← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 36

Sashe 11

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga yanayin yanda tayi maganan cikin muryar kuka ne yasa idanun Yayan nasu cikowa da nashi hawayen shima, Saboda yafi kowa sanin iriyar tsananin SO da ƘAUNAR dake tsakanin Shareefah ɗin da kuma ameenatou ɗin.
Hannunsa yasa ya ɗan dafa kafaɗanta cike dason kwantar mata da hankali yace. "IN SHA ALLAHU babu abinda ze faru da Meenal, wannan ɗin ma kamar kuskuren tane ta amsa daga Ubangijin ta, idan tana da rabon shiriya daga wasu daga cikin halayenta shikenan ta rabauta ranar gobe kiyama..... Jiya jiyar nan na gama magana akan ire-iren shigar da take yi wanda be dace, amma haka ta kaɗa kunnenta maganganun nawa suka wuce ta bayan kunnenta, ita rudin sauran Dactor's na ɗibarta, da yin duk abinda suka ga dama, wanda a yanzun mafi yawancin abinda Dactor's sukafi yi kenan, duk shigar da suka ga dama daga Matan Aurensu har ƴan matan cikinsu, suna ɗaukar hakan a matsayin wata waye wace ta zamani da tazo musu, se dai suna aikata kuskure ne ba tare da sanin suba, lokaci suka nema kuma ALLAH ya basu sedai su sani. Daga lokacin da shi wannan lokacin ya gama kare musu daga nan na ALLAH ke farawa, don faɗin sane hakan domin shi da kansa yace....Yaku bayin ALLAH, ku ji tsoron ALLAH, tsoro na gaskiya domin tsoron ALLAH shi ne ginshiƙin rayuwa mai albarka, shi ne hasken da ke shiryar da zuciya a cikin duhun duniya, Ku kusanta kanku gareni ku nisanci duniya, domin duniya tana wucewa ne kamar mafarki. Abin da muke gani yau gobe zai zama labari tabbas, duk wata ɗaukaka zata barmu, dukiya za ta bar mu!, mukami zai gushe mana, kamar yadda in mun mutu mutane za su manta da mu. Amma aikin da muka yi domin ALLAH shi kaɗai ne zai tsaya tare da mu a kabari, ya kuma ci gaba da ribanya bayan koda ta hanyar kwatance da halaye na gari ne, yana cewa kada mu yaudari kanmu da buri, alhalin mutuwa ko ƙaddara basa taɓa tambayar shekaru ko matsayi da girman ikon mutum , aikinsu kawai suke gudanar akan duk wanda ya bari son zuciya da duniya suka gama rinjayarsa. Inda yake mana nuni da kamar yanda da yawan wasu mutanen sun fita daga gidajensu da safe lafiya lafiya ne, amma ba su dawowa da yamma sabo da amshi abinsa. Ko anan ya kamaci ace duk bawa me tunani me kyau ya tsaya nazartan shin, me na tanadar ma kaina wa ranar da za mu haɗu da ALLAH?, se dai kash bamu tunanin hakan sabo da duniyar kaɗai muka sa gaba, inda yake cewa da zaku gyara zukatanku kafin tsayuwa ranar hisabi, Ku kuma yawaita istigfari, ku kuma koma ga mahaliccinku da tuba na gaskiya, ku darajanta jikkunanku da kun sama babban sakamako a ranar gobe kiyama, kuyi gaggawar tuba a gareni domin ni me gafara ne, ku dena koyi da shigar arna, koyi koyi da abinda addininku ya baku ba na wasu ba, dana azartaku da manyan hijjaban da zasu kare duk haufi naku a ranar gobe kiyama.... Amma Meenal taki ganewa Shareefah, ra'ayin nasara sun rinjayi nata ra'ayin, tabbas wannan aikin nata be jawo mata komai ba face taɓewa da lalacewa mara ƙarshe da kuma tushe...
Ashe don ALLAH yace ka suturce jikinka ba ni'ima bace, yanzun ni nan dake dake nan wurin,duk mun tsaida hujja a kanmu, ita Rayuwar duniyar da muke kallo tamkar zubin dashi ne, iyaka kirki ko zunubin da muka aikata su zamu samu, domin kuwa dama ALLAH (S.W.T) cewa yay mana damu, rayuwar mu ta nan gidan duniya kamar mun zo munyi shuka ne, can kuma shi ne ranar abinda zamu girba , amma duk da zuciyoyinmu sukan rinjayi ra'ayoyin mune daga tafarki na gaskiya zuwa tafarkin ƙarya da burge wasu dabbobin mutanen da sune ALLAH ya ware ya mana misali dasu...... Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³ yake nanatawa tare da Baffa dake tsaye daga bayansu tin farkon fara maganar nasu, se Dr pooja dake tsayen itama gaba ɗaya tsigar jiki da jikinta na wani kalan rawa, a duk lokacin da zata ji ana wa'azi, ko tunasarwa me irin haka. Gyaran muryan Baffansu su ne ya saka kukan Shareefah dakatawa, nuni ya mata da Dr pooja take kuwa itama ta fuskanta halin da take ciki, kai tsaye ta fara ƙoƙarin tallafa mata duk da itama tallafin take. Suna haka sega wata nurses mace nan ta iso wurin tana amsar pooja ɗin suka fara tafiya. Kai tsaye kuma Shareefah'n ta miƙe tana ma su Baffa jagoranci zuwa ɗakin da Meenal ɗin ke kwance amma ta cikin glas, don babu damar shiga ko waye kuwa in aka ɗauke ma'aikatansu. Wata guntuwar kwalla Baffa da Ya Sadeeq suka ɗauke kusan tare, har dama Ya Ahmad da tin isowar Baffan yake biye dashi, sedai baya da bakin da ze iya buɗewa balle har yayi magana, ganin hakan ya saka Baffan kyaleshi ya hutayye ma zuciyarsa, duk da kasancewar bawai ma sanin takamaiman makomar auren Meenal ɗin suka yiba......

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215

*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*

𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

Unexpected and Surprising 🔥💥

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.

Page 7&8

♡ ♡ ♡ ♡

ꨄ.... Sunfi ƙarfin 30 minutes tsaye a wurin kafin Ya Sadeeq ya lalubo hannun Baffansa cikin nasa tafin, cikin dauriya da son danne raunin dake son taso masa game da ƙanwar tashi yace. "Muje gida Baffa!" Don ya lura da yanda jikin Baffan nasa ke rawa, ganin hakan ya saka Baffan kallon Shareefah shima yace da ita. "Muje gida!" Kanta ta girgiza masa wanda taji kamar ze faɗo ƙasa na tsananin damuwar da take ciki, da kuma yunwar dake ƙoƙarin illatata ba tare da sanin taba,don ita samm a babin yau ɗin nan komai mancewa tayi dashi bare wani abinci da ta gama ɗaukarsa ƙaramin alhaki. "Zan tsaya anan Baffa!, Yaya Meenal zata iya farkawa a koda yaushe likitoci zasu bukaci wani nata a kusa!, kuje gida ni ina nan tare da Yaya Meenal...." Ta faɗa idanunta a soye don jin ƙaddarar yayar tata take kamar tata ce, "Kuje gida Shareefah ke macece kuma yarinya ƙarama, zan kula da ameenatou kuje....." Haka duk su ukun suka tsinkayi muryansa, wanda a kallon farko baka isa cewa shi ne yayi maganar ba, daga yanayin yadda fatar bakinsa take a bushe raƙayau, babu kuma wata alamar da zata nuna maka cewar shi ne yayi maganar... Taku ɗaya ana biyu ta ƙara tana tsaiwa a gaban mijin Yayar nata tace. "Kai ne zaka tafi ka barni, domin Ni nafi chanchanta da kulawa da Yayata...." Ba kallonta yake ba sema baya kaɗan da yana yana sake harɗe hannunsa a ƙirji yace, "Ni nafi chanchantar kulawa da ameenatou Shareefah, kina da buƙatar kaɗaicewa ki sama nutsuwa haka nan kema...." Idanunta da suka sake cika taf da hawaye tace "Ni babu inda zana je, sabo da ni macece ƴar uwarta zanfi bata kulawan da tafi buƙata!" "Ni kuma Mijin tane ni ne zanfi kowa bata kulawar da kowa be isa bata ita ma Shareefah!" Daga ya kamo hannun Ya Sadeeq da suka jima da zama status shi da Baffa yana tsaida shi gabanta yace. "Ku tafi........" Ya Sadeeq ɗin ne tamkar wani gunki ya ɗamko hannun Shareefah ɗin ganin yadda take jujjuya masa kai alamar ya barta. Babu yacce ta iya, babu kuma yacce zata yi dole yaja hannunta suka tafi, ta tafi tabar Yayar tata a cikin wayuyacin halin da take a ciki. A cikin rai da ruhinta tana ayyana ba laifin yayarta bane, laifin wulaƙantattun wasu mazan irin ƴan iskan garin nan, ba laifin shigar dake jikinta bane, ba laifin ta bane, ba laifin ta bane, laifin wasu mazajen ne masu son zuciyoyinsu, in banda haka daga ganin mace a hanya shikenan seku haike mata?, dolen dole laifin ba nata ba ne, ko tashi sayayyarsa ALLAH yayi mazan ze kama... Haka take ta jujjuya maganganun ita da zuciyarta. Tin da suka bar wurin Ya Ahmad ya sake jingina da jikin ginin wurin se a lokacin wani abu me kama da dawowa hayyaci ya same shi, wani kalan rumtse rinannun idanunsa da soye yayi ƙafafunsa na fara rawa, ya fara bi yana dafe bangon dake ginin wurin, jikinsa da gaɓoɓinsa na kamar ana ruru musu wuta ne ata jikinsu, isowar Dr Bilal ne ya temaka masa, sabo da Dr pooja da tayi waya dashi ta labarta masa yacce ake ciki, amma bata faɗa masa ainihin abinda ya faru da Meenal ɗin ba ta ɓoye hakan a iyaka zuciyarta, se kuma Sir MAJEED da tayi kuskuren sanarma wa, wanda yace daya saka tsarkakan hannuwansa ya duba ta shima ya kwashi nashi rabon tagomashin zunubin, ƙara ya barta ta mutu, da uban wa yace karta kare martabar aure da addininta... Shi ne fitowar nan da yayi yana ta balbalin bala'insa har Shareefah ta gansa. Shi da kansa ya temaka ma Ahmad ɗin ya miƙa shi ɗakin jinya ya kwantar dashi, tare da auna jininsa da yaga yayi mummunar hawa, drip ya fara ɗaura masa da masa alluran bacci zuwa can dare ya gani, idan har be sama pain Relief ɗin da ake buƙata, se a san yacce za'a yi dashi, bayan ya masa wasu allurai. Ga jikinsa da har wani hucin zafin yake fitarwa tsabar yadda yake amsar kidan dake sake rikita jiki da zuciyarsa, ga daga cikin kansa ji yake kamar ana masa bikin mahaukatan aljanu a cikin tsakiyar kan nasa, sannu a hankali tunaninsa ya fara janyewa yana nesa nesa dashi alluran da aka masa na fara rinjayar kai da tunaninsa, wani wahallen barcin da har a cikinsa mafarkan Meenal ɗin ne kawai a cikinsa, Meenal ɗin da yake ɗaukarka a matsayin DUNIYARSA, se gashi sama ta ka ta meda wannan Duniyar tasa ba komai ba, domin ta gama rugujeta tass babu komai a cikin ta se tarun wasu ababuwan da bai gama tantance ko sanin ko meye su ba....

*Meenerl*

"DON ALLAH DA DARAJARSA KU ƘYALENI, KU RUFA MIN ASIRI NI....NIE MATAR AURE CE, KARKU AIKATA HAKA GARENI NA HAƊAKU DA GIRMA DA ZATIN DA MAHALICCINMU YAKE DASHI....!!!"
Chapter 11 · 0% Book details