← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 36

Sashe 5

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

ꨄ Tana isa cikin asibitin kai tsaye office na Dr pooja ta wuce, wasu ayyuka ta ɗan bata ita kuma tana yin ɗakin wata me haihuwa da aka kawo, tun cikin dare ta kasa haihuwar da kanta shine ma abinda yasa take tunanin ko C/S ma kawai za'a mata, don tana matakin ƙarshe ne don tana 1/cm haihuwa a koda yaushe, amma gashi abu ɗaya ake fama tin wajajen karfe 7 gashi kuma yanzun har goma na nemar wucewa ma, labcoat nata ta zira da handglov a hannunsa ta sake nufar delivery room ɗin da matar ke ciki, tin kafin ta kai ga ƙarasa shiga room ɗin take jin ihu da salatin matar na tashi, goshinta ta dafe tana ƙarasa shiga da ɗan hanzarin ta, handglov ɗin dake hannunta ta sake gyara zamansa tana kai hannunta ƙasan matar dake kwance saman gadon masu haihuwar nan, ganan dai kan jaririn ya ɗoso sedai daga uwar har yaron ko yarinyar dake cikin cikin kowa fafatuwar tsira da rayuwarsa yake, ita tana son taga tayi duk me iyuwa ta yunƙura koda ta numfashi ne abinda ke cikin cikin nata ya sama damar fitowa, shi kuma dake cikin shima yunƙurin yaga ya fito ɗin yake, wata nurses ta ƙora Damaga kan ta haɗo mata allurar naƙuda kawai tama matar, kanta matar ke jijjigawa gafa ɗaya gumi ya gama jiƙeta sharkaf, da kyar ta iya samun bakin furta. "Karku daura min ruwan naƙuda ina da sugar da hawan jiniiiiii...... San...sa...sa....san...nan...ina da raunin zuciya....." Duk wannan abin da take yi cikin fusgar numfashi take da haki.. gaba ɗaya ta gama saddakarma rayuwar ta gama sallama cewar shikenan ita nata ajalin yazo, don haka ta shiga adda'a 'o'i masu kyau da girma idanunta na ƙoƙarin lumshewa, su kuma gaba ɗaya ma ɗakin sun rasa abinda ya kamata su mata, don haka kawai Dr pooja ta fita babu jimawa se gata hankali a matukar tashe da file na saka hannun mijin matar dake can haraban asibitin yana ta safa da marwa yawa me dawafi. Abinda ze baka ma dariya ƙafansa ɗaya da takalmi ɗayan kuma babu faɗi yake. "Don ALLAH NA'EEMERHTOU karki tafi ki barmu!, ki taimaki rayuwar yaran mu dake dani Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ³" haka yake ta famar ambata gaba ɗaya shima ya gama jiƙewa se kace shi ne me haihuwar, gefe can kuma dashi wasu mata ne biyu kowannensu ya buga uban tagumi kowa da abinda ke damunsa. A can ɓangaren Meenal shigar Dr pooja office ɗin ta hankali tashe da kuma fitar ta ne itama ya tashi hankalin ta, don haka ta mara mata baya, bayan ta ɗora labcoat da handglov a hannunta koda ALLAH yasa zata iya musu da wani temako ne haka, gaba ɗaya zuwa lokacin kuwa har Dr pooja ta kammala duk wani shiri nata na fara surgical ɗin, harma an nufi surgery room da matar. Lokacin da take kaiwa ainihin room na Surgery room ɗin har pooja ta ɗora Scissors nata saman cikin matar da numfashin da take shaƙa ma na Oxygen ne, don tuni rauninta yayi ƙasa sosai dole se da taimakon oxygen zataci gaba da numfashin. "Wait a minute, ma'ame..." Haka Dr pooja ta tsinkayi muryan Meenal, dakatarwar kuwa tayi tana isowa ita kuma. Cewa tayi pooja ɗin ta taimaka mata da sabuwar rezor, seda ta sake risinar da kanta tana juye baki cikin yaren Ingilishi tace da ita tayi haƙuri ta shiga cikin hurumin da ba nata ba, ba komai tace da ita, don haka kai tsaye ta saka sabuwan rezor ɗin tana ɗan yankar ƙasan matar, da komai bata ji ba sakamakon allurar kashe jikin da aka mata, oxygen ɗin dake hancin matar Meenal ta zare kaɗan tare da ɗan ɗago kan matar kamar zata zaunar da ita ta kuwa takarkare ta saki wani zazzafan numfashin dake kumshe cikin bakinta ya fashe, wanda dama ita Meenal ɗin hakan take son samu daga matar, daga ƙirji zuwa cikinta ta ɗan danna tare da sake mata irin ta ɗazun bayan ta mayar da ita ta sake ɗago ta, aikuwa a wannan karon ma ta sake yin irin na ɗazun, haka har suka yi karo uku, ana huɗun kuwa tayi wani kyakkyawan nishin da kai tsaye ya taho da yaron dake cikin, hannunta ta saka duka biyun tana ƙarasa janyo yaron ya fito kuwa da assalatunsa, wato kuka irin na jarirai sabuwan haihuwa, suluf haka matar taji jikinta ya koma kamar wacce aka sauƙe mata cutar shekara da shekaru, tana meda wasu numfarfashi, kafin ta tafi zuwa duniyar sumewa... Dama tasan za'a yi hakan duk da cewan bata taɓa amsar haihuwa ba amma kuma Alhamdulillah tana da kyawawan da bata mantuwa, don wannan ɗin duk cikin interview ɗin da aka musu ne na irin dabarun haihuwar da tayi gaddama, kuma Alhamdulillah tayi nasara wanda dama se irin kamar ana daf da yima mutum operation ɗin ake son yin hakan, wanda ita da classmate nata sun sha gwada hakan akan kansu da numfashin da suke gumtsa su fesar idan an zame oxygen ɗin, kamar yadda tayi tama matar. Dr pooja ce ta rumgume ta tana furta "Ohhh jesus Today I saw a young lady who was thoughtful and knew her job well.Thank you Jesus.... Thanks u Maanol....." Dake haka tin jiyan take ƙiran ta dashi wato Maanol ɗin. Ko kafin kace mene se gashi tuni har an gama shelanta wa duka sauran Dactor's ɗin dake cikin hospital ɗin cewa ga wata ƴar baiwar likita sun samu me matsakaicin year's. Cikin ƙanƙanin lokaci se gashi sunan Dr Meenerl Shehu Usman na nema yin shura tun a matakin farko, da kansa Dr Bilal ya ziyarci wurin ya kuma zauna da sauran Dactor's tare da Meenal kan fikirar da tazo musu da ita, nan kuwa ta tashi ta ringa musu bayanai daki daki, wanda daga ƙarshe suka gane cewar lallai ashe ba se iyaka private school's bane suke jajircewa wajen koyar da ɗalibansu ba, nan mijin matar ma ya bada wasu kuɗi masu ɗan gwaɓi yace na likitar data ceci rayuwar matarsa ne da kuma abinda ke cikin ta,duk da kuwa kasancewar tana a Cold room ne. Wato ɗakin sanyi amma kuma ai tana ci gaba da shaƙar numfashin daba na oxygen ɗin bane, ga kariyar da aka haifa ɗin tazo cikin ƙoshin lafiya abinta, dake dama tun a lokacin ta gama wa matar ɗinki,don haka yaci gaba da kulawa da marasa lafiya a fannin haihuwa, kowa se kaji yana don ALLAH a ƙirawo masa Dr Meenerl shima tazo ta taimake shi, wanda ita abin ma yake ɗan bata dariya, wato ma ita ne zata temakesu ba ALLAH, ko dan ance me ciwon haihuwa tamkar zautacce haka yake komawa, duk abinda yazo bakinsa faɗa yake. Ba itane ta koma gida ba yau se wajejen ƙarfe 7:30pm, tin kuma 7:15am data fito. Dake dama tayi waya da Ya Ahmad ɗinta cewar yau kar ya biyo da wuri se after magrib ze biyo ya ɗauketa, SO shi kuma lokacin Hajiyarsa ce tayi ƙiransa dole haka ya tafi yace ta biyo napep amma karta yarda ta hau machine... Koda ta dawo ta tarar ya dafa musu farar shinkafa da yaji, ta wani cunkule ƙaramin bakinta kuwa don ita ba Sosai take son farar zallar shinkafa da may da yaji haka ba, har ƙara ya musu couscous ko noodles da egg, haka bayan tayi wanka tana ƙananun ƙunƙunai tana komai ta tuttura abincin... Wayarta ta ɗauka bayan sallarn isha'a ganin be shigo ba ta shiga WhatsaAp nata da duk wunin yau bata hau ba, da test messages na Shareefah ƙanwarta kuma babbar aminiyarta ta fara cin karo, don haka ta shiga, voice note ne don haka ta kunna tare da kaiwa kunnenta ta saurara. Wata ijiyan zuciya ta sauƙe lokacin data kammala sauraran voice note ɗin, kafin itama ta fara mata nata voice ɗin. _Look Shareefah ina son ki kwantar min da hankalinki kinji, ki kuma ci gaba da haƙuri bana son kika sanya wata damuwa daban a cikin ranki, kinsan koda ace da ran Ummanmu ba zata so ganinki cikin damuwar hakan ba, kuma Baffa yana daidai gwargwadonsa a kanmu tsakanin mu da gwaggo Sadiya, kuma ke ba karatun ki ma kike ba, don ta hana ki abinci kuma se yaya ina ce kusan duk bayan 2 weeks nake saka miki kuɗi a account naki?_ daga nan ta tsaida voice ɗin, babu jimawa kamar da 5 minutes sega wani voice ɗin na Shareefah'n ya sake faɗo mata. _Aunty Ameenatou ba wai rashin hakuri ko rashin kaiwa zuciya nesa bane, kin san ni ina son naga anyi komai cikin tsakani da ALLAH, bana son cuta ko zanba da zagon kasa irin na gwaggo Sadiya, matar nan makirace wllh, bayan rashin bani abincin da bata yi ina jinta ranar tana cema Baffanmu wai na dena cin abincin gidan, haka ta ɗebo kwanukan abinci kusan na kwanaki biyar ta dire a gabansa wai bana cin abincin ya tuhumeni wai a ina nake samar kuɗi?, kin ji fa, karki ga yadda baffan kuma ya wani rutsani wai in faɗa masa inda nake samar kuɗin, alhalin gidansu Yaya Jafaru nake shiga inci wajen mamarsu......_ wata doguwar ajiyar zuciyan dai again ta sake sauƙewa a cikin zuciyarta tana ayyana wai se yaushe gwaggo Sadiyan zata san cewa Annabi ya faku ne?, se kuma zuwa yaushe zata gane gaskiyar dake bayan ƙarya?. Wani voice ɗin ta mata tana ce da ita taci gaba da haƙuri zata ma Yaya Sadeeq babban ƴaƴansu kenen maganar, kuma itama yanzun ganan wasu ƴan kuɗaɗe zata turo mata daga wanda mijin matar nan ya bayar a bata, shi ne ta raba uku ta ɗauki kaso ɗaya biyun ta ce su Dr pooja ɗin su kasa suma, gashi alert nata na wata har ya shigo mata wajen dubu ɗari huɗu da arba'in da biyar. Dake su haka al'adansu yake a ranar da kaje aiki a washe garin ranar alert naka ke faɗo maka. 100k ta turo mata take aiko sega saƙon godiya nan daga ƙanwar nata harda kukanta, da cewar lallai ita ce uwa mahaifiyar da suka rasa itace kuma bangonsu se kuwa Yaya Sadeeq da shima ba'a barinsa a baya, duk da kasancewar ba wata gwaggwaɓar sana'a ke gare shi ba, amma kuma kusan kullum cikin rufin asirin ALLAH suke,don kusan shi ne ke ɗauke da gidan mahaifin nasu, kai tsaye suna kammala maganarsu da Shareefah ɗin ta laluba No na Yaya Sadeeq ɗin buga ɗaya ana biyu kuwa ya katse shi ya ƙirata, ɗan murmushi kawai tayi,don tasan dama ba wai ɗagawar ze yiba, amma kuma ze biyu tunda kamar hakan na masa nuni ne da tana son yin magana dashi kai tsaye, tana cikin wannan tunanin ƙirar nasa ya shigo mata, answering call in tayi tana kai woyar kunnenta. Gaidasa tayi yana tambayar lafiyanta, komai normal tace masa kana tace ta saka masa ɗari biyar a opay nasa ya sake data jarinsa, tif yaji wata wuta ta ɗauke masa duk da dai ba wannan ba ne karo na farko da take tura masa kuɗin ba, duk da kuwa kasancewar baso yake ba yace ta bari alhakin kulawa dasu na a hannunsa ne, wata numfashi me ɗan zafi ya furzar yana ce da ita a ina ta samu kuɗi har haka?, da har tashin farko ta saka masa dubu ɗari biyar?. Wata ƴar ƙaramar dariya tayi tana cewa. "Laaa Ya Sadeeq kana manta cewa yanzun na fara aiki ne halan?" "Kuma daga fara aikin naki shi ne har kina sama uban wannan kuɗin haka?" Fuska ta ɓata tana cewa. "Amma ai na faɗa maka cewar babbar asibiti ce, kuma tashin farko su suke fara biyar ma'aikatansu sabbi,kuma ƙarshen watar ma Dr pooja tace zasu sake sakamin 200k...." Wata yar gubtuwar murmushi yayi yana cewa. " Su kuwa wannan waɗan da irin masu kuɗi ne haka, da tashin farko su hankaɗo miki uban kuɗaɗe haka?, kana kuma ƙarshen wata ma su sake biyar ki har 200k?...., kuma halan ALLAH dai ma yasa kin shawarci Mijin naki, don a wannan fannin na sanki farin sani ba shawara kikayi da kowa ba, duk abinda ya miki kawai kike aiwatarwa..." Tsaye ta miƙe daga zaunen da take tana wani tura micil ɗin bakinta gaba tare da cewa. "To shi in na bashi ma me zeyi da kuɗi?, nasan ko da ace na bashin ma ba amsa ze yiba ai...." Sosai daga ta can ɓangaren Ya Sadeeq ɗin ya haɗe ransa yana cewa ze dawo mata da kuɗin nan lallai ta tabbatar ta fara shawartan mijinta kafin kowa, tin kafin ta ce komai ya datse ƙirar sega alert nan na kuɗinta na dawo mata har da ƙarin dubu ɗarin da take da tabbacin Shareefah ta faɗa masa shi ne ya haɗa ya dawo mata dashi, duk da tasan cewar bawai ze amsa na wurin Shareefah ɗin bane yayi ta aljihun sane, wanda tasan yanzun haka ya gama budget na abinda zeyi da kuɗin sa...
Chapter 5 · 0% Book details