← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 36

Sashe 12

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauri ta wani kalan dafe kanta tare da ƙoƙarin son ganin ta motsa idanunta ko yaya ne, amma hakan na ƙin faruwa sakamakon abubuwan da suka faru da ita ne kawai keta famar dawo mata a sabbin su....

"ALLAH ba zai taɓa ƙyale kaba, ku sani har da ku da kuka bashi goyon baya, zaku hulaƙanta!, za kuyi dana sani, ƘARSHENKU ba zai yi kyau ba, domin kun keta kima da darajar addininsa...."
Ta sake faɗar kalmomin domin ita a tunanin ta har zuwa lokacin a hannunsu take, "Kin makaro Ƴan mata, domin rising naki be amsu ba, uban wa ze ganki da shigar dake jikinki ya yarda ke *MATAR AURE CE?*, to ki sani idan ma ke MATAR AUREN CE se mun keta haddin ki, tun da shigar dake jikinki ita ce ta rinjayi ra'ayina a kanki har na kware miki, dole inyi abinda na gama ƙyasa shi a cikin zuciyata, dole ne in kwashi ganima yau...." Kalmar mutumin da fuskarsa ba zata taɓa goguwa a cikin idanunta ba ya faɗi hakan, yana fara yayyage kayan dake jikinta, dukansa da yaƙushinsa ta fara amma ba abin komai ba..... Da ganan sak komai nata ya tsaya shikenan nan wannan shi ne MAFARIN.....

Kanta ta riƙe ahankali taci gaba da processing farkawanta na farko!, da sumewar data ringa yi haka komai ya shiga dawo mata daki daki cikin kanta, wani kalan rumtse rinannun idanuwanta da suka kasa buɗuwa tayi, ga zuciyarta dake mata wani kalan zogi da ɗacin da ita kaɗai ce tasan iriyar ukubar da take amsa daga hakan, yanzun shikenan hakan yana nufin sun gama da ita kenan? Sun keta hijjaban dake lulluɓe da igiyar AURENTA kenan?, Yanzun shikenan Ya Ahmad rabuwa da ita zeyi kenan?, shin yana inama?, a wanne hali yake yanzun?, tasan duk inda yake baya ƙalau wllh, shi take son gani!, so kawai take ta gansa. Kanta taci gaba da jujjuyawa tana riƙe da kanta muryanta a kasa can sosai take wasu maganganu... Ƙarar tsoki taji an saki, kafin wata fusatacciyar murya ta biyo baya ta hanyar furta kalmar *"IDIOTS"* Bata san murya ko fuskan me maganar ba, don haka ta tattaro duk wani sauran kuzarin da take da tare da ambaton sunan ALLAH, tana buɗe idonta da a disashe suka ƙarasa kalle mata baya da gilmawar inuwar koma waye ɗin, bata zurfafa ko cilasta kanta ba, ta sake jan idanun nata ta kulle wasu zafafan hawaye su biyo bayan hakan. Sosai take ƙoƙarin dannar zuciyarta kasancewarta macece ita me dauriya, da shanye ko wanne irin ciwo da raunin dake cikin zuciyarta idan taso,don haka ko a yanzun ma take ƙoƙarin ganin ta danne hakan saboda ta taso yaƙi hakan. Wani kalan rumtse rinannun idanuwanta tayi a karo na babu adadi tana lallasar zuciya da gangar jikinta dake son bijire mata. Ita da kanta ga shiga bama kanta ƙwarin zuciyar shanye hakan ta fuskanta rayuwar da kyau, ta kuma yi gwagwarmaya tukuru wajen gyara rayuwa da gobenta. Don haka tayi luff idanunta lunshe, A yayin da ruhi da zuciya da gangar jikinya suke samun nutsuwa da hutu, mizanin yadda numfashinta ke sauƙa akan tafukan hannayenta tana tarar ruwan hawayen ƙarshen da In Sha ALLAHU ta gama zubar dasu kenan akan ƘADDARAR data afka mata, Kai bama iyaka ƙaddarar yau ɗin taɓa da duk wata sabuwar da zata zo mata cikin wannan duniyar zata jure, ta kumyi gwagwarmaya da yakar hakan, tafukan hannayenta dake riƙe da fuskanta da hawayen ke ci gaba da bi ta gefe da gefen fuskarta suna sauƙa a cikin tafukan hannayen ta rumtse, wanda take jinsu kamar ɗigar dalma a cikin zuciyarta, haka zafinsu ke ƙara birkita kanta da tunanin ta suna ci gaba da zana mata tabon ƘADDARAR da take kallar kamar ita da kanta ta sema kanta hakan. Wanda kai tsaye idan da ace wani zai iya tambayarta miye sanadin ƘADDARARTA?, Da kuwa kai tsaye zata ce dashi ita ce, wanda rashin bin dokoki da ƙa'idojinsa suka jaza mata, wanda taurin zuciya da zafinta da rudin zamani suka bi suna haɗawa duka waɗan nan abubuwan wuri guda su cakuɗe mata, harma suka mata taron dangin daya jata zuwa ga ƙaddarar ta, tabbas ta yarda ta kuma amince ita ɗin tamkar *MISALI CE* da ALLAH ya bar ma ƴan baya a kanta, tamkar kuma *IZINA CE* gamai hankali da tunani. Wannan yasa da wani kalan gudun ceton rai da fitar numfashi take ƙoƙarin danne zuciyarta daga son faso ƙirjinta da take son yi ta fito, wanda tama kanta alƙawarin cewa IN SHA ALLAHU ba zata taɓa barin hakan, ya zama shi ne destiny ɗin ta ƙaddarar data yi wa rayuwarta dabaibayi wajen fitar numfashinta na ƙarshe ba. Wanda zuwa lokacin wajen ƙarfe biyu na dare ne, Amma har yanzu hawaye bai daina zubowa daga Idanunta ba,kamar yadda lokacin ke wucewa haka hawayenta ke ƙaruwa maimakon raguwa ma.... Wannan hali da take a ciki ne ya sake haddasa bugun zuciyarta ya karu wani zazzafan zazzaɓin kai tsaye na kai mata farmaki, hakan ya saka Dactor's biyun dake duty saurin ƙarasowa gadonta suka danna mata allurar bacci, wanda da farko fin ƙarfin allurar nasu tayi ma, har seda wata data kasance musulma ce ta taimaka da tofa mata wasu adda'o'i kana baccin ya ɗauke, sedai masu cike da wasu muggwan mafarkai wa rayuwar...

Ƙarfe goma a cikin asibitin tama su Baffa dukansu tare da gwaggo Sadiya da Bilkisu, sedai basu faɗin musu hasalin abinda ke faruwa da Meenal ɗin ba, kawai sun ce bata jin daɗi ne, wanda se da ƙyar gwaggo Sadiyan ma ta yarda ta biyo su, don da cewa tai bata zuwa jinyar lallauyi dai kowa tana kansa, se ita ce dan raki da lalacin tsiya daga fara laulayin zata fara tara ma kanta jama'a da mutane. Se kawai suka bita a hakan suka taho, don su duka ukun suma kansu alƙawarin bisne hakan a iyaka zuciyoyinsu IN SHA ALLAHU. Zuwa lokacin kuma Alhamdulillah ta dawo daidai ɗin ta sakamakon kwarin gwiwa da zuciyar da ta ringa bama kanta. Har ma an dawo da ita normal room da kowa ze iya shiga ya ganta...
Shigowar Baffanta da Yayan ta da ƙanwarta dasu gwaggo Sadiyan ne ya saka ta binsu da rinannun idanuwanta tana kallarsu kamar wasu sabbin halitta, zama daga ƙafafunta Shareefah tayi a natse tana dafa kafaɗar Yayar tata ahankali, wanda ya sata ɗagowa a sanyaye ta juyo tana kallon Shareefah'n da jajayen idanunta da suke rine sosai har lokacin, Shareefah'n bata ce bata ce komai ba har na wani ɗan lokaci suna zazzaune a hakan, kafin Gwaggo Sadiya ta miƙe tana me furta. "To Ameenatou ALLAH ya sauwaƙe, dan tafiya zanyi, ni ban san a gidan makoki muke ba mun zauna munyi jigum jigum kamar wasu masu damuwa ko wanda iftila'in rayuwa ya afkawa... Bilkisu taso mu tafi dan zamu biya ta gidan Inna Marka mu dubata...." Da wannan Bilkisun ta miƙe tana kallar Meenal ɗin don da zuciya ɗaya take ƙaunarta tace "ALLAH ya sawwaƙa Yaya ya baki lafiya..."

Suka fita daga ɗakin ya rage se iyaka su, Suna fita ta buɗe idonta da suke jajir tace "Baffa ka yafe min, kaga abinda ya faru da rayuwata ko?, don ALLAH ka yafe min Baffa...." Be kalleta ba yace. "Ai ba yafiyana ya kamaci ace kin nema ba Ameenatou!, domin kuwa ba ni ne kikama laifin ba, yafiyar mijinki da ubangijin ya kamaci ace kin fara nema, domin kuwa su kika saɓamawa..." Shareefah ce ta miƙe tsaye tana isa ga mahaifin nasu, har gaban ta kai ɗurƙushe ta ce "Don ALLAH ka yafe mata Baffa wllh ba zata iya ɗaukar waɗan nan abubuwan ba...."

Seda ya danne tuƙiƙin dake ƙoƙarin taso masa kana yace. "Zata iya mana, tin da ita ne ta saya hakan da kuɗin ta..." Yaya Sadeeq ne yace.

" Zata gaza É—auka Baffa zuciyarta me rauni ce..."

Tsaye ya miƙe don kar suga abinda ke son ciko idanunsa yace.

"Dole zata iya ɗauka mana, domin duk tsuntsun daya ja ruwa, shi ruwa kan doka, Ta san da ba zata iya ɗaukan bane har ta murzawa idanunta toka tayi fatali da dokokin ubangiji da kuma Mijin ta?..." Yadda Baffan ke maganar kaɗai ya isa tabbatar maka da cewar baƙin cikin da tashi zuciyar take ciki me girma ne, Meenerl dake kwance daga saman gadon marasa lafiyar kuwa, wani lumshe idanunta a hankali tayi , wasu zafafan hawayen data bawa damar sakkowa ya shiga sauka saman fuskarta, wani iri nauyi zuciyarta ke sake ɗauka da fitinannen ciwo, wani irin abu take ji me zafi da raɗaɗi, ji take dama ace ana iya meda hannun agogo baya da ta dawo da hasalin rayuwarta ta da can bayan nan, sedai lokaci ya gama nasa alƙalancin sedai batun tuba da miƙa lamura ga ALLAH kuma.
Chapter 12 · 0% Book details