Sashe 8
Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daga haka ya kashe wayan yana fita a ɗakin zuciyarsa na tururi da kuna akan wannan abin data masa, don haka cikin ransa yake raya dole ya nuna mata kuskurenta a wannan karon. Da safe ta farka ta ganta ita kaɗai babu ma alaman ya kwana a ɗakin, se kawai ta taɓe baki ai dai ko babu komai ta tsira daga takurawansa da ba sosai yake barin tayi wani baccin kirki ba. Don haka wanka tayi tayi sallan subhi ta shirya cikin shigar wasu riga da wando palazzo's cubeb. Se ta kawo wani himar irin robo robo ɗin nan ta ɗora kan palazzo's ɗin ta fito, bayan ta dudduba wayanta bata kalla ba, baya parlour ko kitchen don haka kai tsaye ta bishi zuwa dakinsa sedai nan ɗin ba baya nan, gaba ɗaya baya gidan don haka cikin hanzarin karta yi let wurin aikinta ta ɗiba cake da biscuit ta zira a handbang nata ta fita, yau ma ba aikin dare bane da ita don haka tana isa ta kama aiki. Amma time to time tunanin wayartan da bata gani ba kan fado mata, bayan sallar zuhr dai ta gasa samar nutsuwa ta amshi wayar pooja ta ƙira No nashi, amma yana ta ring be amsa ba, short message ta aika masa cewar ita ce yayi answering call nata, kamar da 2 minutes ta sake kira amma No answer. Dole ta haƙura ta kyaleshi tana ayyana baƙar zuciyar ta motsa kenan. Se wajajen 8 na dare take komawa gida lokacin harya jina da shiga gidan shi, yana zaune a parlour yana kallo ta shigo a gajiye sosai, a gabansa ta zube dama takarmi da guntun shimar nata a hannu ta shigo dasu. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa yana kuma ƙoƙarin zame kanta daga jikinsa data ɗora, kanta ta ɗago ta kalleshi tana furta... "Besty yau duk me ya faru ne?, banga woyana ba na ƙira ka data Dr pooja har test messages na ma amma No answer lafiya kuwa?..." Hummmm ya kawo wani gauren numfashi yana ƙarasa zamar da ita daga jikinsa yace. "Yanzun kin kyautama kanki kenan meenor?, duba kalan shigar da kika fita dashi, ina ma laifin kici gaba da saka bubu ɗin kina fita dasu kiyi rolling vail na kayan, bayan haka yanzun ke abin birgewa ne a gareki kiyi video da karamar riga har kiyi status dashi, wasu can su ɗauka su ɗora a group naku da kuke haɗe maza da mata uyhmmmm?. Duk sabbin halayen da kike ta bijiromin dasu inata ƙoƙarin shanye wa sabo da ina SONKI Meenal, amma duk na miye waɗan nan ababuwan?...." Kanta ta dafe tana furta "Ohhh shit dama nayi tunanin hakan wllh" se kuma ta taso gaba ɗayanta tana shigewa jikinsa tace "I'm so sorry Dear, Amma ai naga na kare jikin nawa, kuma ma ai nake kallar hakan ba laifi bane, ni wllh ma sabo da kai ne nayi video's ɗin, idan kana wasu ababuwan se kace wanda be gama wayewa kodai yake da ƙarantar wayewar kan.... Tin da ta fara maganar yake kallonta da kaifafan idanunsa ko fiftawa bayayi, wato ma ita hakan ba komai bane a wurinta, har yana faɗa mata abinda tayin ba daidai bane amma take ƙiran sa me ƙarancin wayewa?, Lallai ya riga yayi saken da Meenal ɗin ta gama rainasa. Amma duk da hakan se ya danni zuciyarsa yana ɗago fuskanta ya riƙe a cikin tafin hannuwansa ya furta. "Ki gyara!, ki sake halaye da ɗabi'unki Meenor!, ina SONKI ba zan iya ɗaukar waɗan nan sabbin halayen naki ba, Pls ki taimaki wannan zuciyar dame zuciyar...." Yayi maganar deep down na bugun zuciyarsa na sake ƙaruwa, daga yanda take lafe a jikinsa tana jin yadda zuciyarsa ke beating very fast akai akai. Tashi tayi ta nufa ɓangarenta wanka ta fara kafin tayi sallan magrib da isha'a da batayi ba duk ta haɗe su a lokacin, wasu riga da wando masu taushi ya saka tana baje jikinta ta turare ta nufa ɓangarensa, zuwa lokacin har ya bar parlourn,yana kwance idonsa bisa p.o.p na ɗakin yana kalla kamar me nazartan wani abu daga cikin sa, be ji shigowarta ba sejinta kawai yayi a jikinsa ta wani faɗo masa, ƙanƙameta yayi da hannunsa yana cusa kansa cikin wuyarta ya wani shaƙi numfashin daya tafi may da mayen ƙamshin ta me bala'in rikitasa. Anan wurin ya zubar da duk wasu makaman yaƙinsa yayi yaƙin gaskiya da gaskiyar da babu saussauci ko sauƙi na ragwanta tattare da shi, amma kuma akwai sanya nutsuwa da nishaɗin hakan tattare da lamarin. Washe gari babu aiki weekend ne, don haka daga shi har ita suka mora wunin ranar da ƙaunar junansu, tuni harya mayar mata da wayarta bayan ya sake roƙon ta da karta sake don ALLAH. Washegari daya kasance Lahadi kuma ta tambayi gidansu,don kawai kewar Shareefah da tayi da kuma Yaya Sadeeq ɗin ta, sha biyu daidai ya sauƙeta a gidan yace after isha'a ze dawo ɗaukanta. Wata leda ya bata yace ta shiga musu da ita, godiya ta masa yana shirin komawa motarsa sega Yaya Sadeeq ɗin ma ya fito tare da Baffansu, fasa shigar yayi yana dawowa ya tsugunna ya gaida Baffan dake tai masa godiya, kafin ya bama ya Sadeeq hannu su gaisu yana jan sa cikin motar shi kuma Baffan suna komawa ciki shida Meenal ɗin, babu jimawa sega Ya Sadeeq ɗin shima ya shigo kafin Gwaggo Sadiyan data matsu da a buɗe ledan ta muskuto tana cewa a buɗe ledan mana.... Komai babu wanda yace mata taja ledar daidai damin kuɗi sabbin ƴan ɗari biyar biyar na faɗowa, daidai kuma da shigowar Shareefah tare da Bilkisu wacce take ƴa ga gwaggo Sadiya, duk su biyun a guje suka taho suna rungumeta da faɗin..... "Oyoyo Yayarmu🫂...." Suka faɗi kowa na sake rungumeta da murna, a cikin ledan kuwa kayan fruits ne da nama me uban yawa, kuɗin kuma pakege ne da 100k dake da Yaya Sadeeq a wurin shi yasa gwaggo Sadiyan ta tura kuɗin ga Baffa tana cewa. "Kai Ma sha ALLAHU babu abinda zamu ce da wannan yaro se godiyar ALLAH, ALLAH dai ya saka masa da alkhairinsa ya bashi masu masa shima, Malam kawo dubu biyar se Bilkisu ta sawo lemu muci da naman...." Ya Sadeeq ne ya buɗe aljihun gaban rigansa ya zaro 2k ya bama Bilkisun yace ta amso na hakan ai ze isa, duk da bata so hakan fa amma haka ta kyale bayan yasha wata uban harara a fakaice. Daga nan ya Sadeeq ɗin da Baffan suka fita don ƙirar sallar karfe ɗayan da ake ta kira, suna fita gwaggo Sadiya taja wata tsuka tana tashi ta bar musu wurin, wajajen ƙarfe uku shiru shiru Meenal taga ba'a ɗora sanwar dare ba, don haka ta fito bayan ta yi shara a gidan ta sake tarar da gwaggon nayi...
"Sannu da gida gwaggo amma ai nayi sharar É—azun babu jimawa." In wurin ya tankata to ita ma ta tanka, yi tayi kamar ta juya se kuma dai ta danni zuciyarta ta sake cewa.
"Gwaggo me za'a É—aro a gidan ne?"
Meenerl É—in ta faÉ—a tana me sunkuyar da kanta kasa, saboda sanin halin mebi yanzun ma ba wai ya zama lallai bane ta tanka mata. Gwaggo Sadiyan kuwa data wani É—an ya nutsa fuska kafin cikin halin ko in kula ta ce....
"Dake da can ma ai kene kike min aikin ko?..."
Da idanu kawai Meenal ta bita kafin ta sauƙe ajiyar zuciya, kafin ta dawo daga duniyar tunanin daya faɗa, ta tsinkayi muryan gwaggon nasu na cewa....
"Sumumu kasau, rasa kunya ɓeran tanka...."
Tasan da ita take amma se komai bata sake ce mata ba ta nufa Dakin Shareefah bayan ta sauƙe wata ƙaƙkafar ajiyar zuciya, kafin a hankali
kuma wasu abu me kana da siraran hawaye masu sanyi taji suna zubowa daga cikin idanunta, tana tunowa da Mahaifiyarsu, Ammeyn su mutum me nagarta da sanin ya kamata, da haka ta koma É—akin nasu ta kwanta wani abu me kama da kewa na taso mata irin na uwar da aka rasa mahaifiya kuma jigon rayuwarsu.....
*BY AMMEY LAYLERH âœï¸*
08104493215
*༺ƘARSHEN ƘADDARA•â—à¿*
ð™ˆð™–ð™§ð™®ð™–𙢠ð™‰að™¨ð™šð™šð™§ ɱⅈð”¯ð”¯É‘Ò»
_ð˜¼ð™ˆð™ˆð™€ð™” ð™‡ð˜¼ð™”ð™‡ð™€ð™ð™ƒ_
Unexpected and Surprising 🔥💥
ð™”ð™Šð™ð™‰ð™‚ ð™ð˜¼ð™‡ð™€ð™‰ð™ð™€ð˜¿ ð™’ð™ð™„ð™ð™€ð™'𙎠ð˜¼ð™Žð™Ž.
Page 5&6
♡ ♡ ♡ ♡
"Sannu da gida gwaggo amma ai nayi sharar É—azun babu jimawa." In wurin ya tankata to ita ma ta tanka, yi tayi kamar ta juya se kuma dai ta danni zuciyarta ta sake cewa.
"Gwaggo me za'a É—aro a gidan ne?"
Meenerl É—in ta faÉ—a tana me sunkuyar da kanta kasa, saboda sanin halin mebi yanzun ma ba wai ya zama lallai bane ta tanka mata. Gwaggo Sadiyan kuwa data wani É—an ya nutsa fuska kafin cikin halin ko in kula ta ce....
"Dake da can ma ai kene kike min aikin ko?..."
Da idanu kawai Meenal ta bita kafin ta sauƙe ajiyar zuciya, kafin ta dawo daga duniyar tunanin daya faɗa, ta tsinkayi muryan gwaggon nasu na cewa....
"Sumumu kasau, rasa kunya ɓeran tanka...."
Tasan da ita take amma se komai bata sake ce mata ba ta nufa Dakin Shareefah bayan ta sauƙe wata ƙaƙkafar ajiyar zuciya, kafin a hankali
kuma wasu abu me kana da siraran hawaye masu sanyi taji suna zubowa daga cikin idanunta, tana tunowa da Mahaifiyarsu, Ammeyn su mutum me nagarta da sanin ya kamata, da haka ta koma É—akin nasu ta kwanta wani abu me kama da kewa na taso mata irin na uwar da aka rasa mahaifiya kuma jigon rayuwarsu.....
*BY AMMEY LAYLERH âœï¸*
08104493215
*༺ƘARSHEN ƘADDARA•â—à¿*
ð™ˆð™–ð™§ð™®ð™–𙢠ð™‰að™¨ð™šð™šð™§ ɱⅈð”¯ð”¯É‘Ò»
_ð˜¼ð™ˆð™ˆð™€ð™” ð™‡ð˜¼ð™”ð™‡ð™€ð™ð™ƒ_
Unexpected and Surprising 🔥💥
ð™”ð™Šð™ð™‰ð™‚ ð™ð˜¼ð™‡ð™€ð™‰ð™ð™€ð˜¿ ð™’ð™ð™„ð™ð™€ð™'𙎠ð˜¼ð™Žð™Ž.
Page 5&6
♡ ♡ ♡ ♡