← Book details Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 36

Sashe 6

Maza Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"bazan bude ba kabar wajen nan kafin babana ya dawo"ya cigaba da bubbuga kofar yana jiyo sautin wakarta,yasan leka ta jikin ramin kofar gidan ya ganta tsaye kanta babu dankwalin kitson kanta ba karamin daukar hankakinsa yayi ba ta juya baya tana tatar koko....ransa ya baci ya kaiwa iska naushi "why mansoor.....meyasa kazo wajen wanan mahaukaciyar kauyen?ga abinda tayi maka nan"cikin fushi ya nufi motarsa da sauri ya bude ya shiga ya rufo motar yana huci cike da tsananin bacin rai tunda yake mace bata taba fada masa abinda Dina ta fada masa ba.....yasa key a motar ya tada motar har zai tafi ya kasa zucuyarsa nayi masa zafi da tsananin takaici ya kashe motar ya kifa kansa akan sitiyarin motar yaga hakan bazai masa ba ya bude wani akwati dake gefensa ya ciro wata kwalbar magani ya soma sha ya dauko karan tabar wiwi ya kunna ya dume cikin motar sha kawai yakeyi idanuwansa sun kada sunyi jajir,bayan ya gama ne wani irin bacci mai nauyi ya daukesa ya kofa akan sitiyarin motar....
*******
sameer Kiran mansoor yaketayi shiru dik ya shiga damuwa dikda yasan inda yaje hankalinsa na wajensa magriba ta gabato be gansa ba kuma yasan baya office to yasan gida ya tafi amma meyasa zaitafi gida be biya ta wajensa ba bayan yasan baya iya good two hours basa tare? tsaki yaja ya kwalawa driver kira "isyaku....dauko makulli kazo ka kaini gidansu man"yace yana kallon kaiwa da komowa cikim sauri isyaku ya dauko makulli "muje ranka ya dade"isyaku ya budewa Sameer mota ya Shiga mazaunin baya ya rufe sanan ya zagaya ya tada motar suka kama hanyar gidansu mansoor,

khairat ke faman kiran wayar sameer ya kasa dauka hankalinsa a tashe yake besan wani hali mansoor ke ciki ba koya dauki wayarta bazata gane kansa ba yanzun,

"kana nufin megadi mansoor be dawo gidan nan ba?"daddy ke tambayar me gadin gidan yace "ehh ranka ya dade,tou kenan shifa sameer wani waje sukayi"yana cikin maganar mai gadi yaji horn din mota ya juya da sauri ya wangle katon gate din gidan saiga bakar motar Sameer matawalle ta shigo daddy yace "au kaga gasu ma aina dauka wani wajen yaje yau ma"sameer ne ya fito daga motar yace "barka da dawowa daddy"

"barka dai Sameer yanzun nake cigiyarku kaida abokinka ashe kuna hanya shi be gadamar fitowa daga motar bane?"gaban sameer yadan fadi ya sosa kai yace "nikadai ne daddy"

"Kai kadai?ina mansoor din bayan tun shigarsa office yace zashi wajenka kana jiransa?ina kuma yayi sameer nasha fada maka kasa ido akan mansoor da wanan shaye shayen nasa a matsayinka na amininsa ka kasa canjashi"sameer yayi shiru kenan dagaake mansoor kauye ya tafi wajen Dina?daddy ya katsesa "ya ina magana kayi shiru kafasan inda yake"

"daddy am dama inaga ya biya karbomin magani ne dan gida ya ajiyeni dama bana dan jin dadi nadauka gida yayo shine na biyosa"daddy kwafa kawai yayi yabar Sameer nan tsaye sameer yace "why mansoor..... kana wajen Dina ina kiranka baka picking?mansoor kodai son dina kakeyi?"tambayar da yayi a fili kenan ya koma mota cike da takaici da bacin rai tayaya zai rinka kiransa baya daukar waya bayan a tarihin abotarsu dik halin da daya ke ciki bayakin daukar wayar daya?haka driver ya juya dashi ya nufi gidansu.....
******
sameer na gefen momynsa yayi shiru tun dawowarsa ya tasa ta a gaba tana lura da yanayinsa "sameer lafiya naganka haka?ko akwai abinda ke faruwa ne?"girgiza mata kai yayi "babu momy kawai inaso in fada miki zanyi aure"da sauri momy ta kalli sameer sanan ta rangada wata irin guda tace "Alhamdulillah Allah ya kawomu ni zainabu aure sameer?"cike da farin ciki take tambayarsa sai yace "aure kuma?ninace miki zanyi aure?"yace a fili cikin zucuyarsa yace nayi magana a raina ta fito fili menene yasameni ne?tambayar da yakeyiwa kansa kenan kardai shaukin khairat ke neman haukatasa, ya mike yabar momy a wajen baki yaki rufuwa cikin farin ciki ta soma danna numbobin daddyn sameer dan ta labarta masa wanan labari mai dadi....
*****
"bawan Allah me kakeyi a nan ne haka bakasam dare yayi ba inji dai ba wani abun dina tayi muku ba?"mahaifin dina ke magana rike da buhunsa ya dawo daga bakin hanya,mansoor ya fito daga motar idonsa jajir warin tabar wiwi ta bugi hancinsa yadan baza hancin ya shaka tabbas wari ne wanan kamar na abun maye ya kara lekasa cikin wani irin yanayi baba ke kallonsa saidai wanan karon daura fuskarsa yayi tamau jin warin da mansoor yakeyi "ka rasa ina zakayi mana shaye shaye sai kofar gida?me kake nema a kofar gidana?"gaban mansoor ya fadi ya kalli mahaifin dina yaga yadda yake jifansa da kallo cike da kyama da fushi yace "wajen Dina nazo?"

"wajen dina?"baba ya maimaita cikin fushi yana kallon mansoor wanda shima shi yake kallo cike da fargabar irin kallon da yakeyi masa ya kasa kara furta kalma daya kawai yasa kai ya nufi cikin gida yana kiran sunan DINA......

*SLIMZY*✍🏻
[09/11, 09:04] 😍Slim girl❤️: 💥 *MAZA BIYU....*💦

*NA:SLIMZY*✍🏻
Wattpad@slimzy33

*Marubuciyar:*

*K'ADANGARUWA*🦎

*RUD'ANI*💥

*DUHU....*🌑

*4*
Dina tasa hannunta a cikin kwanon tuwo miyar kuka da yaji man shanu kenan ta gutsuro tace "innah tuwon nan dadi zaiyi kodan yunwar da nakeji yasa nakosa na kaisa bakina"innah tayi yar dariya "tou wai dik me kikeyi yau Dina bakici komiba?"ta kai lomar bakinta bata tauna ba baba tagani a gabanta kamar an jehosa ya zabga mata wani gigitaccen mari wanda ta kidime ta furzo tuwon daga bakinta lomar na kokarin shaketa ta dafe kumatunta "ke waye yace ki dauko dan shaye shaye ki kawoshi kofar gidan nan?a wanan daren? Kenan ya tabbata maganganun da mutane keyi mun ana ganinki da yan birni masu shaye shaye ko"girgiza kai tayi tana hawaye tace "bansanshiba baba nifa Sameer kadai nasani ni bana"ya kara wanketa da mari ta gefen fuskarta sanan yasa hannu ya fuzgeta yayi waje da ita,cikin alhini da damuwa innah tace "Dina bakyajin maganar mahaifinki nima dana dawo kasuwa saida nace waye ya ajiye mota a kofar gidan nan amma kikace baki saniba gashi ai kinjawa kanki maruka har biyu wanda tunda na haifeki babanki be tabayi mikisu ba"innah ta koma ta zauna ta rafka tagumi,

mansoor na tsaye yana jiyo ihu dina da hargowar baba jikinsa ya soma rawa ya fito da dina dafe da fuskarta tana kuka yace "gashinan kinganshi kikace baki sanshiba?"ta daga manyan idanuwanta da hawaye ke gudu a fuskarta kamar an bude famfo fuskarta tayi jajir ta kalli mansoor wanda tuni jikinsa ke tsuma ganin hawaye a idon ta ga yadda fuskarta tayi pink nan da nan ba karamin daga masa hankali yayi ba ya kalli mahaifinta ransa a bace idonsa jajir kansa na kara daukar carji, saidai ya danne hakan a zucuyarsa jikinsa na rawa yace "baba meyasa ka daketa?Dina batasanniba bata taba ganina ba yau tafara ganina, nazo wajenta batada laifi, da tsayuwata a kofar gidanku,ko kasan cewar da wanine ya daketa ba kaiba da sai nasa an dauresa?saidai kash kaidin mahaifi ne a gareta dani kaina kanada ikon hukuntamu nida ita amma da badan haka ba....."galala Baba yayi yana kallon mansoor take ya tuno da fuskarsa yana nunasa da yatsa yace "ashe kaine?kaine kazo har kofar gidana kakemun shaye shaye?ashe bakada kunya bakada tarbiyya?idan niba mahaifinta bane kasheni zakayi ko zakasa akaini kiri kiri ne a jefar da dan makulli. cikin kogin maliya?"cikin fushi Baba ke magagar dina kuwa kallon mansoor takeyi cike da mamaki da karfin hali irin nasa, yadda shima kallon nata yakeyi ta cikin hasken farin wata,hade hannuwansa biyu yayi alamar bada hakuri yace "am sorry....nine naja miki ko?bazan sake zuwa ba dikda manufata akanki ta alheri ce"yace yana kallonta da idanuwansa da suka kankance da tsananin bacin rai ga kansa dake sara masa

"bakada wata manufar data wuce ka lalatamun yarinya ka lalata mun rayuwarta Karna kara ganinka tare da ita dan bazan bawa mashayi yata ba kuma bazan zuba ido inaji ina gani ka lalatamun tarbiyyar dana bata ba gashi kasa na sauke hannuwana akanta bayan tunda na haifeta ban taba dukanta ba"cikin kuka Dina tace "nasanshi baba"da sauri Mansoor ya shiga girgiza Mata kai cikin tausayawa bayaso a taba lafiyarta ta cigaba da magana "nasanshi amma abinda kake tunani bashi bane shidin mutumin kirki ne kuma bashida wata matsalar daya wuce shaye shaye"

"shaye shaye babbar matsala ce Dina in kina ganinta karama banaso mu cigaba da musayar miyau dake a kofar gida waiga kiga yadda kika taramun mutane".....yana gama magana ya fuzgi dina yayi hanyar shiga gida da ita mansoor yace "idan shaye shaye matsalata nadaina daga yau"da sauri Dina ta waigo tana jifansa da wani irin kallo mai cike da tausayawa hannunta ta daga ta baya alamun bye bye...jijiyoyin kansa dik suka firfito "Dina......"ya furta ya koma ya fuzgi motarsa kamar zai tashi sama aguje yara ke gudu sunayin baya ganin kurar data tashi ta baibaye mutanen wajen,

"malam kayi saurin yanke hukunci akan yaron nan bayan shine wanda ya taimakeka da kudin nan"shiru baban dina yayi cike da bacin rai yake musamman yadda jamaa sukayi cincirindo akofat gidansa yasan yanzun zaa fara maganar nan zata dauka a cikin gari....
*******
"wai nikam ina mansoor ko gidansu sameer ya kwana jiya banga dawowarsa gidan nan ba"cewar momy data samu rufaida da nabeeha a parlor da zaheed sanye da uniform din makaranta yana breakfast,

"momy be kwana ba kila yana can tare da village girl"da sauri rufaida da momy sukace "village girl"nabeeha idonta jajir ta jinjina musu kai "tabbas da bakinsa ya fada"take fuskar momy ta sauya nan da nan annuri. fuskarta ya sauya daga faraar da takeyi zuwa akasin haka a fusace tace "village girl?mansoor din?wacece wanan?yar talakawa?"ta jero wadanan tambayoyi. zaheed ya ture cup din tea yace "momy naga kamar ya Mansoor yana dakinsa ya dawo"

"ya dawo?"rufaida da momy suka hada baki,bata jira me zasuce ba ta shiga bin benen gidan cikin sauri fuskarta a daure take taka benen gidan zucuyarta cunkushe da bakin cikin jin abinda Mansoor ke shirinyi, hayewa sama tayi,
Chapter 6 · 0% Book details