Sashe 28
Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tana karantawa wani kalan kuka ya taho mata a guje amma tayi hanzarin sanya hannunta ta toshe bakin. Wani kalan rumtse idonta tayi tana ƙanƙame wayar nata cikin jikinta, tana a wannan yanayin se ga shigowar Shareefah a guje da kuka ta faɗa jikinta, wani kalan kuka Shareefah'n ta saki tana rungume yayar tata cike da ƙauna da tausayi me tsanani, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³" Meenal ɗin tayi ƙarfin halin kamawa tana maimaitawa don ƙanwar nata ta ɗauka. Aikuwa ta kama suka ringa maimaita har zuwa lokacin da zuciyoyinsu suka ji sun yi sanyi, "Mummunar ƙaddarar data sake samun mu Kenan Yaya?, haka ALLAH ya sake wanzar da ikonsa akan ki kenan?, ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALINNNN koda yaushe, zamu ci gaba da ambatar kalmar cikin kowanne irin yanayi In sha ALLAHU...., Kiyi hakuri In sha ALLAHU wannan ma zai wuce yaya.." wani murmushi me ciwo tayi a matsayinta na wacce take amsar roldin uwa ta shiga kwantarma da Shareefah'n hankali, cikin muryan da yayi laushi sosai take shafa gadon bayan Shareefah ɗin ta ce. "ALLAH ma ya tsare My freind,komai yazo mana cikin sauƙi da amincinsa, ciki kuwa ya fita duk da kuwa cewar naso kayana,amma bana da ja ko hukunci akan duk abinda Ubangiji na ya zartar a kaina. ALLAH Ubangiji ya sake zama gatan mara gata yaci gaba da shiga cikin al' amurranmu yana zame mana jagora a koda yaushe..." Haka taci gaba da kwantar ma da ƙanwar nata hankali har seda taji Shareefah ɗin na maida numfashi a hankali alamun barcin ya ɗauketa, har tana sauƙe ajiyar zuciya kana yaji hankalin ta ya kwanta sosai, Itama se tayi ƙoƙarin zame kan Shareefah ɗin ta mayar mata kan pillow da gefen kafadarta tayi, sedai cikin barcin Shareefah'n ta ƙara janyo yayar nata jikinta tana gyara kwanciyarta a jikinta amman idonta dai a rufe, shiru kawai tayi tana bin ƙanwar nata da tayi lif a jikinta tana sauƙe ajiyar zuciya, gashi bata son ta farka haka kawai take jin bata son ƙanwar nata da kowacce kalan damuwar da zata sake zuwar mata, koda da misƙala zarratin ne, barin ma kalan wannan ɗin da yazo musu hagunce, ba tare da sunyi zata ko tsammanin hakan ba.Tunani barkatai taci gaba dayi akan rayuwarsu har ƙarfe kusan biyar da rabi, kana ta shiga motsawa ahankali, shiru kawai tayi har ta gama tashi bata motsa ba, adda'ar tashi daga bacci tayi a hankali tana zare janye jikinta a na ta, ƙura mata Ido tayi ta cikin ɗan duhun magrib ɗin daya kawo kai. Duk da irin tsananin damuwar da yayar nata take ciki amma hakan bai hana Kyan nan nata fitowa ba, fuskan nan sai glowing na kyau takeyi ko ina kuma a jikinta fresh, kana ta miƙe ta shige toilet bayan tabi yayar nata da adda'ar gamawa da duniya lafiya. Duk abinda Shareefah'n keyi kuwa a ɓangaren Meenal ɗin tana jinta, shiru kawai itama tayi ƙaunar ƴar gudaliyar ƙanwar nata na sake kamata, tana kwancen idanunta a rufe har Shareefah ta fito daga wankan, itama se taji bata son tashin yayar nata ƙara ta barta ta ɗan huta ko taji rangwame da sassaucin abinda ke sukar zuciyarta. Ita kuwa Meenal dake daga kwancen idanunta lumshe har bama tasan taja lokaci har haka ba, se da taji anata ƙiraye ƙirayen sallar magrib, da sauri ta mike tana fita itama, alwala tayo tazo ta tada sallah bayan ta idar ta ɗan kishin gida saman dardumar. Lumshe idonta tayi ababuwan da suka faru na sake nemar dawo mata daki daki, saurin kawar da tunanin hakan tayi tana lalubar kalmar YA WADUD tayi ta maimaita da kuma HASBIYALLAHU LA'ILAHA ILLA HUWA, ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHEEM AZEEM.... Tana nan zaune har aka yi isha'a kana suka fita tsakar gida da Baffa ya leka da kansa har ɗakin yace su fito suci abinci, duk jikinsu babu me kwarin gwiwar cin abincin amma haka suka fito, ALLAH yaso ma bame nauyi bane, yau matar gidan bata ga damar yin tuwo ba, jallop ɗin taliya da maccaroni tayi, se ruwan shayin data haɗa musu dashi, plat guda aka zuba musu me ɗan girma Meenerl tayi hanzarin cewa a rage amma Baffa yace suci iyaka cinsu in sun yi sauran a bama ko almajiri ɗaya ne. Rabi kuwa basu ciba duk da cewar yadda taliyan tayi daɗi, shayin dai sun sha da ɗan yawa kana aka ɗan taɓa fira wacce mafi yawanci nasihohi suka fi yawa, sai wajajen tara da rabi kana suka yi sallama kowa ya nufi makwancinsa, nan fa yauma baccin nan yaso yama Meenal gaddama, don kuwa yace baisan zance ba, amma albarkacin Shareefah da Adda'ar data fara tofa mata sama sama har bata san lokacin da baccin yayi awon gaba da ita ba, ba tare data san sanda ya ɗauke tan ba.
Washe gari suna tashi bayan sunyi sallar asuba suka sake komawa se wajajen bakwai suka tashi, tare suka fita zuwa tsakar gidan duk kuwa da yanda Shareefah taso Yayar nata ta sake hutawa amma tace ta barta, idan ta barta a ɗakin ita ɗaya bata jin daɗi ne, haka suka kama aikin gidan a tare, se Shareefah'n ta kama shara wanke wanke tace Meenal ɗin tayi musu abin kari, kitchen nasu ta shige ta ɗora musu farar taliya ƴar Hausa da manja, ganin yajin gidan se a slow ne ya sa tayi saurin daka me daɗi kana ta sake ɗora musu ruwan tea yaji kayan ƙamshi. Tana gama dafa musu tea ɗin ta juye a flask, kana ta gyara komai data bata ta ɗebi ruwan zafin data ɗora musu ya yawa ta shiga wanka, tana fitowa Shareefah ta shiga itama, bayan ta gama shafa mai wata doguwar riga ta zira ta yadi kana ta fito daidai shigowar Shareef. A zaune taga Baffansu saman tafarma, tsakar gidan nan yayi ƙal ƙal gwanin birgewar sharar da yasha, gefensa gwaggo Sadiya se famar hamma take tana wani murza idon daya bada alamun yanzu nema take tashi a baccin, ɗan murmushi kawai Meenal tayi tana ƙarasa fitowa cikin kaunar ta take ma Baffanta da baya taɓa ɓoyuwa a fuskata tace "Barka da safiya Baffa!". Murmushi yai me kyau yana me furta. "Barkanmu dai Ameenatou!, fatar kina lafiya?" "Lafiya ALHAMDULILLAH" ta bashi amsa tana tashi cilak ta ɗebo musu kayan karin, gwaggo Sadiyan ce ta zuzzubama kowa kana ta ɗauka nasu da niyar shigewa ɗaki, amma Baffa yace ta dawo ta zauna yana kwalama Shareefah ƙira kan tayi tayi ta fito, don ya santa da nauyi akan komai. Bayan sun karya kana suka miƙe suka nufi ɗakinsu. Kallon Shareefah dake shirin kwanciya Meenerl tayi data riƙe bakin ganin wai kwanciya ne ma za tayi, "Ke Shareefah baki san zaki iya makara ba?" Kallonta Shareefah'n tayi tare da cewa "Wai me kike nufi da nine Yaya Meenal?, nufinki daga zuwa yau ɗin shikenan se in ɗebi jiki in koma yau kuma?, cab wllh da sake, ai sena cinye satin nan tsaf tare dake..." Murmushi Meenal ɗin tayi me cike da dattako tace "Yanzu ke Shareefah ko wani yace ki zauna ki cinye satin seki yarda ki zauna karatun duk da aka muku ya tafi a banza?" Turo madaidaicin bakinta gaba tayi kana tace. "A tinaninki kenan ai, ga yawa ne nan ta waya zanka amsar duk lesson ɗin da ake mana...." "To ai shikenan, ke kuma ALLAH ya taro min ke..."
★..