← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 36

Sashe 15

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hakimi yace "tou kai yaro wace alak'a ce tsakaninka da Dina din?soyayya kukeyi aurenta zakayi ka kaita birni ko yaya?"mansoor yayi shiru gabansa na faduwa ya juya ya kalli Dina wadda ke tsaye kamar an dasata hawaye ke zuba a idanuwanta kamar am bude famfo ga majina dake zubowa daga hancinta, runtse idonsa yayi ransa na kuna ganin tana hawaye bayan baya son kukanta ko kadan,"tambayarka mukeyi"hakimi ya dawo da tambayar dayayi masa,

"Ehh sonta nakeyi da....."kafin mansoor ya karasa mahaifinta ya daukesa da Mari"sonta kakeyi da aure zakace ko?"mansoor ya dafe kuncinsa yanajin wani radadi a kwakwalwarsa a karo na farko a rayuwarsa da aka maresa tinda uwarsa da ubansa suka haifesa baa taba marinsa ba yau gashi akan Dina mahaifinta ya maresa yau da wanine ya maresa bashiba da sai yasa an kashesa har lahira,kallon mahaifinta yakeyi cike da mamakin yadda ya zabga masa mari be Bari ya jira yaji sonta yakeyi da mene ba? so yakeyi yace sonta yakeyi da abota amma ya maresa?"karya kakeyi kaso yata dama abinda nakeson ji kenan kuma naji ya tabbata maganar da innahrta ta fada ta zama gaskiya to kasani bazan taba baka yata ba harabada kuma yadda ka kangarar mun da ita ka sauya ta kotu ce zata rabamu dakai,kuma ka gaggauta fitomin da yara ka jira goron daurin auren Dina"idanuwan Mansoor sun kankace tsananin takaici da bacin rai duhu kawai yake gani a gabansa besan lokacin da dakyar ya motsa bakinsa ya kwalawa Sergent kira ba,cikin sauri yazo "jeka fito da yaran can"yana gama maganar ya mike ya cigaba da tafiya Dina kuwa ji tayi kamar kasa ta bude ta shiga menene laifin mansoor dan ya kaunace ta? ashe sonta yakeyi dagaske?ta lumshe idonta ta soma takawa mahaifinta ya daka mata tsawa "ina zakije?zaki bishi ciki ne ya koya miki sauran iskancin da be koya miki ba?dawo ki tsaya a nan"jikinta na rawa ta dawo mansoor ya juyo ya kalleta tausayinsa ne ya kamata ta rushe da kuka ya juyar da kansa idan ya cigaba da tsayuwa a wajen tabbas zai iya illata mahaifin Dina zai iya kauda soyayya,da Abotar dake tsakaninsu ya bar masa tabon da bazai taba mantawa dashi ba,suna tsaye aka fito da tasiu wanda dik sun galabaita tasiuu a wuyace yace "dama kina nan?kince ya daina shaye shaye?tou me yakeyi jiya daddare da yau da safen nan?"cije lebe tayi ta danne zucuyarta da takeji kamar ta tsunka masa mari tace "karya kakeyi baya shaye shaye ya daina a ta dalilina saidai nasan rabashi dani zai iya maidasa halin da yake ciki"tasiu zai sake magana baban ya hanasa "rabu da ita idonta ya makance amma zanyi maganin abun ka kwantar da hankalinka zan aura maka ita cikin satin nan"Dina jikinta ya soma rawa dakyar take taka kafarta tana biye dasu har gida.....
******
sameer gyara zama yayi a gaban momynsa ya kurbi juice yace "momy nasan kinyi farik ciki sosai da jin labarin zanyi aure da wadda zan aura ko?"momy ta kara fadada murmushinta sosai tace "kwarai dagaske kaga zumunci zai kara kulluwa tsakanin mu ban taba kawowa khairatu kakeso ba sameer kayimun ba zata" murmushi Sameer yayi yace "mansoor nakeso muyi tare dashi amma abun da kamar wuya"momy tace "kamar yaya bayan hajiyar ta aikomin akan an tsaida lokacinsa da nabeeha?"shiru sameer yayi kamar ya sanarwa da momynsa maganar Dina amma gudun halin Mansoor yaja bakinsa kawai suna cikin maganar kiran mansoor ya shigo wayarsa,

"yadai man yanzun muke maganarka da momy Dan halak kaki ambato"momy tana dariya tana kallom Sameer gyara zama yayi jin yanayin muryar mansoor yace cikin rudewa da damuwa "lafiya meya faru?"Mansoor muryarsa a shake cikin tsananin bacin rai yace "ka dawo please i need you by my side inaso ka fadamun alamomin soyayya"hankalin sameer ya tashe yace "yeah dama naso biyawa gidanku na gaidasu momy ne amma ganinan zuwa yanzun zan kamo hanya kaji?ka kwantar da hankalinka ina tare dakai kadafa ka damu kaji?"ya mike zumbur "momy zan tafi akwai yar matsala tare da man"momy tace "tohhh meyafaru inji dai ba ciwonsa bane ya tashi"kada kai yayi"ko daya momy babu komi i will handle it"momy tace "tou Allah ya tsare ka kula da kanka sanan gobe zan karasa gidan ummahn khairatu din idan mahaifinka ya dawo zamuyi magana zan kiraka"yace "badamuwa"cikin sauri ya fice hankalinsa a tashe yake burinsa kawai ya ga mansoor yasan halin da yake ciki....

*****
"Dina kinbani mamaki ban taba zaton wani zaizo ya batamun tarbiyyarki ba, dik irin yadda kikejin maganata kinsa kafarki kim shure tunda kika hadu da wanan majanunin yaron to kisani babuke babushi dukkansu kar insake ganinki da daya daga cikinsu,sanan maganar sakaki a secondary da kuma karatun da kikeso kiyi na sokeshi"da sauri ta durkushe a gaban mahaifinta "kayimun rai baba idan mansoor kakeso na rabu dashi zan rabu dashi zanyi yadda kakeso amma inaso kayimun uzuri guda daya banaso na zama silar tarwatsewar rayuwarsa bayan nice nayi silar shiriyarsa mansoor mutumin arziki ne wallahi,kuma yana so.....n"kasa karasawa tayi ganin yadda mahaifiyarta ke kallonta cike da takaici tace "innah ki sa baki kada baba ya rabani dashi nasaba dashi sosai naji bazan auresa ba amma inaso ya bari muyi rabuwar mutunci sanan banason auren tasiu gara ya nemi wani ya auramunshi"innahrta batace komiba saboda takaici baba kuwa can kasan zucuyarsa kuna takeyi masa shi kansa baasom ransa zai aurawa Dina tasiu ba da wani zai fito maganar aurenta ko waye zai aura masa ita amma banda mansoor banda abinda ya shafesu,cikin zucuyarsa yace "Allah ga yata nan a hannunka banason aura mata wanda surukata keson aura mata nabar komi a hannuka"yana gama adduar ya mike innah ta nisa tace "zakaje wajen mai gari ne akan a kira iyayen yaran nan subar garin nan kuma su fita a sabgar yarinyar nan ko?"baba yace"ehh can zani akan maganar ansamu number mahaifin takadirin za kuma a kirasa a fada masa komi sanan ayi masa tsakani da Dina"Dina idonta jajir take kallon mahaifinta wanda bakinsa ya bushe ya kamata ace yana wajen facin tayarsa amma yana gida akan maganarta,yunkurawa tayi ta mike zata shiga daki,"ina zaki?"innahrta tayi mata magana cikin tsawa,cak ta tsaya batare da ta kalleta ba tace"dawo nan ki zauna kusa dani dan idan kin shiga dakin bansan menene zaki aikata ba kila ya baki siddabarun da kikebi ta jikin bango kike tafiya wajensa ki zauna ina ganinki a nan sanan ga dan wakenki nan har ya sandare tun safe bakici komiba kokon da kika kai daki ma kuda ke binsa gashican"ajiyar zucuya ta sauka ta koma ta zauna ta tasa robar dan waken a gaba tunanin mansoor takeyi tasan bacin rai na saka shaye shaye Allah yasa ba shaye shayen yakeyi ba,ko wani hali yake ciki oho,taso ace ta Shiga daki ta kirasa ta jadadda masa yadda ta damu dashi ta fada masa damuwarta amma ba dama saidai akwai dabarar data fado mata wadda zatayi amfani da ita wajen Yin magana dashi,ajiyar zucuya ta sauke tana tsananin kewarsa ta lumshe idonta shi take gani lokacin daya dorata akan window yanayi mata tsadadden murmushinsa....

*****
koda Sameer ya iso ya samu Mansoor a buge yasha yasha har ya gaji kwalabe ne a gabansa ga hayaki daya turnuke dakin,"kai man zaka kashe kanka meyake faruwa haka?ya naganka cikin wanan yanayin?"idonsa jajir yake kallon sameer dake kallonsa cike da rudani ya fuzge kwalbar daya dauko zai bude ya cillar gefe yace "wanan itace soyayyar da kakeyiwa Dina?"zuba masa ido mansoor yayi sameer ya cigaba da magana "tabbas son Dina kakeyi zan fada maka gaskiya ko kaki ko kaso man,saboda haka ka dawo hankalinka mu nemi mafitar yadda zaayi ka mallaketa"mansoor ya zuba masa ido cike da kunci yace "menene alamomin so?"sameer ya nisa yace "alamomin so dik sun bayyana a gareka man,abinda nake guje maka tun farko kenan gashi ya faru saida na tabbatar maka da sonta kakeyi kaki amincewa gashi da kanka kanaso ka gane haka,alamomin so sun bayyana a tattare dakai,yawan ambato,kulawa, damuwa da damuwat abinda kakeso,kishi da tausayi"

"duka inayiwa Dina?"ya tambayi sameer a sanyaye,sameer ya jinjina kai "Duka kakeyi mata man,harda wanda ban fada ba,yanzun fadamun meye ya faru bayan tafiyata in nema maka mafita?"shiru mansoor yayi bayaso ya tuna yau mahaifin Dina ya maresa akan yarsa a karo na farko a rayuwarsa,nan da nan ya sake ganin duhu ya mamaye ganinsa ya runtse idonsa gamm cikin takaici yake bawa Sameer labarin abinda ya faru da furucin da yayi yanason dina da....basu bari ya karasa ba,sosai sameer ya tausaya masa yace "man inaso ka yarda kanason Dina sosai so bana wasa ba tunda har mahaifinta ya mareka baka aiwatar da komi ba"mansoor ya jinjina kai yace "na Amince tabbas ina sonta kuma na shiryawa yaki akanta"

"dakyau mutumina"Sameer yace yana murmushi "dan ko akwai yaki sosai a gabanka dan tabbas zaku kara da mahaifinta sosai da kuma momy da mutanen gidanku,yanzun abu daya nakeso nabaka shawara shine kayi dik yadda zakayi kafin kabar garin nan ka kafa soyayyarka a zucuyarta"mansoor ya tsurawa sameer ido yace "tayaya?bayan mahaifinta ya tabbatarmun da zai aurawa wancen jakin ita?ai inaga karshe sace yarinyar nan zanyi"da sauri sameer ya tarbi numfashinsa "karma ka fara"kiran wayar daddynsa ne ya shigo wayarsa suka kalli juna "daddy"mansoor yace a dan tsorace ganin kiran daddy a wanan lokacin,sameer yayi kasa da murya yace "ka dauka mana"shiru mansoor yayi haka kawai gabansa ya Shiga faduwa,dakyar ya danna recieve,

Daddy dake zaune a babban parlor yasa wayar a speaker dukkansu suna parlorn cike da damuwa da takaici musamman momy wadda kad'a kafa kawai takeyi "Daddy...barka"yace murya ciki ciki take daddy ya fahimci a buge yake a kausashe yace "mansoor meye ya hadaka da yar masu garin nan?"damm gaban mansoor ya fadi a karo na farko,suka hada ido da sameer daya zaro ido waje,
Chapter 15 · 0% Book details