← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 36

Sashe 24

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko Baffa da Ya Sadeeq ya nasar dashi Adda'a kawai yayi akan batun yace ALLAH ya kai su lokacin, ɓangaren su Hajiya Madina ma duk sun gama har haɗa shedunsu akan cewar lallai Meenal ita ce sanadiyyar mutuwar yaronsu, wanda ranar juma'a za'a yi zaman, wacce ta kama saura kwanaki uku kenan a shiga Shari'an, sosai aka sake linka tsaron dake cikin anguwar wanda su kansu masu anguwar har mamakin hakan ya gaza barinsu,gashi kullum suna bakin aiki duk irin daren da zaka tsala zaka taddasu kiƙam ɗin nan. Sosai kan Ahmad ke ɗaukar hayaƙin shiga kotun da za'ayi, wanda se a daren washe garin ranar da za'a gudanar da zaman yake sanarma mahaifinsa IBRAHIM SHAREEF komai, sedai be musu zancen fyaiɗen ba, don a ganinsa ya wuce fannin tun da har yace Meenal ɗin karta yarda ta faɗa maganar fyaiɗen bare kuma cikin jikinta, sedai ya makaro kusan zamu ce, don kuwa a nata ɓangaren ta gama shirya duk wasu hujjoji nata ba tare da sanin kowa ba ta naɗe kayanta a kanta, ko lawyer ɗin da Ahmad ya ɗauko mata bakinta be jiba, duk kuwa da irin bugun cikinta daya ringa yi, amma haƙarsa bata cimma ruwa ba......

_To fa wannan shi ake ƙira da ana wata ga wata_

_Jama'a ya kuke tunanin wannan zaman ze wakana kuwa?, shin kuna jin wani ƙanshi ƙanshi koni kaɗai ce nake jiyo mana?_

_Wannan tafiyar fa itama da nata kalan salon da tazo mana shi, don na fahimta yanzun alƙalamin nawa nema yake ya faɗa kan iyaka ƙaddara da kuma ƙalubalen rayuwa Tabbas, to koma dai miye nidai AMMEY LAYLERH burina in nayi rubutun jama'a su amfana dashi_

_Nasan zaku ringa tunanin cewar ya alƙalamin yake nemar mana wasa da hankali ne ko?, zuwa yanzun nasan ko kowa be furta ba to kuwa abinda ke ƙumshe cikin rai da ruhinsa kenan..._

_Se dai ku sani cewar indai wasa da hankali ne Hhhhhhhhhhh badai zan ce komai ba amma dai akwai zatan da zakuyi tayi kuma na sanja salon tunanin naku kamar dai yacce aka saba, lolz 🤩 Ni kaina nasan banyi kamar wannan littafi ba, gashi dai labarin ba tsayi zeyi irin sosai ɗin nan ba, amma kuma nace sena rikita tunaninku, na gama assignment ta yacce zakuyi ta hasashe da tsammatar abinda be shi ke akwai ba, karfa ku manta sunan littafin ƘARSHEN ƘADDARA!!!. Kun ga kenan ai ƙaddarar ba ɗaya bace kenan ƙaddarorine da yawa....._

_Hhhhh to lolz 🤩 🤩 🤩 koma dai miye ku muje zuwa🤸🤸🤸💃💃💃💃💃💃🤸🤸🤸_

*BY AMMEY LAYLERH ✍️

08104493215

*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*

𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

Unexpected and Surprising 🔥💥

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.

ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏....

Page 15&16

♡ ♡ ♡ ♡

ꨄ Daga cikin motar da take zaune take ƙarewa harabar kotun kallo, wacce take cike da mutane kowa na harkan gabansa, wanda da dukkan alamu wata Shari'a ce aka gudanar me zafi, wanda ganan jama'a se famar mayar da yadda al' amarin ya kaya suke. Gaba ɗaya a yau ɗin data tsinta kanta a cikin kotun se take jin kamar zata sare ne, domin taki bama lawyer ɗin da aka kawo mata dama, wanda ita a karan kanta take son zamewa kanta da kanta lawyer kamar yacce Yami Ghautam tayi a cikin Film ɗin ta na HAQ wato ƙare Haƙƙi, za tayi iyaka yinta In sha ALLAHU itama har taga tayi nasarar da ikon ALLAH. Buɗe Motar da wata police tayi ne ya katse mata tunaninta, tana sanye cikin ɗamararta ta cikakkar ƴar sanda, hannunta da ɗan kulkensu wanda tin a daren jiya suka je har gida suka tafi da ita,sedai hakan bata faru se sune suka kwana a ƙofar gidan suma suka zama kamar body gurds nata ne, ita kuma ta a daga cikin gidan soye da zuciyar da tayi kwanan wasi wasi da fargaban ko me ze faru a cikin shari'an nasu. "Mrs Meenal zaka iya fitowa?" Christian police ɗin ta fadi, wanda ya sakata yunƙurowa tana zube kyawawan ƙafafunta da suke fess tayi, akan ta tsaya akan diga diganta tana fesar da wani gauron numfashi, Idanunta ta lumshe a can cikin zuciyarta ta furta....

_ALLAH kai ne ALLAH!, kai ne kuma buwayi gagara misali, UBANGIJIN da babu wani kafinsa, kuma babu wani a bayansa. Ya ALLAH na san mutanen nan sun fi ƙarfina ta ko wace siga, amma ni ban damu ba sabo ni kaine GATANA kuma abun DOGARO NA!, na san ba za ka taɓa bani kunya har na tozarta a idon duniya ba.Ya ALLAH gasu nan sun fi ƙarfina ka fi mini ƙarfinsu kai ma. Ya ALLAH ka nuna musu irin naka ikon na KUN FAYAKUN akan wannan shari'an!, Ta inda HASKEN dake cikin shari'an ya bama GASKIYA kariya ya shafe Ƙarya da sharrin dake cikin ta, Ya ALLAH ka zamana a bayana duk da ina da wanda suke tsaye a bayan nawa kuwa, amma ALLAH goyon bayanka nake buƙata, Ya Wadud!,UBANGIJINA ka iya mini badon iyawata kota wani na ba......._ tana kai nan ta soma tafiya cikin nutsuwa, Nan ƴan jaridu su kayo Caaaa a kansu wasu jami'ai biyun dake bayanta da aka rasa daga inda suka fito na bata kyakkyawar garkuwar da babu Yar jaridar data ko sake yunƙurin tun kararta, a nata ɓangaren kuwa tana tafiyar kawai amma Zuciyarta bugawa take duk lokacin da take sake tunkarar ƙofar shiga kotun, zuciyarta naci gaba da tsananta bugawa,tana fata da roƙon ALLAH ya shiga lamarin ta. Bayyanuwarta tsaye a gaban kotun ne ya saka wata hayaniya ɓarkewar da seda tayi yunƙurin kai hannunta da nufin toshe kunnuwanta ta tuna da Onka ɗin dake ɗaure da hannuwar nata, Wata tsawa ɗaya daga cikin lauyoyin dake zazzaune wani ya doka musu wanda ya saka kotun wani irin tsit, ta yanda har ba ka jin sauti da motsin komai face na ƙarar gudun A/Cn , gaba ɗaya mutanen sun kame sun zama kamar wasu gumaka tamkar kuma masu jiran wani sakamako. Kana sannan kotun ta sama nutsuwa har aka wuce da ita wurin da ake tare wanda ake tuhuma, gaba ɗaya kowa ya gama hallara a babbar kotun se dai anki fara gudanar da shari'an ne akan One Man ɗin da suke jira, wanda kowa be san ko wanene ba, kana babu mutumin daya san shi ko meye huriminsa akan Shari'a ɗin....

★..

Tin bayar fitowarsa daga gida daya hau titi yake fuskantar kamar ana bin bayansa, gashi shi dama ba gwanin yawo da security ba don yace yawo da security ai na matsoratane masu raunin zuciya lolz 🤩 ba inji LAYLERH ba, Inji Majeed tin dai masu ɗan security ɗin nan daɗi ne dashi, ko kuwa yanzun mace Yaya Kuwait ɗin mu ÈÃGLÊ yana da tsoro🤸, kai tsaye ya ƙira security line na gidansu ya basu umarnin su biyo bayan shi akwai wata Black Bentley car ɗin dake bin bayansa da be gama yarda da ita iba kawai suyi kidnapping nata.
Tun daga nesa yake hango irin uban tarin car's É—in dake cike da harabarn kotun, wani murmushin gefen baki yayi tightly yana parking nashi ka É—in a wurin da aka tanaja don ajje motoci.
Bayyanuwarsa a wurin ne kuma yayi sanadiyar da iskan wurin ya sanja da ƙamshin daddaɗan out irin me sanyin daɗin nan, be san me yake ji game da case ɗin ba, abinda kawai ya sani tausayinta yake ji, yana tuna ameenatou ɗin sa ne, don haka duk wani taku ɗaya da zai yi sai ya ji ƙirjinsa yana amsawa, tun kafin ya iso wajen wani kalan kamshin da yake fitarwa me azabar daɗi da saka mutum yaji ya fara jin bacci take.... Alƙalin da ze gudanar da shari'an ne ya miƙe tsaye, tare da gyara farin yankakken gilashin dake idanunsa na ƙara ƙarfin gani, kafin yayi ɗan gyaran murya ya fara da cewa.

"A yau data kasance ranar Juma'a wacce tayi daidai da _27/2/2026_ Zamu gudanar da Shari'armu akan laifin kisan kai, wacce ake zargin AMEENEERH SHEHU USMAN da laifin a cikin wannan KOOOTU!, tamu me albarka" Alƙalin yayi maganar yana buga ƴar hidimarsa, tsittttt kuwa kotun ya ɗauka shiru....
Nan ya umarci da lawyer ɗin dake kare ɓangaren iyayen yaron da aka kashe da su fara fitowa su gabatar da shari'ansu... Mutum ɗaya ne daga cikin lauyoyi biyun da suka diba ya miƙe tare da furta.... "Ya me girma me shariya sunana lawyer Ibrahimul-khaleel datti!, nine kuma lawyer ɗin da yake kare ɓangaren shari'an iyayen Sameer,akan Rashin tallafin da ɗaya daga cikin Dactor's na asibitin 4&4 suka kashe mana shi!!!!..." Ɗaya lawyer ɗin ne ya miƙe tare da ci gaba da faɗin.. "Kwarai kuwa yame girma me shari'a!, kamar yadda ɗan uwana Lawyer Ibrahimul-
khaleel datti ya faɗi haka ne, domin a lokacin da iyayen Sameer suka kai shi cikin asibitin 4&4 lokacin daya sama accident aka kai shi can, amma se Dr Meenerl Shehu Usmanu taki amsar shi tin uwar yaron nayi da ranta har ya koma ga ALLAH, Na gode yame Shari'a...." Lawyer ɗin ya faɗi yana ɗan dukar da kansa ƙasa ya koma mazauninsa ya zauna.... Ɗan gyaran murya Alƙalin yayi tare da faɗin "Ina son ganin lawyer me kare haƙƙin DR AMEENEERH SHEHU USMAN" Tsit da shiru kotun ta ɗauka, kowa na son ganin ta inda lawyer ɗin da zai kare Meenal ze fito, ciki kuwa harda su Dr pooja dasu Dr Bilal, sedai shiru har na wosu ƴan mintuna babu alamar zai fito ɗin kuwa. Don haka Lawyer Ibrahimul-khaleel datti ya sake miƙewa yana me furta...."Tun daga nan ma sun bayar da shedar cewa lallai Dr AMEENEERH SHEHU USMAN ita ce sanadiyyar mutuwar Sameer Garba Aliyu na Ya......
Chapter 24 · 0% Book details