Sashe 14
Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan tafiyar su Baffan sun jima zaune a wurin zaman kurame kafin tayi kundin balar sake nemar yafiyarsa gare ta, Komai bai ce mata sema tashi da yayi ya bar mata parlour ya shige bedroom nashi, don kansa wani bala'in ciwo yake masa, koda ta bishi taji ya rufe ɗakin kanta kawai ta jinginar da jikin ƙofar tayi kukanta me isarta a wurin, kafin taja ƙafafunta ta nufi bedroom nata, kwanciya tayi zuciyarta na wani kalan mata bugu da tafasa, ƙarfe biyu bayan tayi Sallah ta fito tayi girkin rana, ɗakinsa ta leƙa daga a rufe ta woje alamar ya fita kenan, kaɗan ta ɗan cakali abincin itama ta ture ta koma tayi wanka ta ɗauki Alqur'ani tayi karatu, har kusan yamma sosai tana nan zaunen kafin ta tashi taje ta meda na dare, bayan ta kammala tayi sallar magrib, ta sake karatun Alqur'ani tsakanin magrib da isha'a, wajajen tara taji alamun shihowansa gidan, tayi hanzarin fitowa jikinta da himar har ƙasa, daidai lokacin yake ƙarasa bayyana a cikin parlourn, sannu da zuwa ta masa ya amsata da hannunsa yana ƙoƙarin wucewa, cewa ta mishi ga abincinsa yace ya gode amma ya koshi, bata ji daɗi ba amma haka ta danne ta kyale shi, kana ta mara masa baya zuwa ɗakinsa, Sedai ya dakatar da ita ta hanyar ce da ita tayi haƙuri yana bukatar balance ne sosai, don haka ta dawo parlourn jikinta a matuƙar sanyaye, seda dare ya tsala sosai kana tabar parlourn, koda ta shige bedroom nata bata kwanta ba Alwala tayi ta fuskanta alƙibla, ta fara jero sallolin da bata san iyakar su ba, har aka ƙira asuba, A hankali ya turo ɗakin nata don tada ta tayi sallar subhi ɗin, Sedai ganinta a zaunen da yayi ne ya saka shi fita be ƙaraso ba, wajan shida ta fita ta ɗora musu brekfast. Lafiyayyar Doya da kyau ta musu, da lemun kwakwa, a gurguje taje tayo wanka kana tazo ta zauna cikin parlourn tana jirar fitowar sa, babu jimawa kuwa se gashi ya fito da brifcase nashi a hannunsa ta fita aiki, saurin miƙewa tayi tana isa gare shi yay hanzarin janyewa ya koma gefe guda, kanta ta sunkuyar ƙasa ta gaida sa, amsata yayi sama ² tace dashi ga breakfast yace da ita ya gode zeci a woje. Kusan a wannan karon kam daskarewa a tsaye tayi, shin me yake nufi ne wai, ko dama shi ne haƙurin da ya ce se tayi? In sha ALLAHU zata yi za kuma ta jure da Ikon ALLAH...
Tin tana kallar kamar zata iya jurema yanayin, har hakan ya fara fin ƙarfin tunani da kuma kanta, don takai ta kawo ko zama ya dena yi inda ta zaune, tayi kukan tayi adda'ar amma duk a banza, abinci kuwa dama tuni ta dena yi dashi, don ko tayi Sedai ta tayin asara tana bama getman ya rabama almajirai, abinda ya sake bata mamaki kuma shi ne da sati ɗaya da faruwan abun ya zo mata da zancen zata iya ci gaba da aikinta tace ta dena ta haƙura har gaban abada, komai daga haka be sake ce mata yaci gaba da rayuwarsa, har takai ta kawo gidan ma yanzun kafin ta tashi ya fita, lokacin da zai dawo kuma tayi bacci, inda sosai hakan ke damunta, har take jin ƙara kawai ya rabu da ita idan har hakan shi ne mafi alkhairinta, saboda da wannan matsalar nasu har Shareefah seda ta tuntuɓa da lamarin, kai tsaye kuma tace da ita ta ƙara hakuri akan wanda take yi, In sha ALLAHU komai zai wuce, gama hucewar ne be yiba. Tin Dr pooja na ƙirar ta har ta haƙura, inda daga ƙarshe take jin kyakkyawan labarin musluntar Dr pooja ɗin, wacce ta musulunta a hannun Baffansu a masallacin ƙofar gidansu, a yanzun haka tana amsa sunan AYSHA ne, tayi murna sosai da jin lamarin na musuluntar da tayi, Ta inda take sake godema ALLAH ma shi ne da bata da komai, idan kuma ta tsaya ta tsai da ranta rashin samun cikin da batayi ba a tin farkon Aurensu har zuwa yanzun kan damunta, se dai shima ta barma ALLAH lamarinta, haka sukaci gaba da gudanar da rayuwar Aurensu, ba tare data sake fuskantar kowa da matsalar ta ba, har kimanin 2 Months, gashi ma har suna kokarin shiga na uku...
Masu iya magana sukan ce a duk lokacin da wani abu ya tunkaro ɗan Adam yana yi masa barazana da rayuwarsa, sai yaga kamar duk duniya babu wanda ya kai shi shiga tsananin rayuwa. Har takan kai wasu ƙarancin imanin fara fafutar nemarwa kansu mafita ta kowacce siga ce kuwa domin kawar da ita wannan matsalar da yake fuskanta. Kamar yadda ya kasance a cikin rayuwar Meenal a ƴan tsakan kanin lokutan da suke wucewa a cikin rayuwar aurenta da Ahmad. Lallai ta sake yarda da wannan maganar da ake yawan cewa. Ciwon da ya addabi hannu idanu yake hanawa bacci. Idan ido bai yi bacci ba to lallai dukkan jiki ba zai huta ba. Jikin da rashin hutu ya yiwa sarƙa kuwa yana tattare da ƙarantar kuzarin kare kansa daga bullowar wasu cututtukan ne, Kamar yacce sannu a sannu wani irin ciwon da bata san ko ainihin na minene ba ke famar wajiga rayuwarta, Ta kuma sake yarda da ake cewa idan bamu magance ciwon hannun ba, da sannu sannu shi dai wannan ciwon zai iya kama ragowar sassan jiki ko kuma ya bayar da ƙofar samuwar cutar da tafi ta hannu. Sannu a sannu rayuwarta ke ci gaba da gudana cikin kunci a gidan Ahmad, ga ciwon dake ƙoƙarin kaita ƙasa amma tana gwada jarumtarta akan hakan, har tana daukar hanyar wata guda kenan da wannan jinyar, wanda a zahiri na gaskiya ba haka hasalin lissafin yake ba, wannan jinyar alamu ne bayyanuwar cikin haihuwa a jikinta, sedai tsananin kunci da damuwar da take ciki be saka ta fuskanta hakan ba, ko daga yanayin sanje sanjen da take samuwa daga wasu sassa na halittar jikinta, se dai idan aka ce tashin hankali to anan nufin gaba da komai kenan, don babu cikakkiyar nutsuwar da ya kamaci ace ta tsaya duba ko tantance yanayin da take a ciki ba...
Ranar da ba zata taɓa mancewa da ita ba a cikin rayuwarta itace ranar wata LAHADI, ranar ta tashi ne kamar ba ta kai labari ba, gaba ɗaya tin daga kamo daren ranar har kamo la'asar ɗin ranar haka ta wuni a kwance ko ruwa kasa zama a bakinta yayi, tana daga kwancen a yadda take ta fara ƙoƙari da yunƙurin miƙewa, da shigowar Ahmad sassan nata da rabon daya shigo shi har ta manta, gaba ɗaya ya gama fitar da ita daga cikin rayuwarsa tun faruwar wancan lamarin, ko zama kusa dashi be sake bari tayi ba. Kin kallar inda take kamar ko da yaushe, kamar yaga dogon zunubin da ze iya kifewa koya halakar dashi, haka ya dubeta yace tayi maza ya shirya ta fito yana jiranta a mota, tambayarsa tayi lafiya ina kuma zai kaita, wayarta yace ta duba Dr pooja (AISHA) tayi ta ƙiranta amma ta gaza taƙi amsawa, ƙoƙarin komawa kwancen data yunƙura ta tashi take, tana ce dashi.....
"Babu inda zani Ahmad!, ai na faɗa mata bana jin daɗi ne, ko kuwa duk Dactor's ɗin dake cikin asibitin basu isa ba se lallai dole ni naje???, Haba Ahmad da wanne kake son inji, na baka hakuri kaki ka haƙura ka fita a cikin rayuwata, ka dena sakewa dani ka dena kusantata, komai daɗa lalacewa yake, memakon ace samun sassauci nake, Bayan kuma na baka hakuri na baka hakuri, don girman kayi hakuri mana..." Tsaiwarsa ya gyara yana fuskantar da kyau yace. "Wanene ya gaya miki ban haƙuraba?, Idan da ban haƙura ba da tin tuni kin jima da tafiya gida!, kinga yanzun dai wannan a matsayin umarni da kuma temakon rai zakiya, kasancewar weekend na babu yawaitar manyan Dactor's duk se ƙananu shi yasa suka biyo ta hannu nama, Dr Bilal ne yamin waya don shi ashe ma baya 9j ɗin ne.........
Da kyar ta yunƙura tana shigewa bathroom, babu jimawa ta fito babu laifi kuwa taji ƙarfin jikinta sosai, don haka ta zira doguwar hijjabarta har ƙasa ta fito ta same shi cikin motarsa. Karatun Afid muhd taj ya saka musu, cikin ƙanƙanin lokaci suka isa asibitin, tin daga yanayin tsaron da aka bama hospital ɗin ta gane cewar lallai wani babban ne ko ɗan gidan wani kusar ne me jinyar, tana isa ta shiga wani room ta sanja kayanta zuwa na surgery, hannunta da handglovs idanunta da glasses fari ta nufi ICU inda nan ne me jinyar yake, Dactor's biyu ne suka mara mata baya ta shiga, tana isa Dr Aysha dake kan majinyancin ta bata hanya, isa tayi gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta ta saka hannu kenan da niyar amsar tiyatar idanunta ya sauƙa akan...................
_To fa shin akan mene ko waye idanun Dr Meenerl ya sauƙa?..._
*BY AMMEY LAYLERH âœï¸*
08104493215
*༺ƘARSHEN ƘADDARA•â—à¿*
ð™ˆð™–ð™§ð™®ð™–𙢠ð™‰að™¨ð™šð™šð™§ ɱⅈð”¯ð”¯É‘Ò»
_ð˜¼ð™ˆð™ˆð™€ð™” ð™‡ð˜¼ð™”ð™‡ð™€ð™ð™ƒ_
Unexpected and Surprising 🔥💥
ð™”ð™Šð™ð™‰ð™‚ ð™ð˜¼ð™‡ð™€ð™‰ð™ð™€ð˜¿ ð™’ð™ð™„ð™ð™€ð™'𙎠ð˜¼ð™Žð™Ž.
Page 9&10
♡ ♡ ♡ ♡