← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 36

Sashe 30

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba ɗaya yinin ranar ta yau ta sake yinsa gata nan gata nan ne, barin ma makwafta da mutanen anguwa da suka ringa shigo mata jaje, wasu kuwa dama da gayya suke zuwa su yayyaɓa mata magana a matsayin jajantawa suke mata, har da masu ce mata ai tama godema ALLAH da cikin ya fita shikenan babu ita babi idda ko a yau taga damar sake wani auren za tayi, duk cikin masu zuwan babu wanda ya taɓa tankama, daga ƙarshe ma se ta wuce dakinsu se yamma kana ta dawo tsakar gidan, zama tayi tace Shareefah ta mata kitso, suna cikin kitson sega shigowar Bilkisu nan daga wurin bikin da taje. Ciki a sanyaye ta ƙaraso don ummar ta harta riga ta sanar mata da komai, wacce matuƙar tausayin yayar nasu ya sake rufeta da ganin nata kawai zai ne a gida. Idonta fall da ruwan hawaye ta zauna tana gaida yayar nasu tare da jajanta mata lamarin, da cewa ALLAH ya rufa asiri ya tsare gaba. Da Amin suka amsa ita da Shareefah sega fitowar gwaggo daga ɗakinta ta fara masifar wato ko wurinta ba zata shigo ba shi ne ta tsaya a wurinsu, da uban wani ne yace karta kama kanta ko ita ta aikata ne bare ace ita ce silar ƙaddarar nata. Babu daɗi samm haka Bilkisun ta miƙe tana sake bama Meenal ɗin hakuri, ko da aka yi sallar isha'a se aka fito tsakar gidan zaman fira bayan anci abincin dare. Se dai shiru shiru Meenal daga shiga daki ɗaukan abu har yanzun shiru, tun Shareefah da Bilkisu na saka ran fitowa Meenal ɗin har su hakura. Ita kuwa Meenal a nata ɓangaren tana shigewa ciki duk da ba barci take ji ba, se kawai tayi kwanciyarta don tun safiyar ranar take wani sukuku da ita kamar marar lafiya. Akan sallayan da tayi Sallah ta zauna tayi shiru tana istigifari ga ALLAH da Salati ga fiyayyan halitta Annabin Rahama, duk yanda tunani yaso ya bijiro mata saida ta kawar dashi kawai ta fawwalawa ALLAH lamarinta tasan duk rintsi yana tare da ita, a haka har bacci yaci ƙarfin ta ba tare data shiryama hakan ba. Cikin kwanaki uku amma anguwar ta gama haɗewa da zancen wannan zancen abinda ya sama Meenal ɗin, Nan kuwa mutanen anguwa harma da tsallakenta aka samu abin yamaɗiɗi a unguwar,
Gaba É—aya se suka sako Meenal a gaba har seda Shareefah ta yankama É—aya daga cikin munafukan katin rashin mutumci kana sauran suka shiga taitayinsu, wannan abu da Shareefah tayi shi ne ya É—an kwato Meenal É—in daga munafukan anguwar.

"Yahanasu...."
Abban Ahmad ya wani irin ƙiran sunanta a mugun tsawacen da ya sanya kowa dake wurin rawan jiki. Don ba abu bane daya taɓa faruwa a zahirance duk kuwa irin tijara da jalalar da Umman Ahmad ɗin keyi akan duk wani abu daya danganci Ahmad ɗin. Bakinta dake rawa ta buɗe da kyar tace "I'm sorry Abban Ahmad, wllh sharrin shaidan ne" Ta furta muryan ta na rawa sosai.

"I said get out my friend! Nace ko?" Gaba ɗaya se jikin yaran nasu yayi sanyi ganin dai da gasken gaske mahaifin nasu ya rantse se tabar masa gidansa itama, in yaso se taji idan sakin da daɗi itama. Be sama labarin sakin data titseye Ahmad ɗin yama Meenal ba se a wayewar yau daya kasance kwanaki huɗu kenan da faruwar abun. Don haka yace itama wllh se ta bar masa nasa gidan se lokacin daya ne mata, domin dama ya jima da mugun gundura da halin nata, kawai yana dauke kai ne sabo da yaransu, to amma tun da ta nuna masa iyakarsa da cewar shi be isa ba to ya rantse a yau ba sai gobe ba seta bar masa gidansa. Ahmad ɗin idanunsa sunyi jajir ya nufa Abban nasa yana bashi hakuri shima ya buga masa wata tsawa yace ya fice ya bar masa gida. Fatima kuwa wani irin kuka take na nadamar halayen momin nasu marasa kyau. Ta buɗe baki da niyar sake bashi wani hakurin ya sake buga mata wata uwar tsawar da tafi ta farko ba shiri ta haɗiye maganar da bata ƙarasa taba, tana barin wurin don A yadda ta ji muryarsa a kausashe kam ta tabbata babu wasa a cikinta ko sauran mafaka,
Jiki a sanyaye Ahmad ɗin ya fice a parlourn nasu itama Fatima ta wuce nata ɗakin. Ita kuma Umman nasu da jikinta ke rawa ne ta wuce ɗakinta babu jimawa se gata ta fito da hijjab ɗin bata fiye yawan da shiba. Ganin daga se himar nata ne ya saka shi sake buga mata tsawa yana cewa maza ta haɗo kayanta a akwatu don ba nan kusa zai nemeta ba, har se lokacin data dawo da Meenal ɗakinta. Sosai ta sake razana da lamarin wata muguwar nadama na sake kamata, tana jin tsanar mugwayen halayenta da har yay sanadiyyar rabata da bugun numfashinta wato Abban, don ba ƙaramin mahaukacin SO take masa ba. Shi yasa ma take taka tsantsan da duk wani abinda ya shafe sa, amma se gashi yau saboda wata watsatstsiya can daban har yana mata barazana da nata auren, sosai ta sake jin tsanar Meenal ɗin a cikin rai da ruhinta. Babu jimawa se gata ta fito da akwatun ta taf da kaya ta fice tana jan majina, ido yayi fulin fulin tsabar kuka... Kai tsaye daga nan gidan su Meenal ɗin tama tsinke, taje ta sake yayyaɓa maganganunta san ranta, har da cewa yo dama ita yar malamai ba dole ubanta ya shiga tsakanin zaman lafiyarta da mijinta ba, daidai kuma Baffa ya kawo kansa lokacin da take faɗar kalaman nata, don haka ya ƙaraso yace da ita. Ta sani ita data koma gidan ɗan nata har abada, domin ta gama zaman aure dashi, tana nan zaune In sha ALLAHU se taga mijin Meenal ɗin zata aura ko ba jima ko ba daɗe, kuma taje duk abinda tayi kanta, se da Baffa ya mata tasss kana ya komar da Meenal ɗakinta da idanunta suka sake rinewa sosai, Runtse idanunta a karo na biyu tai tana ƙoƙarin kwatar numfashin ta dake barazana wa gangar jikinta. danne dukkan abinda ke yunƙuro mata tayi, tun da ga aurenta da Ahmad da irin baƙar tsanar da ummansa ke nuna mata haka kawai, har zuwa loƙacin da tafiyar su tasha banban da juna wacce wata shuɗaɗɗiyar Ƙaddara tazo ta ratsa tsakani, amma duk da haka baiwar ALLAH'r nan ba zata barta ta huta haka nan ba, se tayi ƙoƙarin mantawa da abu kana se wasu mutane su sake tado mata da danyen raunin da ya dauka hanyar warkewa.Lallai ta sake yarda duk inda Kalmar KADDARA take, lallai kalma ce dake motsa zuciyar ko wanne bawa domin kuwa tabbas wannan kalmar ta KADDARA kalmace me girma da faɗi wacce ta ƙunshi abubuwa masu yawan gaske a cikinta, domin kuwa Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwa juna. haka kuma kowacce rayuwa tafe take da nata salon ƙaddarar ita ta amshi nata da hannu bibbiyu In sha ALLAHU, kamar yanda Baffan ta yasha ce mata Idan har bawa zeyi haƙuri wajen jure wannan tarin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin rayuwarsa game da duk abinda ALLAH ya riga tsara masa, to kuwa lallai kayi hakuri da duk abinda ALLAH ya tsara maka domin kuwa shi ne mafi alkhayri agareka. Sake Runtse rinannun idonta tayi sakamon kanta da taji ya wani kalan mugun sara mata da tsanin ciwo. Zaune takai bakin bed haryanzun hannuwanta riƙe da saman kanta dake jujjaya mata. Maganganun Umman Ahmad ɗin na son haifar mata da wani damuwan. Wani kalan zazzafan numfashi ta fesar tana hana kanta bama damar hakan faruwa. Domin kuwa ita ɗin mutumce me tsananin ƙarfin zuciya. Ba kowanne abu take bama dama yay crossed nata mind ba, duk yadda maganganun suka so haukata kanta amma ƙin bama hakan dama tayi. Lumshe idonta tayi ta taji hawayen da suka tara nemar zubo mata, amma ta sake shanye hakan har tana jin yadda jinin jikinta ke wani irin harmutsawa tamkar ana aza wuta a jinin jikintan haka take ji, shigowar Shareefah ne ya sakata ɗago rinannun idanunta ta zuba mata, zuwa loƙacin kuma jikinta har rawa yake a mugun wahalce ta nufi jikin Shareefah'n , dama tasan ita ɗince ta biyo ta lallashi bayanta. Rungumeta kawai Shareefah ɗin tayi tana bata baki da haƙuri. Ganin duk yacce Shareefah'n tabi ta ruɗe ne ya sanya Meenal ɗin ɗan janye jikinta ana Shareefah 'n tare da ƙaƙaro murmushin dole wai duk don ta kwantar mata da hankali. Saidai zubowar ruwan wahayen dake yankar zuciyarta da bala'i bala'in zafi da ƙunar da suka kusa haifar mata attack take ne ya saka Shareefah fashewa da nata kukan itama, jin yadda jikin yayar nata ke jijjiga......

_The comments are dropping. 😔 ko dai baya muku daɗi ne? Naga ba comments ba reactions naku._

_Please don't be a silent reader. Comment, vote and share. Thank you 👏👏👏_

_Love you all my mutanena Amanana😘🫂_

_Put a smile on my face please. Vote, comment, and share My lovely friend's ana tare_

# Voice of the innocence
# Team AMEENEERH SHEHU USMAN where Are You???

_Team Meenal wai kuna ina ne haka? meke meke shirin faruwa daku haka?_

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215

*༺ƘARSHEN ƘADDARA•◍࿐*

𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

Unexpected and Surprising 🔥💥

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.

ALHAMDULILLAH Ya Rabb👏....

Page 19&20
Chapter 30 · 0% Book details