← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 36

Sashe 3

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lokacin da Dr pooja ke can tana ma Meenal interview tuni shi har ya jima ma da barin cikin hospital ɗin baki ɗaya, kuma Alhamdulillah sosai tayi ƙoƙari dan tiyatan Ɓera ne tayi, kuma cikin ikon ALLAH bayan allurar baccin da akama ɓeran ta masa tiyatan cikin taka tsantsan da kuma tsoro, amma cikin iko na Ubangiji tana kammalawa sega ɓeran nan na motsi harma yana ƙoƙarin tashi ya gudu, wata nannauyar ijiyar zuciya daga ita har Dr pooja ɗin suka saki ita tana godiya wa ALLAH,ita kuma tana cewa. "THANKS JESUS...." daga nan suka ci gaba da ƴan ababuwa har ƙarfe sha biyu da kusan rabi, kafin ta ɗebeta suna komawa office ɗin Dr BILAL, sedai tin kamin Meenal ɗin ga kawo kanta taga Dr pooja ɗin tayi hanzarin yowa baya tana dafe goshinta da zuciyarta, na irin alamar nasha da kyar ɗin nan kafin kuma taga lokacin data furta thanks jesus, ta motsawar mukwallonta, tana kama hannunta suna saurin barin wurin, suna yin ta bayan window me girma, tsaiwa tayi bayan ta saki hannun Meenal ɗin dake ganin Ikon ALLAH, "Thanks god Sir MAJEED!! be ganmu ba...." Ta furta tana sake sakin wata ijiyar zuciyan. office nata ta wuce da Meenal ɗin, suna isa ta saka ƙiran Dr BILAL. Nan take bashi labarin ai taje zata shiga office nashi ta tarar da Sir MAJEED a ciki yau dai jesus ya tseratar da ita, dariya bame yawa ba Dr Bilal ɗin dake tare da Sir MAJEED ɗin har kusan daf ya saki, can ƙasa ƙasa yana satar kallon inda MAJEED ɗin ke zaune daya wani sha mur sosai yana cike wasu takaddun da shi ne abinda ya kawo shi cikin asibitin da seya kusa shafe rabin shekara be leƙo taba,dan hakan nema yasa ba kowa ne ya masa cikakken sani a matsayin me hospital ɗin ba, mafi yawancinsu ma sukan danganta asibitin data Dr Bilal ɗin ne, idan kuwa kaga mutum ya masa farin sani a cikin asibitin to kuwa tabbas babbane me girman matsayi kamar dai Dr pooja ɗin da ta ganshin a yanzun, wanda mamakin ganin san da tayi har yaso bata mamaki, wanda ita a karan kanta sau da dama takan sha mamakin yadda aka yi Majeed ɗin ke mata kwarjini bayan kuma schoolmate nata ne, tare suka yi karatu a ƙasar Oxford amma yanzun ya wani girme mata ya zama magidancin dole, duk da dai dama magidancin ne kuwa, harda ƴar sa ƴar kimanin 7 year's. Fesar da iska daga bakinsa Dr Bilal yayi yana datse ƙirar bayan kallon da yaga Majeed ɗin na jifarsa dashi, komai kuma be ce masa ba, wanda dama yasan hakan cewa zata faru tin da hakan shi ne kusan ɗabi'arsa. Miƙewa yayi yana nufar hanyar barin office ɗin, seda yaga yakai har bakin ƙofar kana ya masa gwalo yana cewa. "Maye dai yaci kansa banza miskilin tsiya da baƙar zuciya, yanda mutum yaƙe baƙi haka ma zuciyar tirr da MAJEED DAWOUD ISHAQ...." Yana kai nan ya fice a guje daga office ɗin baki ɗaya,ɗan yasan tsaf shi idan ya tashi yaɓo tashi baƙar maganar ze kusan kashesa da ransa. Kai tsaye office na Dr pooja ya wuce saɓunta gaisuwa tsakanin su suka yi, yana amsar document ɗin da pooja ɗin ke bashi, dubawa yayi yana cewa ta kwana ma gidan sauƙi bara kawai ya bema Majeed ya shigar da file ɗin cikin jadawalin list na ma'aikatan asibitin, seda Dr pooja ta ɗan waro ido har tana gaza yin shiru tace. "You don't see any problem with that, do you Dr?" Murmushi yayi yana fita kawai dan ya fahimci tsaf pooja ɗin zata bashi ciwon kan da Majeed ɗin ke yawan cewa tana bashi. A lokacin da yaje masa da zancen duba file ɗin daya masa wani kallo yana ma turar da laptop ɗin dake gabansa gefe daban, kafin ya wani kalle sa yace. "Kai me yasa ba zaka shigar ba,halan ka haɗu da cutar kuturtace bana da masaniyar hakan, to bara kaji indai se na shigar da wannan cikin jadawalin list ɗin ne, to kuwa ko waye sedai ya mutu be sama aiki anan ba...." Daga haka yasa kansa yana ficewarsa, ko ina be kalla ba ya shige motarsa yana ma yin reverse yabar cikin asibitin.

Ƙarfe biyu daidai Ahmad ya dawo asibitin suka wuce bayan ya sake jaddada godiyansa ga abokin nasa Dr Bilal, har gaban motarsu ya sake rakasu daga ita har shi suna sake jaddada godiyar su, tana cewa ya sake miƙa mata godiyarta ga Dr pooja. Daga nan kai tsaye gidan Hajiyarsa yakai Meenal ɗin, duk kuwa da yanda gabanta ke faɗuwa da haɗuwar nata da hajiyar san, don tasan bame kyau bace, amma bata nuna masa komai ba har suka isa gidan, hong yayi get man ya buɗe musu get ɗin yana cilla hancin motar nashi cikin haraban gidan nasu, Motar Abbansa daya gani a gidan ne ya bashi tabbacin yau babu inda ya fita kenan, duk da dai dama be ganshi a Company ba, wanda da ya zata ko wani wurin yaje, ashe duk ko ina ne ma beje din ba. Ajiyar zuciya me kyau na ziran da tayi itama tayi ganin motar Abban, don tasan ko babu komai ta kuɓuta daga bakaken maganganun hajiyar Ahmad ɗin....

Da sallama ɗauke a bakunansu daga ita har shi suka shiga parlourn gidan, wanda mutane uku ke zaune a babban ƙaryataccen parlourn, magidancin jarida ce ɗauke a hannunsa yana dubawa, yayin da magidanciyar matar ke zaune tana fuskantar plasma da ake haskaka labaran Duniya, se wata matashiyar da ita kuma ke kwance saman 3siter tana lallatsa wayarta, wanda sallamar su Ahmad ɗin ya saka gaba ɗaya attention nasu dawowa kansu ciki kuwa harda hajiyar da tana kallon sa tare da Meenal take ta ɗauke kanta bata sake kallar inda suken ba. Zaune matashiyar ta miƙe tana gyara hulan dake kanta dake ƙoƙarin zamewa, fuskanta da fara'an ganin Meenal ɗin ta miƙe tana nufosu tana cewa _Oyoyo Meenally'n babban Yaya...._ ta isa gare su tana rumgume Meenal ɗin da ita ma ta rumgume Fatiman, A kunyace ta ƙaraso tsakiyan parlourn tana ɗurƙusawa gaban Abba da yake tace da ita ta koma saman sofa, gáidashi ta shiga yi a girmame tare da Hajiyar da take wani amsata a ciccure, wanda hakan ma tasan albarkacin Abba ne taci, se lokacin kuma Ahmad ɗin ke ƙarasowa cikin parlourn shima yana zama daga ƙafafun Abban nasa ya gaida shi, kafin ya juyo a natse ga mahaifiyar nasa, "Hajiyata barka da rana, fatar kin wuni lafiya...." A daƙile ta amsa may da "Lafiya Alhamdulillah" kawai tana ɗauke kanta daga garesa. Fatima ce ta Abba yace ta wuce dani ɗakinta,hakan kuwa yamin daɗi ba kaɗan ba muka wuce abin mu, babu jimawa sega Ya Ahmad ya shigo mana da abincin da na tabbata ni ya kawowa ma. Da ido na masa alamun ya ka min haka?, shima da idon yamin alamu da sabo da hakan hakkinane... Murmushi kawai nayi kuma kamar abin haɗin baki muka saki dariya a tare, be zauna ba ya fita sakamakon shigowar ƙira cikin wayarsa ya fita, dake tayi salla a can asibitin se kawai ta zauna sukaci abincin, koda suka kammala kwanciyar ta tayi a gadon Fatiman take nannauyar bacci yayi awon gaba da ita, wanda ta jima yi, don se bayar la'asar sosai ta tashi sallarn ta fara yi kuma zuwa lokacin Fatima bata nan, wanda take da tabbacin Islamiyya ne ta tafi, fita tayi zuwa parlourn Hajiyar, har lokacin Abba na zaune a parlourn amma babu Ahmad, Hajiyar kuma bata parlourn sema motsinta data fara juyowa a kitchen don haka kai tsaye ta nufa kitchen ɗin, A ɗan tsorace ta mata sannu tana ce da ita ta kawo ta mata aikin, wani banzan kallo ta wurgo mata tana jan tsaki tare da nuna mata hanya alamar ta bar mata wurin, "Don ALLAH kiyi hakuri Mami ban san abinda na miki ba wllh..." A wani irin fusace kuwa ta juye tace. "Baki san abinda kika min ba?, tun da ke muna fuka ce gadon munafurci taya ya zaki san abinda kika min kuwa, tin da kin gama mallake min ɗa babu kowa a gabansa in ba ke ba, gashi yau watanni Bakwai kenan da aurenku, ban ga alamar komai tattare dake ba, halamar sedai aci aje masai kenan ke ba matar ƙaruwa bace out....."
Chapter 3 · 0% Book details