← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 36

Sashe 19

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wani kallon zallar tausayin ɗan nata Ummeh ta shiga binsa dashi, A cikin zuciyarta tana jin inama ace wani na iya ɗauke damuwar wani, da kuma ciwon wani,da ita kuwa tabbas ita ce uwa ta farkon ta zata fara ɗauke duk tarin abubuwan yaron nata, ba tare da ko shi kansa ya san da hakan ba. Idanunta ne ya ciko da hawayen tausayin ɗan nata. Maganar Ayla ne ya sake katse duk tunaninsu da tace. "Papa shike nan nima zan mutu ne irin na Maama narhhh ko???" Da sauri Majeed ɗin ya rufe mata bakinta shima yana danne nashi bakin da ɗaya hannun sa da yaji kukan shima na dab da subce masa. da sauri Ummiensa ta miƙe daga wurin da take tana faɗawa kitchen itama, Ikleemerh ce tayi ƙarfin halin isa gare ta tana shirin ɗaukarta daga wurin mahaifin nata, dakatar da ita yayi ta hanyar girgiza mata kansa, rungume kanta yayi sosai yana tunawa da Ameenatou mahaifiyar ta, Wanda yake mata wani irin mahaukacin SO da ƘAUNAR da be taɓa tsammanin zema wata halitta bayan taba. Ɗaukarta tsam yayi yana yin woje da ita bayan ya furta mata. "Ba zaki mutu ba In sha ALLAHU Ummiena...." Dake sunan ummin ameenatou ɗin tace yasa mata, wanda shi kuma da ita ya niyar yima takwarar, amma tace ita dai ya saka sunan ummien, idan ta sake haifa musu wata Babyn ya saka nata sunan amma ummien first kafin ita. Kai tsaye wajen parking manyan motocin gidan ya nufa, wata Black Bentley ya faɗa tana jikinsa yake driving zuwa hospital. Yana zuwa shi da kansa ya wuce da Ayla wani special room ya ɗaura mata ruwa, bayan wani lokaci ya cire mata ya ƙira wani Dr Saif ya kwanta yace ya zuƙi jininsa ya ƙarama Ayla da nata yayi ƙasa sosai, ana dibar jinin nasa ya miƙe zaune tare da ziro ƙafafunsa ƙasa ze sauƙa, saurin dakatar dashi Dr Saif ɗin yayi yana me furta. "Zaka ɗan huta ne Sir. Domin akwai buƙatan ka huta ɗin, zan maka allura ne.... Da hannunsa yayi amfani wajen dakatar da Dr ɗin daga dogon sharhin da yake koro masa, kafin cikin zurfin murya yace. "Bana buƙata...." Daga haka ya fice bayan ya ƙira pooja yace ta kula da Ayla. Kai tsaye ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa, zuciyarsa na masa bugun da bai san kona minene shi ba, Sedai yana zuwa yaga bata nan, ya jima yana ta dube duben inda zai ganta amma be gani ba, duk da zurfin cikinsa amma se da ya magantu ya tambaya wata nurses, "Mr MAANAL FA?...." Da farko da nurses ɗin daburcewa tayi don bata san wacece kuma Mr MAANAL ɗin ba, har seda ya dafe goshinsa kana yace... "Dr ameenatou...." Jikinta na ɗan rawa da bakinta tace. "Mijinta ya zo ya tafi da ita...." Rumtse idonsa yayi yana rike kansa dake ɗan sara masa yana soma haɗa hanya ya fice a room ɗin. Drectly office nashi ya wuce yana zubewa saman doguwar kujera, Kai tsaye wani hawaltaccen bacci nayin gaba da shi, masu cike da kalan wasu surkullen mafarkai marasa kan gado....
Wajajen sha biyu ya farka a firgice sakamakon wani irin mummunan famarkin da yayi, Rumtse Idanunsa yayi gamm tare da ƙara ƙankame jikinsa wuri guda,a ƙalla ya ɗauki sama da minti uku zuwa biyar kafin ya saki ajiyar zuciya. Amma baiyi motsin kirkiba balle kuma ya iya furta wata kalma. Sosai mafarkin ya firgita shi, in banda tsuma babu abinda jikinsa ke faman yi sai uban zufar dake yanko masa ta ko ta ina. Idanunsa da suke a lumshe ya ware tare da ƙurama wuri guda ido tamkar Anan ne za'a faɗa masa fassarar mafarkin da yai. Kafin ahankali ya riƙe kansa da hannuwansa biyu da yake jin tabbas yana gaf da samun matsala, indai har zaici gaba da shiga irin wannan attack ɗin. kwanciya yayi daga jikin sofar don gani yake daya koma ɗin mafarkin da yai zai kuma maimatuwa ne. "Ya Rabb" ya faɗa yana ci gaba da adda'o'i cikin ransa... Ya dau lokaci zaune a hakan kafin ƙarar shigowar ƙira cikin wayar nasa ya sanya shi buɗe idonsa da suka gama galabaituwa sosai, Ahankali ya janyo wayar tare da shafa screen nata, take kyakkyawar Pics na Ayla ya bayyana. ganin sunan Dr Bilal ne ya sanya shi
ɗaukan wayan ba tare da yace komai ba yayi shiru. Kamar da 3 minutes ya janye wayar daga kunnen bayan ya furta. "Karka dawo ka tabbata a airport ɗin indai se nazo ɗaukar kane...." daga nan ya shige bathroom babu jimawa ya fito ɗauke da alwala, kai tsaye yana fita zuwa masallacin da ake daf da shiga sallar ma. Bayan idar da sallar ya nufa ɗakin da ya kwantar da Ayla, yana tafe yana duba Rolex ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa a nutse, don ƙa'idar sace yin komi akan loƙaci tamkar yanda ya gama gindayama kansa, don aganinsa bashi da loƙacin ɓatawa lokaci lokacinsa, komi yana yinsa ne akan loƙacinsa ba tare da wani ya shiga cikin woni ba, donshi mutum ne mai tsananin bin kowacce ka'ida acikin dukka lamuransa da taka tsantsan, kai tsaye har an zare mata jinin da aka sa mata an gyara ta harda wanka, ɗaukanta kawai yayi bayan ya furta ma Dr pooja ɗin "Thanks!" A samar lips nashi ya fice da ita, be ko bi ta kan office nashi ba ya wuce wurin motarsa. Seda ya fara kwantar da ita dake bacci take har yanzun be gama sakin taba, ya zaga ze shiga driver sit kenan sega Bilal nan ya nufo wurin yana masa tsiya, "Banza da wani bauɗaɗɗen halinsa, da baka ɗauko ni ba gani na kawo kaina se ka mutu...." Ko kallar inda yake bai yi ba ya faɗa cikin motar yana mata reverse yabar wurin. Kansa kawai Dr Bilal ɗin ya girgiza a ransa yana cewa. _ALLAH ya taro ka ABDOUL-MAJEED...._ daga nan yayi cikin asibitin.....
★..
Tun da ya ɗauko ta daga Asibitin ta rufe kanta a ɗaki take kuka, kuka irin wanda ke gasa da soya zuciyar me yin sa, kukan baƙin cewa wai ita AMEENEERH SHEHU USMAN yau ƙaddara ta tsara mata ke ɗauke da ciki!, cikin wanda ya mata fyaiɗe tin da ganan watan cikin huɗu da kwana biyar ɗin da abin ya faru, ta gwada paisoning ɗin kanta yafi sau uku, idan ta tuna ko ta mutu bawai ta huta ko ta tsira bane, Wannan dalilin yasa ta gama tsarama kanta za ta tsaya ta fuskanta rayuwar, tayi gwagwarmaya ta jure ta daure ta cinye duk wani maɗacin da duniyar da abinda ke cikinta zata basu, ta gode ALLAH da tin da abin ya faru ko sau ɗaya Ahmad ɗin be taɓa koda kwatankwacin kusantarta bane, Idan kuma ta tuna cewar zasu rabu ne a duk lokacin da cikin jikinta ze bayyana tana jin kamar ba zata iya jurema hakan ba. Ahmad ɗin da tunda ta rufe kan nata yake ta famar Safa da Marwa kamo ɗakinta kamo ɗakinsa, yana cewa ta buɗe masa don ALLAH!, ta buɗe ze yafe mata komai, ze dawo suci gaba da gudanar da rayuwarsu irin ta baya, ze manta komai, ze shafe komai kamar komai ɗin kuwa be taɓa faruwa ba. A lokacin da maganganun nasa ke dukar cikin kofofin kunnenta kuwa kukanta tsananta yake, tana jin ta gama yafe kanta ta kuma haramta daga gare shi, yin Duniyar yayi ta buɗe masa amma ta ƙi ya, Dole ya kira Ya Sadeeq yazo har gidan amma taƙi saurar kowa daga cikinsu, Ina samm bata jin zata iya buɗe musu wannan ƙofar, ko kuwa so suke ta buɗe tace musu ciki ne da ita?, cikin da ba na mijin taba?, haba abin yayi munin da bata jin zata taɓa buɗe musu wannan ƙofar a dai daidai wannan lokacin ɗin.Suna tsaka da wannan danbarwar sega ƙarar jiniyar ƴan sanda nan ta gama karaɗe ilahirin gidan baki ɗaya, wanda jiniyar gaba ɗaya ba ƙaramin tasar hankulansu yayi ba,se dai banda ita. Don jima tayi kamar an yaye nata dala ne bisa kanta, tasan zasu tafi da ita ne bisa mutuwar mutumin da tasan ita ce sanadin hakan. A ruɗe Ya Sadeeq da Ya Ahmad ɗin suka isa ga harabar gidan, Suna zuwa wani baƙi murjejen ɗan sandan da kana kallonsa kasan babu imani tattare da shi yace. "Ina mai laifin kisan take?" Wani kalan mugun shock ne ya ziyarci Ya Sadeeq da bai san da zancen komai ba. Don haka ya duba Inspector ɗin tare da furta. "Ƴallaɓoi ko dai kun yi ɓatan kai ne?" Jajayen idonsa Inspector ɗin ya zaroma Ya Sadeeq ɗin yace. "Ba nan ne gidan AMEENEERH SHEHU USMAN ba?, Matar AHMAD IBRAHIM SHAREEF?" tin da ya kama hasalin cikakken sunanta Ya Sadeeq ɗin ya gama sallama wa, Kafin ya juya ga Ahmad ɗin don yana buƙatan ƙarin haske dangane da maganar kisan da tazo masa a matuƙar bazata kwatsam lokacin guda. A takaice Ahmad ɗin ya bashi labarin abinda ke faruwa daga jiya zuwa yau, har musabbabin ƙiran da ya masa ɗin kuwa. Jikin Ya Sadeeq ɗin ne ya fara wata kalan rawan tashin hankali. Kafin ya kalla Inspector ɗin yace. "Ƴallaɓoi zaku iya tafiya dani, domin wacce kuka zo wurin nata bata da lafiyar da ko fitowa da kanta ba zata iya ba, amma ni yayan tane, zaku iya tafiya dani duk hukuncin daya kama nata a min ciki kuwa koda rataya ce...."

"Gani nan da lafiyana Sir!, ni zaku kama domin kuwa ni ce mai laifin!!!..."
Chapter 19 · 0% Book details