← Book details Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 36

Sashe 13

Krshen Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitar Baffan ne ya saka kukan da take ta ƙoƙarin dannewa kufce mata, tana kuwa fasa shi da azabar da yake taho mata daga cikin ƙarƙashin tsakiyar ƙirjinta, saurin dawowa gare ta Shareefah tayi, tana tallafar kan yayar nata tare da soma karanto duk adda'ar da tazo bakinta, don ta sama sassaucin abinda ke zuciyarta ya ragu, Cikin iko da buwayar Ubangiji kuwa se gashi adda'o'in na ratsa ta sosai tare da sanyaya zuciyarta. Kafin cikin natsastsiyar kalama da natsuwa Shareefah ta ce... "Ki sani! Babu wani abinda zai faru sai da izinin ALLAH mai girma Yaya!, Tabbas na yarda da ƙaddara kuma koda ace kina yawo da mafi girma a cikin sutturu ne tin da ya ƙaddara hakan a cikin kaddararki seta same ki, sedai sanadin kawai da kika faɗa tarkonsa na shaidan, wajen rashin ƙarasa suturta jikinki da rashin daraja ƙa'idojin da Ubangiji ya gindaya a cikin rayuwar aure. Kiyi hakuri Yaya Meenal, kiyi hakuri ki kuma yi joining wannan ƙaddarar,ki kuma roki ALLAH gafarsa ze kafarta miki, domin kuwa shi ya ce. idan wani lokaci mai tsanani da wahala ya zo a cikin rayuwarku, kafin komai ku sani cewa ALLAH yana da manufa da dalilinsa na zuwan wannan al'amarin dake tare daku, kuma ku tuna cewa na ɗan ƙanƙanin lokaci ne abin zai zo ya wuce ɗin, tamkar ba'a taɓa yin saba.... Yaya Meenal I know da zan ci gaba da ce miki wani abu, domin duk kalmomin da zanyi amfani dasu kin fini saninsu, I know kuma bana da kalmomin da zan baki baki wajen sanyaya zuciyarki a wannan lokacin!, Kamar yanda babu wanda zai iya kashe wutar da ke balbala acikin Rai da Ruhinki sabo da But trust me, I can imagine your pain akan kaina, amma kuma babbar gudun mawar da zan baki a matsayina na Ƴar uwar da kika kasance Yaya kuma Uwa a gareni shi ne, kawai zance ki dage da haƙuri da kuma dannar zuciyarki da fawwalama ALLAH duka lamuranki. In sha ALLAHU Lokacin da baki tsammani ba, Zai sauya miki damuwarki zuwa farin ciki mara iyaka. Tamkar yadda yake juya dare izuwa rana....." Kukan dake ƙoƙarin kufce mata ta danne tana sake tallafar Yayar tata da take jin ta tamkar uwa a gare ta, Don haka cikin wata irin muryan kwantar da hankali ta ci gaba da faɗin. "Ina son ki rungumi duka ƙaddarorinki da zuciya ɗaya, Ki bar komai ga ALLAH domin kuwa shike maganin kowacce irin damuwa da matsala, kana ki yawaita adda'a ki kuma tsarkake imaninki tare da komawa gare shi baki ɗaya, kiyi kokarin cire komai daga ranki duk da nasan da wuya,amma ina son daga wannan rana me kama da haka ki dena ɓata hawayenki akan kaɗɗararki dama ƙalubalan da zakici gaba da riska a gaba , kar kiyi kuka ki dena kuka Yaya domin kuwa ba'a ma ƙaddara kuka bata waje tayi aikinta ake, don kuka baya maganinta sedai karfin adda'a kan rage kaifinta, Bama da uwar da zata tsaya mana wajen dannar zuciyoyinmu, sedai muna da ALLAH shi tsai tsaya mana kin ji Yayata....." Takai ƙarshen maganar nata suna rungume juna su sake sakin wani sabon kukan a tare, sedai na Shareefah'n yafi nata tasirintuwa, don ita nata se ka kasa kunne da kyau zaka iya jin sautin kukan nata,sautin da bashi da wani ƙarfi ko ƙarsashi da amo cikinsa ko misƙala zarratin,saboda rashin wadatacciyar garkuwar jikin da zata bata wannan damar,uwa uba kuma tayi kukan tayi kukan har batasan adadi ba,ta zubda hawayen har sai data daina sanin lokacin tahowarsu, har sai da idanunta suka fara gani dishi dishi tin a daren na jiya data raba kuka da kowa da numfashinta, wanda har daga karshe ta yanke tsammani daga samun dukkan ɗauki,ta kuma gama sallamawa ƙaddarar rayuwarta sedai a yanzun ƙanwar nata ta bata kwarin gwiwa sabuwa. Motsin taɓa ƙofar da akai ne ya saka ta buɗe jajayen idanunta, duk da cewar a hankali ne aka buɗe ƙofar ɗakin, haka nan zuciyarta ta bata tabbacin shi ne, Ya Ahmad ɗin tane, da jiya jiyar nan ta gama wulaƙanta aurensa dashi, amma yanzun wa gari ya waya?, ita ce, ita ce ta sani har gaban abada ita ɗin nan dai ce a ruwa. A hankali ta ɗaga kanta tana kuma sauƙe dubanta ga bakin ƙofar shigowar,duk da kuwa irin yadda gabanta ke mummunar faɗuwa wahala da iftila'in daya gama afkama rayuwarta me gigita hankalin taya gama riskarta, kai tsaye kuwa idonta ya faɗa cikin nashin.
Shi da ita suka zubama juna ido kamar yau ce ranar farko da suka fara ganin juna,kowannensu da kalar kallon da yakema ɗan uwansa. Wanda a kallon farkon daya mata yana kallar yadda tashin hankali ya gama dabaybaye kyakkyawar fuskar nan tata, da har yanzun wani irin kyau na daban me matuƙar tasiri da fusgar hankalin da ya gagara gushewa shimfide saman fuskar tata,saidai kana kallonta kasan ba haka take ba,abubuwa da yawa sun canza wanna fuskar, tsakanin daren na jiya zuwa yau komai ya sanja lissafin fuskar nata, idanuwansa na a kanta ya fara takowa Mahaifinta na tako masa baya, raunin kalaman da Shareefah tayi na kamasu su duka, don suna tsaye sun kuma gama saurarar komai daga gare ta, wannan abu shi ya sanyaya duka jikkuna da zuciyoyinsu, kamar yadda suka gama ruguwa taurin zuciyar Ya Sadeeq ma anan ɗin, da yake zaune har lokacin ya gaza koda wanne kalan motsi, tabbas kalaman Shareefah haka suke kuma suna akan daidai, lallai duk abinda ya faru da bawa tin daga Rabbil Izzati ne yake, Koda ace kai ne ka fi kowa kare martabar da kimarka, idan har ALLAH ya rubuta hakan to kuwa se an samu ɓata garin da dolen dole su bata maka rayuwar a irin wannan gabar!, se dai kamar kuma yacce tace ɗin ne still, son zuciya da rudin zamani kan zama sila ko kuma ja gaba wajen bama shaidan damar afkuwar hakan.
A wani kalan sanyin jiki dana zuciya ya ƙaraso gar gaban gadon yana kaiwa zaune inda Shareefah tayi gaggawar tashi ta bashi,ya zauna sosai yana fuskantarta haɗi da zuba masa idanunsa da suka janye sosai shima... Ganin hakan ya saka su Baffa fita dukansu amma kuma suna daga bakin ƙofar room ɗin, "Me kika yi haka ameenatou?, wanne kalar fentine ne haka kika gogama rayuwar aurenmu uyhmmmm?, kawai don biyema rudin duniya da zamani kika zaɓa lalata rayuwarmu mu duka biyun, da kuma ruguza yardar dake tsakaninmu!. Kina jin irin yadda nake ji kuwa a cikin ƙirjina?, ashe dama haka ƙaddarar take bata da sauƙi irin haka?" Ya ɗinke maganar nashi ne saboda rawar da bakinsa ya fara da haƙoransa, zuba masa jajayen idanunta dake a rine tayi kafin ta lumsh su, ragowar hawayen da basu samu damar zubowa ba suka gangaro mata kana ta buɗesu tarwai a kansa tace....

"Bana da tsumi ba kuma ni da dabarar hana faruwar hakan Ya Ahmad, Kamar yadda ban isa na fidda kaina daga gare kaba, nasan zuwa yanzun ka tsaneni ne Ya Ahmad, kayi hakuri kayi hakuri kayi ta yin haƙuri da bama zuciyarka salama, Ubangiji ya maka mace ta garin data fini nagarta!, da halaye masu kyau fiye dani, zanyi nesa sosai da rayuwarka kamar yacce kaima nasan za kayi nesa da tawa rayuwar!!!, Sedai ka tayani adda'ar koda ace bana raye, to ina son ka tayani da Adda'ar hana duk wanda yamin haka nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin rayuwarsa,Ya kuma girbe fiye da abinda ya shuka min.... Saurin rufe bakinta yayi da hannunsa yana jijjiga mata kai, kafin Yace...

"Ina sonki Meenoh!, bazan iya rabuwa dake ba, kuma banajin zan daina SO da ƘAUNARKI don wata ƙaddara ta gilma tsakaninmu, zan ci gaba da zama dake ameenatou!, kuma bana son wannan maganar ta fita ko ina daga mu se su Baffa, Sedai se kin yi hakuri kin kuma jurema zaman, don kuwa se na gama jinyar zuciya da kaina kafin komai ya dawo mana dai-dai gwargwado iyaka abinda naga naga zan iya, ba zan rabu dake ba INA SONKI ina ƘAUNARKI Meenal........" Sosai ta buɗe ido da baki da hanci tana kallarsa da wani kalan yanayi, kafin bakinta na rawa ta ce...

"Har yanzun kana jin zaka iya ci gaba da zaman aure dani Ya Ahmad?, bayan na gama take aurenka dake kaina, wasu kuma sun gama wulaƙanta martaba da yardar dake cikin auren namu amma har yanzun kake jin zaka iya zaman auren dani?...." Kansa yake ɗan jujjuya mata kafin Yace... "Kifar taso da abinda ya riga da ya gama faruwa, ki ɗauka hakan a wani issue ne na daban daya shafi interest nawa da kuma naki kawai, ki dena sako ko danganto wani a ciki domin zuciyata ba zata ci gaba da jure hakan ba...." Wani kuka ta saka tana ɗamke hannunsa dake cikin nata take furta. "Na gode!, na gode ALLAH, Alhamdulillah ko yanzun ALLAH ya ɗauki raina na gode masa...."

Rumgumeta kawai yayi domin bazai iya ci gaba da saurarar kukan taba, daga nan Dr pooja ta shigo ta sake dudduba jikinta ta haÉ—a mata magani ta basu sallamar da ita ce da kanta tace a basu, Sosai Baffa da Ya Sadeeq suka ta yima Ahmad É—in godiya don duk dama zullumin hukuncin da zai yanke a kanta suke da tsoron kar ace ya rabu da ita, Se da suka musu rakiya har gida kana Baffa ya sake jaddada godiyarsa ga Ahmad kana suka bar gidan....
Chapter 13 · 0% Book details