan kafafuwanka kabar kofar gidan nan tun kafin in tara maka jamaa,ni bazan taba abota da dan shaye shaye ba mai isa da izza da mulki irinka ni Dina, niba kowa bace face mahaukaciya kamar yadda ka zageni,sanan kayi ikirarin kasheni,koda kaga na tsaya ina lallabaka ne dan karka fito da wuk'a ka lumamun a cikina"tana gama maganar ta watsa masa wani kallo wanda ya kasa fassara maanar kallon ta kada kanta ta shige cikin gidansu ta rufo kofar langa langar dake kofar gidan,cikin sauri ya karasa yana bubbuga kofar "Dina Dina ki bude kofar ki saurareni"
Chapter 5 · 0% Book details