Sashe 34
Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Kwanci tashi aka ce hasarar me rai se gashi har sunyi wata huɗu da aure suna daf da shiga na biyar ma, kuma Alhamdulillah zuwa yanzun sosai take sakin jiki da Alƙali Yahaya,sedai har zuwa yanzu tsakaninta da tsaki yarunsa Indai sun haɗu su gaisa sama sama ta wuce itama ta wuce. Don ba ƙaramin kishi ne da ita da sam bata iya sarrafa shi, tsakanin ta kuwa da Uwar gidansa Hajiya Asma'u se son barka. Don tamkar ƙanwa haka ta ɗauke ta, duk da dai itama tana kishi da Meenal ɗin, ko dan sabo da yadda Mijin nasu hankalinsa yafi karkata akan Meenal ɗin, komai yace ita duk randa zai koma ɗakin ta uban kowa se yaga kalar rawan ƙafan da yake, amma duk sanda ze bar ɗakin nata kuwa kusan kowa se yasan yadda baya son ya baro ɗakin nata, in me girkin ma batai wasa ba ranar ko kallo bata ishe shi ba, amma fa idan ta tanka masa, don duk da hakan yana ƙoƙari sosai don abinda yake zasu daga yarinyar shi kadai yasan kayansa. To amma sedai takan danne hakan itama ta kuma yi adda'a, amma banda shugaba Raƙabiya da ake kwasar yan kallo da ita... Tin wajen ƙarfe tara saura yake zamar jiran shigowarta har gashi yanzun wajajen goma saura, don haka ya miƙe ya nufi Part ɗinta ya shiga ba kowa palourn kuma palourn a share yake sai dai ba wani ƙamshin da kullum baka raba parlourn dashi, bedroom nata ya nufa kai tsaye kwance ya same ta ta dugungune a cikin bargo, da sauri ya isa gaban gadon yana kaiwa zaune, hannunsa ya ɗaura a gefen wuyanta Jin zafi rau ne yasa shi faɗin "Baki da lafiya Meenal amma shi ne baki fada min ba?" Rintse idonta tai hawaye suka silalo tace "Daddy na ƙira ka ai amma bai shiga ba kuma wayar tawa ta mutu ban sa a charge ba" takai ƙarshen maganar a mugun wahalce. Ɗan shiru yayi na wani lokaci kafin ya miƙe yace "Bara na dauko mukullin mota muje hospital, ai zama da jinya babu daɗi...." Yay maganar yana fita, babu ɓata lokaci kuma se gashi ya dawo hannunsa riƙe da car key, da kansa ya taimaka mata
ta saka kaya ya tallafota suka fice zuwa compound na gidan, da ko ina hasken solar da bata jima ba aka gyara, suna gaf da isa gaban motar se ga Raƙabiya kamar wacce aka cillo daga sama, kallo ɗaya ya mata don haukarta tayi yawan da ko tanka ta baya son yi, gaba ɗaya yanzun kaff gidan itace me basa ciwon kai. Be kula ta ba sema kwantar da Meenal da yayi akan kujerar motar, kana ya zaga ɓangaren me zaman banza yaja motar suka fita, kai tsaye wani private Hospital ɗin dake nan kusa da su ya kaita, sai da ya buɗe mata file sannan suka shiga gurin doctor ɗin.
Ƴan tambayoyi tai mata dake Dr ɗin macece kafin ta kira nurse tace suje ayi mata test, nan suka je aka mata shi dai Alƙali Yahaya yana ta adda'ar ALLAH yasa ciki ne da ita, sedai saɓanin hakan ya samu don cewa sukai maleria ne ya mata yawa. Magunguna aka basu suka koma gida, anan ɓangaren nata ya kwana yana kulawa da ita, washe gari bayan ya dawo daga sallar subhi ya dawo se ya ɗan janwota jikinsa bayan ta gaida shi yace.... "Wai yaushe zaki bani baby?, ina son inga kin haifa min baby kyakkyawa me kama dake..." Kanta ta sunkuyar tana wasa da yatsun hannunta tace "ALLAH ne be kawo ba amma nima ina so ai..." "ALLAH ya kawo mana masu albarka" yace yana fita kai tsaye don shiryawa ya tafi wurin aikinsa.
Sannu a hankali ababuwa suka fara cakuɗema ma Meenal a gidan, ga yara da kamar ma turo su ake takanas su mata rashin kunya, in abu ya sayo irin duk gidan nan se an ga dama za'a raba da ita, gashi yanzun kamar sun haɗe mata kai ne, bata da wata kyakkyawar sukuni a gidan, tin bata kai masa kara har ta fara don ababuwan sun fara fin ƙarfin, ga wata shegiyar rama da tayi ita ba wacce tasan jinyar laulayi take ba, tin a wasu ababuwan yana bin bayanta yana bata kariya harta kai ta kawo yanzun se dai ma ya hauta da faɗa da masifar cewa da shi duk be san wasu ababuwan nan ba se da auro ta, shifa yanzun wani bin har dana sanin aurenta yake, gaba ɗaya ta gama ficewa a hayyacinta gashi tin da aka yi auren zuwanta gida befi uku ba, don matsin lamba ce dashi wajen fita, kuma baya taɓa barin ta wuni sedai taje da magribar fadi isha'a yaje ya ɗauko ta, wai a hakan ma ada ɗin kenan yanzun wani bin ma girkinta yakan shiga har ya fita bata saka Alƙali a idon taba, kafin taje ya rufe ɓangarensa wanda tin abun baya mata ciwo har shi ma ya shiga sahun daya sake figar da ita, idan kaga yadda ta tsige ta rame zaka ɗauka DEEPIKA PUDAKUNE ce farkon shigarta BOLLYWWOD dan rama, ko ina se ƙasusuwa da ƴan hakwara likely dai tamkar deepika ɗin ga duk wanda ya mata farin sani farkon fara film nata lolz🤩. A lokacin da Shareefah ta mata zuwan ƙarshe da kuka suka rabu ita kuka itama kuka, amma tace karta faɗama Baffansu ko yaya Sadeeq su tashi hankalinsu, gashi shirye shiryen bikin Shareefah ɗin da Bilkisu ake lokacin, dan dama kusan fikon turakane tsakaninsu. Ko da ta koma gida adda'a ta dukufa yima Sister ɗin nata kan ALLAH ya yaye mata dukkan abinda ke damunta, in kuma rabuwar su ce alkhairi Ubangiji ya bama kowa hakuri don idan wata ukubar tayi yawa rabuwan shi yafi alkhairi... Ita kuma Meenal a nata ɓangaren ba taji zata sare ba, za taci gaba da juriya da hakuri In Sha ALLAH, don bata son aurenta ya sama matsala se adda'ar itama data riƙe da nafilfilu kuma har lokacin ko ɓatan wata bata taɓa yi ba a gidan. Komai take cikin ƙarfin hali da ƙarfin zuciya take, wanda hakan har bama Shareefah mamaki take, don ta sha tambayarta ita kuwa wanne kalan ƙarfin hali ke gare ta, takan yi murmushi a lokacin tace mata. _Wani lokacin muna murmushi ne domin kar duniya tasan ciwon dake cikin zukatanmu.._